
TIJJANIYYA MEDIA NEWS
February 5, 2025 at 09:03 PM
An Binne Almajirai Mutun 17 Sanadiyar Wata Gobara A Kauran Namoda Jihar Zamfara.
Akalla Amajirai 17 makaranta ALKUR'ANI suka mutu sakamakon tashin gobara da ta tashi a wata makarantar Allo a garin Kauran-Namoda dake jihar zamfara.
Gobarar ta fara ne daga wani gida kusa da makarantar a daren Talata ne kuma wutan ta yaɗu zuwa makarantar yayin da yaran suke bacci.
Duk da ƙoƙarin shawo kan wutar da hukumar kashe gobara tayi lamarin yayi ƙamarin da har aka samu asarar rayuka.
Allah ya jikan su da rahma, ya gafarta masu, muna addu'an Allah yasa ALKUR'ANI ya cece su baki daya. Amiiiin Yaa ALLAH
😭
😢
😂
😪
🙏
11