TRT Afrika Hausa

TRT Afrika Hausa

55.4K subscribers

Verified Channel
TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
February 27, 2025 at 06:52 PM
Hukumar tsaro ta farin kaya ta NSCDC reshen jihar Zamfara ta kama lita 1,571 ta man fetur da aka yi fasa ƙwaurinsu kana ake zargin za a kai su wuraren 'yan bindiga a jihar. A yayin zantawarsa da manema labarai a madadin kwamandan NSCDC na jihar, jami'in hulɗa da jama'a rundunar Sani Mustapha ya bayyana cewa an kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata laifin a wurare biyu daban-daban. Biyu daga cikin wadanda ake zargi, ma'aikatan da ke sayar da mai ne a wani gidan mai, sai kuma sauran biyun an kama su a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Tsafe na jihar.
Image from TRT Afrika Hausa: Hukumar tsaro ta farin kaya ta NSCDC reshen jihar Zamfara ta kama lita...
👍 🙏 🇵🇸 ❤️ 😙 😢 🤝 23

Comments