
ABU UMAR ALKANAWY 📚
February 19, 2025 at 06:45 AM
Daga Mu'adh yace: Manzon Allah yace: Ubangijina ya zo mana a mafarki sai yace ya Muhammad, kace: Ya Allah ina roƙonka sonka, da son masu sonka, da aikin da zai samar min da soyayyarka"
Tirmidhi, Albaniy ya ingantashi (3235)
Ga addu'ar da larabci 👇
اللهم إني أسألك حبك، و حب من يحبك، والعمل الذي يبلغني حبك.
Idan ka tun irin son da Allah yake yiwa Annabi Muhammad (S.A.W) a sannan ne girman addu'ar zai ƙara bayyanuwa gareka.
Idan ka tuno abin da yake biyo baya idan Allah ya so mutum kuwa to ba zaka taɓa wasa da ita ba.
🖋️
Abu Umar Alkanawy
👍
🙏
🥰
3