
📚 ZAURAN TUNATARWA 📚
February 25, 2025 at 04:09 AM
MATSALAR NAMIJIN DARE (JINNUL ASHIK ):
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamu alaikum. Malam don Allah shawara da addu'a nake nema. Nakai shekara ashirin da biyu amma bani da tsayayyen saurayi wanda in akace ya fito ayi aure zai fito. Akwai wanda ya taɓa neman aurena har manya sun shiga cikin maganar daga baya yace ya fasa. Duk wanda yazo gurina da niyyar yana sona bama dadewa dashi sai ya daina zuwa ba fada ba komai. Akwai wani mutum a layinmu yace mun inzo ya kaini gurin wani malami in amshi taimako, ni kuma ban yarda dashi ba shine nike neman shawara da addu'a a bakunanku masu albarka.
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Wa'alaikum salam wa rahmatullahi
Hakika kinyi zurfin tunani da baki biye ma wannan mutumin ba. Domin kuwa acikin masu bada irin wannan taimakon ana samun da yawa waɗanda sukan aikata shirka da kuma haramtattun abubuwa iri-iri waɗanda shari'a bata yarda dasu ba.
Yara 'Yan mata da yawa suna fama da Irin wannan matsalar taki. Amma dai wasu tasu matsalar bata rasa dangantaka da matsalar nan ta *jinnul ashiq (Namijin dare).*
Wani irin Shaiɗanin Aljani ne wanda yake addabar Mata. Yakan zo ma mata acikin mafarkinsu yana saduwa dasu, ko kuma yana nuna musu abubuwa iri-iri. Kuma yakan shiga zukatan samarinsu yana chusa musu waswasi game dasu, yana shiriritar dasu, ko kuma ya chusa Qiyayya atsakaninsu.
Wasu kuma matsala ce wacce ta danganci irin gidajen da suka taso, ko kuma yanayin Mu'amalarsu da jama'a. Amma dai dukkan matsalalolin biyu babban maganinsu shine addu'a tare da jajircewa wajen nafilfilin dare da rana.
Idan har abun ya tsananta kuma, akan yi Ruqyah wani lokacin ma har akan tarar da shi Aljanin dake jikin.
Don haka kema shawarar da zan baki anan ita ce ki dage wajen yin azkar ɗin safe da yamma da karatun Alqur'ani da zikirin Allah ko yaushe. Sannan ki yawaita ayyukan biyayya na nafilfili kamar sallolin dare da rana da yin azumi da kuma Sadaqah don neman yarda Allah.
In Shã Allahu zaki ga biyan bukatarki da yayewar damuwarki cikin sauki. Amma kada ki rika bibiyar Malaman duba ko bokaye da 'Yan bori. Allah ta'ala ya tsare mana imaninmu.
WALLAHU A'ALAM
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
❤️
👍
2