Eloquence Online English Academy Channel
Eloquence Online English Academy Channel
February 14, 2025 at 07:21 PM
Words You Need To Know To Use Them Daily // 010 161. Apple /ˈæpəl/ Ma'ana: Tuffa (aful) Sentence example: - He has gone to buy an apple. = Ya tafi siyo tufa. 162. African cherry /ˈæfrɪkən ˈtʆeri/ Ma'ana: Akwaluma Sentence example: - I don't eat African cherry because of its sour taste. = Ba na shan agwaluma saboda tsaminta. 163. Banana /bəˈnɑːnə/ Ma'ana: Ayaba Sentence example: Monkey likes banana. = Biri yana son ayaba. 164. Mango /ˈmæŋgəʊ/ Ma'ana: Mangwaro Sentence example: - We have many mango trees in our garden. = Muna da bishiyoyin mangwaro da yawa a lambunmu. 165. Palm kernel /pɑːm ˈkɜːnl/ Ma'ana: Kwakwar manja Sentence example: - Many girls like palm kernel. = Da yawa yara mata suna son kwakwar manja. 166. Orange /ˈɒrindʒ/ Ma'ana: Lemon zaki Sentence example: - She bought oranges for the patient. = Ta siyowa mara lafiyar lemon zaki. 167. Tiger nut /ˈtaɪgə nʌt/ Ma'ana: Aya Sentence example: - Tiger nut is used to make a tiger nut drink. = Da aya ake yin kunun aya. 168. Garden egg /ˈgɑːdn eg/ Ma'ana: Data Sentence example: - Garden egg come in various colours. = Data na zuwa da launuka daban-daban. 169. Grapes /greɪp/ Ma'ana: Inibi Sentence example: I like to eat grapes. = Ina son cin inibi. 170. Watermelon /ˈwɔːtəˌmelən/ Ma'ana: Kankana Sentence example: - Watermelon contains a lot of water. = Kankana tana dauke da ruwa da yawa. 171. Date /deɪt/ Ma'ana: Dabino Sentence example: It is Sunnah to break fast with dates. = Sunnah ce yin buda baki da dabino. 172. Pineapple /ˈpaɪnæpəl/ Ma'ana: Abarba Sentence example: - Some pineapples are sweet and some are sour. = Wasu abarbar ka same su da zaki wasu kuma tsami. 173. Carrot /ˈkærət/ Ma'ana: Karas Sentence example: - Carrots improve the health of the eyes. = Karas yana kara lafiyar idanuwan. 174. Cucumber /ˈkjuːkʌmbə/ Ma'ana: Kwakwamba Sentence example: - She sliced cucumbers for the salad. = Ta yayyanka kwakwambar domin salak 175. Onion /ˈʌnjən/ Ma'ana: Albasa Sentence example: - Slice the onion over the salad. = Yayyanka albasa a kan salak din. 176. Potato /pəˈteɪtəʊ/ Ma'ana: Dankalin Turawa Sentence example: She used to fry potatoes for breakfast every day. = Ta kan soya dankali a karin kumallo. 177. Sweet potato /swiːt pəˈteɪtəʊ/ Ma'ana: Dankalin Hausa Sentence example: He grows sweet potatoes every year. = Ya kan noma dankalin Hausa duk shekara. 178. Baobad fruit /ˈbaʊbæb fruːt/ Ma'ana: Kwalba Sentence example: Baobab fruit power is used in traditional African medicine. = Ana amfani da garin kwalaba a maganin Afrika na gargajiya. 179. Coconut /ˈkəʊkənʌt/ Ma'ana: Kwakwa Sentence example: Water may be found in the coconut. = Za a iya samun ruwa a cikin kwakwar. 180. Lemon /ˈlemən/ Ma'ana: Lemon tsamin Sentence example: She squeezes lemon in tea. = Ta kan matsa lemon tsami a shayi Copyright © Eloquence Online English Academy Ubaidu Lawan Ahmad, CEO
👍 2

Comments