Blockchain News 🌐
Blockchain News 🌐
February 27, 2025 at 01:49 PM
Har yanzu mutane sunada wata gurguwar fahimta akan Pi dinnan Wannan rubutun damai rubutun ba ruwana dasu, maganata akan iya rubutun dana zagaye ne, wato tunanin mutane na cewa a sayi Pi account dinsu ko wallet nasu mai lockup sbd wani dalilai nasu, domin naga har yanzu mutane da yawa sunada wannan tunanin. Toh ku sani, Pi dinku da yake kan app(wanda kuka tara ta hanyar mining) idan yakai guda 10000000π toh kasani cewa dashi da babu duka dayane. Zai iya zama wani abu bisa wasu dalilai, kuma zai iya zama lambobi marasa amfani shima bisa dalilai. Idan darajar 1π a kasuwa ta kasance $1,000 toh har yanzu darajar Pi dinnan naka dakayi mining guda 10000000π daidai yakeda $0 Baka da ko sisi a Pi, sbd baka da Pi. Tayaya zaka samu Pi? Shine kabi hanyar da zaka mayarda wannan lambobi su zama Pi. Hanyar itace: kazama Committed ga abinda ya shafi Project din da kuma ka'idoji da aka tsara maka ka bisu kafin mayarda lokacinka daka ɓata ya zama Pi. Wannan Sune abubuwa dasuke a mainnet checklist dinka:. Installing Pi browser, creating wallet, saita lockup, Signing acknowledgement, cike Kyc idan baka dama, Jiran KYC result, da kuma jiran Migration. Bayan wannan kuma sai lura da pass phrase dinka, tsallake jeri-jerin tarkon scammers, da kuma bibiyan abubuwan da ke faruwa gameda shi project din. Toh shi kansa samun kyc da migration din yanada alaƙa fa jajircewarka da kuma motsinka da Ɗabi'unka akan network din. Akwai ƙaidoji dayawa da zaka karyasu ka zama kasha wahala a bangaren Kyc da migration din. Duk sai wannan ta faru an saka maka coins a wallet, sannan kuma lockup dinsu dakayi ya ƙare sun zama available a cikin wallet dinka. Toh a sannan kakeda Pi. A sannan kakeda 'yancin da zakace wani ya sayi Pi dinka. Dan haka masu siyan Pi account da masu siyarwa da masu siyan wallet mai lockup da masu siyarwa Kowa yasan me yakeyi, idan ba haka ba kuma watakila ku rabu da rigima. Allah ya kiyaye. Musamman masu siyan wallet mai lockup, shin kunada tabbacin cewar mai wallet din baije ya saka pass phrase dinsa a irin shafukan scammers dinnan ba? Wannan ba kawai daukar risk bane, akwai neman rigima. Da yawan wanda suka zama frustrated akan Pi a yanzu sune masu Matsalar maƙalewa a kyc da migration. Sai suce sunyi shekaru da yawa amma an turesu gefe. Bawanda ya tureka Gefe, kamar yadda na fada akwai ƙaidoji wanda Kyc/migration na kowanne user sun dogarane akan wannan ƙaidoji. Idan ka saɓasu wani daga ciki toh wannan delay din shine consequences dinka. Amma kowa zaiyi KYC/Migration idan ya tsaya akan abin. Ko kuma ka koma kabi layin masu kushe Pi kagani ko zaka ƙara masa wani abu. A yanzu dai Pi value a exchanges ya karya ATH na Price din yan bunburutu (Mutane da suka taimaki Pi ya samu daraja)
👍 😂 🙏 4

Comments