๐Ÿ“š ZAURAN TUNATARWA ๐Ÿ“š
๐Ÿ“š ZAURAN TUNATARWA ๐Ÿ“š
February 25, 2025 at 04:09 AM
BANA IYA MAGANA A GABAN SAURAYINA: : ๐“๐€๐Œ๐๐€๐˜๐€โ“ : Assalamu alaikum Malam. Ina neman shawara ne kamar haka; maganar aurena ya nuna. Amma babbar matsalata shine yanzu haka kusan sati 2 ba magana atsakaninmu da saurayin nawa, Daman Muna irin hakan kowa ya qyale kowa, Amma daga baya muna shiryawa ko ya bani haquri. Yanzu haka matsalar da Nike ciki kenan. Ni da kaina nayita kiranshi a waya yaqi dagawa nayi Text shiru sai da na roqeshi sannan yay magana. na tambayshi mi ke faruwa? nayi nayi ya nuna min ba komi. Yanzu haka ran asabar na kira Mun gaisa lafiya lau Amma Yanzu haka shiru. lokacin da muke normal kusan kullun sai munyi waya Amma Yanzu ko a chat baya iya yimin magana. babban abinda ke damuna tun zuwan farko da yayi Yana son mu tatauna muhimmiyar magana sai inji kamar an sanya min zip abakina. Zuwan shi na biyu ma haka. last zuwanshi haka nayi magana ta gagarenj gaba ษ—aya sai in rasa me zan cewa akai. Yana qoqarin yasan rayuwar abinda nike son da Wanda banaso kafin ayi aure Amma wlh sai inyi shiru in kasa tuna komai. Ina cikin damuwa. Malam ni ma'abociyar karatun Alqur'ani ce da safe inayi tareda azkar bayan magrib sai nayi tareda azkar har zuwa ishaa. Ina cikin damuwa. Allah ya qara wa Malam lafiya amin. : ๐€๐Œ๐’๐€โ—๏ธ : Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Kici gaba da abinda kika saba ta ษ“angaren addu'o'in da azkar da yawaita karatun Alqur'ani Mai girma. Sannan idan zaki iya, ki rika yin nafilfilin dare wato Qiyamul Layli domin tana da mutukar tasiri wajen samun biyan bukatu da yayewar damuwa. Abu ne mai kyau mace ta kasance mai yawan kunya da kawaici da Qarancin surutu. To amma babu laifi ki saki zuciyarki domin ku tattauna akan muhimman batutuwan dake gabanku. Don haka ina baki shawarar cewa duk lokacin da yazo, ki tsaya tukunna ki kintsa kiyi nafila koda raka'a biyu ne sannan kiyi addu'o'i da zikirai kafin ki fita kofar gida wajensa. Ina yi miki fatan alkhairi da fatan Allah shi tabbatar miki da cikar burinki, ya baki miji nagari wanda zai kula da hakkokinki. Ameen thumma Ameen. WALLAHU A'ALAM. ๏บณู๏บ’๏บคูŽ๏บŽ๏ปงูŽ๏ปšูŽ ๏บ๏ปŸ๏ป ู‘ูŽ๏ปฌู๏ปขู‘ูŽ ๏ปญูŽ๏บ‘ู๏บคูŽ๏ปคู’๏บชู๏ป™ูŽ ๏บƒ๏บทู’๏ปฌูŽ๏บชู ๏บƒ๏ปฅ ๏ปŸูŽ๏บŽ ๏บ‡ู๏ปŸูŽ๏ปชูŽ ๏บ‡ู๏ปปู‘ูŽ ๏บƒ๏ปงู’๏บ–ูŽ ๏บƒ๏บณู’๏บ˜ูŽ๏ปู’๏ป”ู๏บฎู๏ป™ูŽ ๏ปญ๏บƒูŽ๏บ—ู๏ปฎ๏บู ๏บ‡ู๏ปŸูŽ๏ปดู’๏ปš
๐Ÿ™ 1

Comments