
📚 ZAURAN TUNATARWA 📚
February 25, 2025 at 04:09 AM
HUKUNCIN WANDA YA KARYA AZUMIN NAFILA:
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
ASSALAMU ALAIKUM brk d dare malam Allah yakara lfy tmbyata itace , mutum ne yayi niyyan yin azumi Monday (nafila like Monday and Thursday) saida yatashi da safe yace yafasa yayi breakfast, shine akace mishi sai ya Rama, toh malam yanxu sai ya Rama ne ? Azumin nafila ne ba farillah ba
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.
Malamai Sunyi Saɓani akan wanda ya Ɗauki Azumin nafila Shin dolene saiya kaishi ko ba tilas bane?
Wasu Sukace: Ba tilas bane kai Azumin nafila, kamar yanda yake a mazhabar Shafi'iyyah da Hanabila Sun kafa Hujja da Hadisin Aisha Allah yaqara mata yarda wanda yazo acikin Muslim (1154) da hadisin Abu juhaifa wanda Bukhari ya ruwaito (1968) da Hadisin Abu sa'idul khudry Wanda Dharul qudny yaruwaito (24) Alhafiz ibnu hajar ya kyautatashi acikin fat-hul baary (4/210).
Wanda dukkansu suna Nuna Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yawayi gari yana azumin nafila, amma daya Samu Abunci saiya karya azumin.
Haka Sahabi Abuldar-da'a yawayi gari yana azumin nafila sai Ɗan'uwansa salman Ya haɗa masa Abunci yaci, yakarya azumin kamar yanda yazo acikin hadisin Abu juhaifa.
Wasu Malaman sukace: Wajibine kai Azumin nafila, idan kuma mutum yakarya wajibine ya ramashi, wannan shine yazo amazhabar Abu hanifa sunkafa hujja da: Hadisin Aisha Allah yaqara mata yarda wanda Abu dauda ya ruwaito (2457) da Turmuzy (735), saidai hadisine mai rauni Nawawi ya raunatashi acikin Al-Maj-Mu'u (6/396) da Ibnul Qayyeem acikin zhadul Ma'adi (2/84) da Albani.
Wanda ya nuna Aisha da Hafsa sun wayi gari Suna azumin nafila sai aka kawo musu abunci dasukayi sha'awarsa sai suka karya azumin, da Suka baiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam labari saiyace: Su rama wani amadadinsa.
Saidai hadisine Mai rauni bai ingantaba.
Maganar farko itace mai qarfin dalili hadisan da suka kafa hujja dasu sun inganta..
Babu laifi idan ka dauki azumin Sittu shawwal saika karyashi bazaka ramashi ba, domin mai azumin nafila shine sarkin kansa.
WALLAHU A'ALAM.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ