
طالبات أكاديمية القوارير
542 subscribers
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

Assalamu Alaikum Warahmatullah Makarantar Alqawareer Academy na yi wa ɗalibanta albishir ɗin bude sashin gudanar da ayyuka na alkhairi wanda suka haɗa da ayyukan jin ƙai da taimako, da'awa da kuma umarni da kyakkyawa da hani da mummuna domin cimma hadafin taimako da kuma kawo gyara cikin al'umma. Dukkanin wannan a ƙarkashin Gidauniyar Daliban Alqawareer na ayyukan alkhari. Wannan sashen zai kaddamar da Ciyarwan Watan Ramadan 2025 a matsayin aiki na farko da zai fara gudana a ƙarƙashinsa. Saboda mahimmancin ciyar da mabukata a wannan wata mai alfarma, da kuma tsananin bukata da mawuyacin hali da da yawa daga cikin al'umma suka tsincin kansu a ciki. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: (Duk wanda ya ciyar da mai azumi yana da kwatankwacin ladansa, ba tare da wani abu ya ragu daga ladan mai azumin ba.) Tirmithi. Manufan wannan yunƙuri: Ciyar da gidagen mabuƙata guda 30 a watan Ramadan. Kofar bada taimako a buɗe take daga yanzu har ranar 25 ga watan Febuary. Domin ba da gudunmawarki: 0003507134 Alqawareer Educational Foundation Taj Bank