
TRT Afrika Hausa
53.3K subscribers
Verified ChannelAbout TRT Afrika Hausa
Afirka tsantsarta
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

https://trt.global/afrika-hausa/article/577c1e5c84ac

Yayin da yanayin zafi ke ƙaruwa a yankin, Saudiyya ta ƙaddamar da tsarin sanyaya waje mafi girma a duniya a Masallacin Harami na Makkah da Masallacin Annabi a Madina domin sauƙaƙa aikin Hajji ga mahajjata a yayin tsananin zafi. 👉🏻 https://trt.global/afrika-hausa/article/0f973ed6aee2


Ku saurari Labaran TRT Afrika Hausa na yau Laraba 4 ga watan Yunin 2025 tare da Shamsiyya Hamza Ibrahim 🎧 👉 https://trt.global/afrika-hausa/audio/7e57b3a5ceb5


Daga ranar Laraba 8 ga watan Zul Hijja da ya yi daidai da 4 ga watan Yuni miliyoyin Musulmai daga sassan duniya suke fara aikin Hajjin bana, ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar. Ga wasu daga daga cikin ayyukan da mahajjata ke yi a lokacin aikin Hajjin. Ga cikakken labarin a nan 👇 https://trt.global/afrika-hausa/article/420f030abed1


A wata sanarwa mai ɗauke a sa hannun Danmakwayon Kano Alhaji Abba Yusuf, wacce aka fitar ranar Talata, sanarwar masarautar ta ce ana umartar dukkan hakimai su shiga cikin birnin Kano tare da mahayansu da dawakansu ranar Laraba, don jin yadda hawan zai kasance. https://trt.global/afrika-hausa/article/7e22351297a2

Aƙalla yara almajirai 11 ne suka rasa rayukansu a jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya bayan wani tarin yashi ya rufta kansu yayin da suke tono laka daga rami, kamar yadda kafofin watsa labarai na cikin gida suka ruwaito. 👉🏻 https://trt.global/afrika-hausa/article/f784f9b38a85


Ba a lokacin Aikin Hajji ne kaɗai hankulan Musulami ke karkata ga Ka'aba ba, a duka fadin duniya Musulmai suna fuskantar ɗakin mai daraja yayin sallolinsu biyar a kowace rana. Latsa nan don ganin wasu bayanai na tarihi dangane da wajen mafi tsarki ga Musulmai. 👇🏻 https://www.instagram.com/p/DKe5YbFoazM/?img_index=1


Malam Nuhu Ribadu ya alaƙanta amfani da miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin matasa — da ƙaruwar rashin tsaro, yana mai cewa yawancin ‘yan ta’adda na amfani da miyagun ƙwayoyi. https://trt.global/afrika-hausa/article/521514cac6b3

A wata sanarwar Masarautar da aka fitar ranar Talata, ta ce ana umartar dukkan hakimai su shiga cikin birnin Kano tare da mahayansu da dawakansu ranar Laraba, don jin yadda hawan zai kasance. 👉https://trt.global/afrika-hausa/article/7e22351297a2


Jakadan Amurka a Turkiyya, Tom Barrack ya bayyana cewa Turkiyya ta taka rawa ta musamman a tattaunawar da ake gudanarwa kwanan nan a Istanbul domin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine. https://trt.global/afrika-hausa/article/fdbf08388f59