
📚 ZAURAN TUNATARWA 📚
February 25, 2025 at 04:09 AM
HUKUNCIN SAKIN MACE MAI HAILA:
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Menene Hukuncin Wanda Ya Saki Matarsa Cikin Haila?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fadin Allah a Suratu Addalak aya ta farko:
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحْصُوا الْعِدَّةَ ۖ
“Ya kai Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a farkon iddarsu (wato a farkon tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba).
Ana nufin a halin da za su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya faruwa sai idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin tsarkin da bai take ta ba, domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci idda ba, saboda hailar da ya sake ta a ciki ba za’a kirga da ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da tsarki bayan ya sadu da ita, domin bai sani ba shin ta ɗauki ciki ta yadda iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta ɗauka ba ta yadda za ta yi idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai sakin ya haramta.
Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa: Ibn umar ya saki matarsa tana haila, sai Umar ya bawa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam labari, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi fushi, sai ya ce “ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya rike ta har ta yi tsarki sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so ya rike ta ko kuma ya sake ta kafin ya sadu da ita, wannan ita ce iddar da Allah ya umarta a saki mata a ita”
ANA TOGACE GURARE GUDA HUƊU WAƊANDA SAKIN MACE MAI HAILA YAKE HALLATA:
1. idan sakin ya kasance kafin ya Kaɗaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda anan bata da idda, sakinta ba zai zama ya Saɓawa faɗin Allah maɗaukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba
2. idan ta yi hailar ne tana da ciki kamar yadda aka riga aka yi bayani a baya.
3. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL’I) to anan babu laifi ya sake ta tana haila.
4. Idan ya yiwa matarsa I’LAA’I kuma aka yi watanni huɗu bai dawo ba.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Yusuf Zarewa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
🙏
1