Blockchain News 🌐
Blockchain News 🌐
February 27, 2025 at 12:52 PM
Ɓarayin pi lokaci zaizo da zakuyi kuka da idanku wallahi. Dan sakarai ne kawai zaa sace masa pi a wallet ya ƙyale. Amma ku sani koba yanzu ba 90% na case ɗin sai sun tashi. 😅 Akwai hanyoyi da yawa da mutun zai iya tracking wallet dinka yaga activities din da kake a explorer muraran mussamman idan yanada case dakai mussaman barayin pi makusanta na unguwa, Amma real scammers masu yi da ilimi zai wuya su kamu. 1]• Hanya ta farko; zai iya daukar address din da akai masa satar yaje explorer yayi ya kalli activities din wallet din, Saiya duba updated transection da akai ya bibiyi wallet dinsu yaga da wace wallet ya taba muamala aciki koshi ko wani abokinsa. Daga nan idan ya gone zai iya tambayar mai wallet din waye ya taba turo maka pi adadi kaza ranar kaza misalin karfe kaza ya bada resit shikenan wanda ya kwasa zai iya shigowa hannu 2]• Hanya ta biyu; yawanci dai duk pi din da aka sata a baya yan bunburutu aka siyarwa, to su kuma yan bunburutu wallet din da suke amfani dasu basa wuce biyu zuwa uku, idan kuma direct marchent zasu bawa zasu saka wallet dinsa ne kai tsaye. A takaice dai suma wallet dinsu duk sanannu ne kana ganin wallet kaza kasan ta wane ce, dan wasu ma saboda sabo turawa kawai ake daga baya ayi masa magana ace antura pi adadi kaza ya shiga ya tabbatar sannan yayi payment. Kaga nan ma simple hanya ce da idan mutun ya sani zai bibiyi wallet din aka tura pi dinsa da aka sata tunda yan bunburutun nan dai kowa ya sansu ba wasu boyayyu bane. 3]• Hanya ta uku; Duk wanda kake zargi daya satar maka pi address din da aka tura kawai zaka dauka saika lallaba shi ya ara maka wayarsa, Saika shiga kamar Gate .io ko Mecx, ko Bybit kayi search deposit address na pi idan kaga yayi dai dai da wanda aka turawa to kawai ka rike shi ya biyaka abinka. Dan kana shiga history zakaga yayi dai dai da lokacin da aka satar maka kuma wannan address din dai aka turo. 4]• Hanya ta hudu; itace (username) 😂 wannan hanyar tafi ko wacce zama hadari da tonon asiri duk randa ta fara aiki dan koda kaci banza a sauran chan to gaskiya zaiyi wuya kasha a wannan. Abokina inda kasan ka taɓa ƙwamushewa abokin ka Pi daga wallet dinshi ka tura wallet dinka to kayi ƙoƙari ka mayar masa da abinsa dan nan gaba username dinka baro baro zai bayyana a wallet dinsa cewa ita aka turawa ga rana ga lokaci, indai bakaso nan gaba kaji kunya to lallai ka mayar masa da abinsa, dan nasan garanti ko bai rike walletl address dinka ba tofa yasan sunan banzan ka. Bama kai kadai ba duk randa akace maka wannan function ya fara aiki to duk wata aika aikar sata da akayi akan blockchain din Pi a fili zafa fito muraran kowa ya ganta kuma bazata gogu ba. Saboda ko wane username da yake kan Pi blockchain ana linking din shine ta da smartcontrack shiyasa zai iya wakiltar ka ka anshi kuɗi ko kuma ka tura kuɗi, sannan shine yake bayyana waye kai akan blockchain din Bayan haka akwai function da yawa da zasu bayyana dannan gaba zaka iya login mining app dinka da username. Nan gaba mutane ba zasuci gaba da amfani da wallet address ba saboda rudaninsa sa asara da akeyi wajen anfani dashi ga wanda bai kuma ba ko bai iya ba, sai dai su dinga amfani da "username" ko "bar code" dan sunfi sauki sau 1000 amma suma anan kuskure sai dai ba kamar wallet ba. Da wannan dalilin nake ganin duk wani wanda aka taɓa satarwa Pi sai yayi tracking wallet din a exploler ya nemo username din wanda yayi satar kuma nasan yana gani zai iya gane wanene, daga nan balli zai tashi kaga yasan yanada phrase dinsa kuma shine ya taba mai sata ga rana ga lokacin da abin ya faru. shikenan mutunci ya zube. Shi kuma ruwan sane yayi genarating wata wallet ya kwashe kayansa ko kuma ya barta. Amma ina mai tabbatar maka kada ya hakura gaba idan yaga Pi ya tashi saiya tafi kotu da wannan hujjar da nufin abi masa hakkin sa. Lokaci Alkali. ⏰ *© Mubarak Na'allah*
👍 ❤️ 😂 🙏 5

Comments