Eloquence Online English Academy Channel
February 2, 2025 at 11:37 AM
Yadda Na Fassara Wa Dalibanmu Na Asal College Kabuga Kano Sabon Taken Najeriya:
Nigeria, We Hail Thee: New National Anthem (English) + Hausa Translation
By: Ubaidu Lawan Ahmad
1.
Nigeria we hail thee
= Najeriya muna gaida ki
Our own dear native land
= Kasarmu ta asali abar alfaharinmu
Though tribes and tongue may differ
= Duk da cewa kabilunmu da harsunanmu mai yiwuwa sun bambanta
In brotherhood we stand
= A cikin 'yan uwantaka mun hada kanmu
Nigerians all, are proud to serve
= Duka 'yan Najeriya, suna alfaharin yin hidima
Our sovereign Motherland.
= Ga kasar nan tamu ta asali mai cikakken 'yanci
2.
Our flag shall be a symbol
= Tutarmu za ta kasance wata alama
That truth and justice reign
= Wadda gaskiya da adalci za su ja ragamarta
In peace or battle honour'd,
= A cikin zaman lafiya ko yaki muna matukar alfahari da ita
And this we count as gain,
= Kuma wannan abu ne da muke kirgawa a matsayin riba
To hand on to our children
= Domin mikawa 'ya'yanmu
A banner without stain.
= Tuta ba tare da sauya launinta ba.
3.
O God of all creation
= Ya Ubangijin dukkan halitta
Grant this our one request.
= Ka amsa wannan roko namu guda daya
Help us to build a nation
= Ka taimaka mana mu gina al'umma
Where no man is oppressed
= Wadda babu wani mutum cikinta da za a zalunta
And so with peace and plenty
= Saboda haka tare da zaman lafiya da yalwa
Nigeria may be blessed.
= Najeriya za ta kasance mai albarka
👍
❤️
7