Jidda Hub Academy
Jidda Hub Academy
June 4, 2025 at 05:22 PM
YANDA ZA KA RIBACI RANAR ARAFA 1-Kebance kanka guri guda domin yin ibada 2-Yawaita karatun Alkur'ani 3-Kiyaye Azkar A- Azkar din safe da yamma B-Laa ilaha illallah wahdahu laa shareeka lahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shay'in qadeer(Sau 100) C-Istigfari (1000 zuwa 3000) D-Salati ga Manzon Allah a qalla sau dubu E-La haula wala quwwata illa bilah(100 ko fin haka) F-Subhanallahi walhamdulillahi wala ilaha illallah wallahu Akbar(100) G-Subhanallahi wabi hamdihi Subhanallahil Azeem(100) H-Hasbunallahu wanimal wakeel(Kamar sau 200) Duka kirgan da a ka ambata za ka iya karawa ko ragewa, an kawo sune a matsayin misali ba qayyadewa ba. 4-Ka kwanta da wuri dan ka samu karfin yi ma Allah da'a. 5-Ka tashi cikin dare ka yi raka'a biyu ko hudu ko abin da dai Allah ya ba ka iko. 6-Ka yi addu'a cikin sujudojinka ka roki Alkhairan duniya da lahira kuma ka yi masa godiya da ya raya ka zuwa wannan rana. 7-Niyyan azumi kuma ka tashi da azuminka. 8-Kafin alfijir ka yawaita Istigfari. 9-Ka shirya tsaf ma Sallar asuba kafin a kira da yan mintuna ka yi raka'oi biyun Alfijir ka zauna jiran sallah, kuma ka rika jin cewa zunubanka suna fita a yayin da kake alwala. 10-Kar ka bata kowani yanki na wannan rana cikin abin da Allah ba ya so. 11-Ka yi sallar asuba ka zauna a wajen da ka yi sallarka kana zikiri har rana ta fito. 12-Ka fara Kabbarori daga lokacin da ka idar da sallah, ka yi azkar dinka na safe, Hailala, Hauqala Hamdala, Tasbihi, Karatun Alkur'ani... 13-Yin Sallah raka'oi biyu bayan fitowan rana. 14-In ka samu dama ka cigaba da ibada, in kana son ka dan kwanta ka yi barci na awa daya, sai ka tashi ka yi Sallar walaha. 15-Kabbarori, Tilawa, yawaita fadin: Laa ilaha illallah wahdahu laa shareeka lahu, lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kullu shay'in qadeer... 16-Ka fita sallar Juma'a da wuri, ka yi azkar din bayan sallolin farillah, Kabbarori, Tasbihi, karanta wani abu na Alkur'ani. 17-Ka dage ka yi Sunan rawatib baki daya(Nafilolin kafin sallar farilla da bayanta). 18-Ka yi La'asar, zikirorin bayanta, Azkar din yamma, Kabbarori... 19-Ka cigaba da karatun Alkur'ani har zuwa kusa da faduwan rana da kaman awa daya, sai ka fara addu'oi cikin kankan da kai da karerayewa ga Allah da nuna buqatuwa gareshi tare da jin cewa an amsa maka, kar ka manta da kanka, iyayenka, 'ya 'ya, yan uwa da malamai a cikin addu'oinka, haka kasarka kar da ka manta da ita cikin addu'oi. 20-Ka yi ta addu'a har rana ta fadi. Allah ya karba mana ya datar da mu ga ayyukan kwarai. 😊

Comments