
๐ ZAURAN TUNATARWA ๐
February 25, 2025 at 04:03 AM
HUKUNCIN KULLA NIYYAR AZUMI:
:
๐๐๐๐๐๐๐โ
:
Assalamu Alaikum, Dan Allah tambya nake, Ina son yin ramuwar azumin ramadan to ban ษaura niyya ba se bayan alfijr, Yaya matsayin azumina, Kamar dai ance ba Azumi koh, Toh ina tantama ne idan kuma babu shin zan iya maida shi azumin bakance da nayi Alkawari ?Allah ya saka da alheri.
:
๐๐๐๐โ๏ธ
:
Wa Alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Yin niyya cikin dare game da azumi na farilla, a bisa mahangar malamai mafi inganci, game da azumin ko kuma na ramuwa ne wannan shine ra'ayin mafi yawan malamai.
Ibn Qudamah mai littafin al-Mughni ya ce: Idan ya kasance azumin farilla ne, kamar azumin Ramadan akan lokaci ko kuma na ramuwa ne wanda mutum zai rama shi daga baya, ko azumin cika bakance, ko azumin kaffara, to an shardanta ma mutum ya yi niyya tun daga daren da ya gabata, kamar yadda limaminmu, da Malik da ash-Shafi'i suka fada.
Imam Abu Hanifah ya ce: An yarda gameda mai yin azumin ramadana da duk wani azumi wanda wani dalili ne ya ke samar dashi na musamman ya samar da niyya tun daga ranar. (littafin Al-mugni 3/109)
Dalilin da yasa suka ce wajibi ne mutum ya yi niyya tun daga daren da ya gabata, shi ne hadisin da ya tabbata daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: โDuk wanda bai yi niyyar yin azumin gabanin alfijir ba, to azuminsa ba ya cikin lissafi (bashi da wannan azumin).โ Tirmiziy (730) ya ruwaito kuma Albaani ya sanya shi a matsayin hadisi sahih a cikin Sahih at-Tirmidhi.
Imamut Tirmizi ya ce, bayan ya kawo wannan hadisi: Abin da ake nufi da hakan, a wajen malamai, shi ne, babu azumi ga wanda bai yi niyyar yin azumi ba kafin fitowar alfijir, ko a cikin Ramadan ne ko kuma lokacin da ya zo rama azumin ramadana ko lokacin da zai rama azumin bakance. Idan bai yi niyya daga daren da ya gabata ba, to bashi da azumi.
Amma azumin nafila, ya halatta a gare shi ya yi niyya bayan ya tashi (da safe). Wannan shine ra'ayin ash-Shafiโi, Ahmad da Is-haaq.
Allah ne mafi sani.
๏บณู๏บ๏บคู๏บ๏ปงู๏ปู ๏บ๏ป๏ป ูู๏ปฌู๏ปขูู ๏ปญู๏บู๏บคู๏ปคู๏บชู๏ปู ๏บ๏บทู๏ปฌู๏บชู ๏บ๏ปฅ ๏ปู๏บ ๏บู๏ปู๏ปชู ๏บู๏ปปูู ๏บ๏ปงู๏บู ๏บ๏บณู๏บู๏ปู๏ปู๏บฎู๏ปู ๏ปญ๏บู๏บู๏ปฎ๏บู ๏บู๏ปู๏ปดู๏ป