ABU UMAR ALKANAWY  📚
ABU UMAR ALKANAWY 📚
February 8, 2025 at 09:24 AM
*DALILIN SAMUWAR WADATAR ZUCI DA KUMA DALILIN SAMUWAR TALAUCINTA* Annabin Rahama yace: Hakika bawa idan himmarsa ta zamo neman kyautata lahira, sai Allah ya gyara masa rayuwarsa (kasuwanci, sana'a, noma dss), kuma ya sanya masa wadata a zuciyarsa (wadatar zuci). Wanda kuma himmarsa ta zamo akan Duniya ne kawai, sai Allah ya lalata masa hanyar samunsa, kuma ya sanya masa talaucinsa a idanuwansa, ba zai yammata ba face talaka, kuma ba zai wayi gari ba face talaka. Ahmad a kitaab Zuhd 180 Abu Nu'aim a Hilya (3/47) Wannan ya nuna idan mutum ya kyautata neman lahirarsa sai Allah ya kyautata masa duniyarsa, idan ya gyara alaƙarsa da Allah, sai Allah ya gyara masa alaƙarsa da bayinsa, kuma nutsuwa za ta tabbata a gareshi, zai wadatu da abin da ya samu, zai rayuwa cikin yalwa da aminci. Haka nan idan bawa ya rufe ido wajen neman duniya to Allah zai wahalar da shi da wannan duniyar, zai kuma sanya masa talauci a zuciyarsa ta yanda ba zai taɓa wadatuwa da abin da ya samu ba, kullum ba shi da buri sai hangen na sama da shi da kuma ƙoƙarin kamosu. Sannan zai rasa nutsuwar zuciya, zai rasa aminci da kwanciyar hankali. Allah ka inganta rayuwarmu, ka bamu wadatar zuci, ka sauƙaƙa mana hanyar arzikinmu, ka kuma kiyayemu daga dukkan abin da zai nesanta mu da rahamarka. Ameen ✒️ Abu Umar Alkanawy
🙏 👍 🤲 6

Comments