📚 ZAURAN TUNATARWA 📚
📚 ZAURAN TUNATARWA 📚
February 25, 2025 at 04:03 AM
ANA BINA AZUMIN SHEKARA 2 DALILIN RASHIN LAFIYA, GA WANI AZUMIN YANA ZUWA, YA ZAN YI? : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamualaikum, malam inada tambaya nice ake Bina azumi na shekara biyu bara waccen da bara inada larura ta sikler yau lafiya gobe ba lafiya ga olcer tayi min mummunan kamu bana iya azumi uku ajere innai sai na kwanta jinya ahaka har azumin bara ya tarar Dani ban Rama Wanda ake bina ba gashi yanzu ma azumi yakusa bansamu narama na shekara biyun ba yanzuma haka daga gadon asibiti nake ansakamin jini malam Dan Allah mine mafita yazanyi. Nagode : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa Alaikis Salaam:- Toh abun da Shari'ar Musulunci yace shine, duk wani Rashin Lafiyar da aka je gurin Likitoti Suka Yi Bincike Sosai, Likitotin Musulmai ne masu Amana da riko da Addinin Allah wato masana Musulunci ko ba Sosai ba, sai suka yi Bincike Suka tabbatar da Cewa duk jinyar da Za'a Miki ba za ki warke ba Wato Olsar ki tayi Kuronin Sosai Dole duk Bayan Mintuna ko awanni Zaki bukaci Abinci Ko magani, ko kuma Ciwon da kike fama da shi yayi tsananin da ba za ki iya warkewa ba, duk wasu Mintuna Ko Awanni Dole Sai kin bukaci Abinci da Magani. Toh Shari'ar Musulunci Daman Mai Sauki Ce, Sai Shari'a ta ce Za ki Ajiye wannan Azumin naki, wato Za ki Sha Azumin Watan Ramadan idan ya zo, amma duk Azumin da Za'a Yi Sai ki bayar da sadakar muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam. Kamar misalin a yau an Kai Azumi 1, toh sai ki Auna muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam Kwano 1, sai ki bawa Mubukaci a hakan zakiyi ta yi har a Gama Azumin Watan ramadan ɗin guda 30 ko 29, wato kenan za ki bayar da Muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam Kwano 30 ko 29, wato a Watan Ramadan gaba Ɗayan ta har a Gama abun da za ki bayar kenan. Amma idan har Likitoti sun Yi Bincike sun tabbatar da Cewa Lallai Za ki warke daga wannan Rashin Lafiyar wato Ciwon naki, toh sai ki hakura da yin Azumin, wato ki Sha Azumin Watan Ramadan ɗin, bayan kin samu Sauki sai ki Rama Azumin dukka Wadda Kika Sha kenan in ma Watan dukka ne Kika Sha ko Kuma wasu Kwanaki ne duk dai. Haka zalika, Waɗancan Azumin da Kika Sha a wancan Shekarun ba ki samu damar yin su ba har Zuwa yanzu, idan a Dalilin Rashin Lafiyar ne Kika Sha su a wancan Shekarun, Kuma ga shi har yanzu ba ki biya ba domin Rashin Lafiyar ki wato ba ki warke ba, ba za iya yin Azumin ba sabida Ciwon olsar ki ko wani Ciwon daban, duk wasu Bayan Mintuna ko awanni Dole Sai kin bukaci Abinci Ko magani, toh sai kiyi muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam ga waɗancan Azumin da Kika Sha, tunda kina Tsammanin Daman za ki warke ne ki biya Azumin, kuma ga shi ba ki warke ba, toh sai ki yi Amfani da bayanin mu na sama Cewa idan ba za'a warke ba ga Hukuncin yadda Za'a yi. Yadda za ki yi da muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam, Misalin ana bin ki Azumi 20 ne na waɗancan Shekarun, toh sai kiyi muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam kwano 20 ki bawa Mubukata. Idan 10 ne ko 5 ko Watan dukka, Haka za kiyi. Muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam, Ana fitar da shine da irin Kalan Abincin da Mutanen Gari Suka Fi Amfani da shi, Kamar Misalin Masara, Shimkafa, da Sauran su a Gefen Nigeria kenan. Toh ko Masarar Kika samu Ko Shimkafan ne, da shi za ki yi Muddun Nabiyyi Sallallahu Alaihi Wasalam Ki bawa Mabukata. WALLAHU A'ALAM. ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Comments