
ABU UMAR ALKANAWY 📚
February 8, 2025 at 03:24 AM
*KANA SON HASKEN KABARI DA YALWARSA?*
_Kwarai da gaske, kabari yana da ƙunci kuma yana da mutuƙar duhu..._
Shin akwai wani tanadi da ka yiwa kabarinka ta yanda za ka samu sauƙi daga duhunsa ko kuma ƙuncinsa?
Muna cikin laluben *fitilar* da za ta *haska* kabarburanmu sai kawai muka ci karo da maganar Annabin Rahama (S.A.W) da yake cewa *"Sallah haske ce."*
Ashe kiyaye sallah zai haskaka kaburburanmu.
Haka nan, muna cikin laluben sababin da zai sa mu samu yalwataccen gurin hutawa a kabarinmu maimakon ƙuntatacce, sai muka ci karo da hadisin dake cewa "Wanda ya fitar da mumini daga wani ƙunci a nan duniya to shima Allah zai yaye masa ƙunci daga ƙuncin lahira."
A cikin hakan zamu fahimci cewa hasken kabari da yalwar sa suna samuwa ne sabo da biyayya ga Allah da kuma kyautata mu'amala ga bayin Allah. Domin kuwa sallah tsakanin bawa da ubangijinsa ne, yayin da fitar da bayi daga cikin ƙunci yana daga cikin kyautata mu'amala a tsakanin bayi.
Ma'anar hakan tana ƙara fitowa idan muka koma zuwa ga hadisin da Annabin rahama ya ambaci ma'abota wasu kaburbura guda biyu da cewa ana musu azaba.
Ɗaya laifinsa tsakaninsa da Allah ne cikin abin da ya shafi fitsari ko suturce kansa, ɗayan kuma laifinsa tsakaninsa da bayi ne cikin yawaita annamimanci.
Kaga na farko laifinsa yana da alaƙa da sallah, na biyu kuma laifinsa yana da alaƙa da mu'amala.
Tabbas wauta ta tabbata ga wanda yake fafutukar samun haske a rayuwar duniya amma yayi biris da neman hasken gidansa na kwanciyar jiran makoma.
Allah ya kyautata makwancinmu da na magabatanmu da waƴanda suka rigayemu da kyautatawa.
✒️
Abu Umar Alkanawy
🙏
5