TRT Afrika Hausa

TRT Afrika Hausa

55.4K subscribers

Verified Channel
TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
February 5, 2025 at 04:14 PM
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi Faransa ranar Larabar nan a wata ziyara ta ƙashin kansa, daga can kuma zai wuce taron Kungiyar Tarayyar Afirka AU da za a gudanar a birnin Addis Ababa na Ethiopia a makon gobe, kamar yadda wata sanarwa ta fadar shugaban ƙasa ta bayyana. Sanarwar, wacce Mai taimaka wa shugaban na Musannan kan watsa labarai Bayo Onanuga ya sanya wa hannu ta ce Tinubu zai gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ziyarar. Onanuga ya ce Shuugaba Tinubu zai wuce Addis Ababa a makon gobe domin halartar taron na AU da za a gudanar ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairu.
😂 👍 ❤️ 💣 😡 😭 🇳🇬 👺 37

Comments