
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 11, 2025 at 01:37 PM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Shekarar Rubutu
10-02-2024
Website:- www.Arewanovels.com.ng
Wthapp Number
08137237071
https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
KUNDIN AL'AJABI
GWARAZAN JIYA
BABI NA UKU
Kimanin shekaru ɗari biyu da ɗoriya a birnin Romaniya mahaifinmu sarki Raziban shi ne ke riƙe da Sarautar birnin,
Sarki Raziban yakasance gwarzon mayaƙi kuma JARUMIN JARUMAI gawutaccen matsafi wanda masu bincike da hasashe suka tabbatar da cewa a ƘARSHEN ƘARNI na uku bayan shuɗewar boka Shuyuɗan mai taskar ANNOBA DARI ba a samu wanda ya kai mahaifinmu ƙarfin sihirin tsafi,
Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan nahiyar ke yi masa mubaya'a bisa dole,
Wasu ma na kiran mahaifinmu da Amirul-Sihir ma'ana Sarkin bokaye.
Duk da irin ƙasaitar mulki da mahaifin mu ke da shi amma giyar mulki ba ta ja shi ba yakasance mutum adali ma'abocin tausayi da afuwa,
Mahaifinmu ya na da 'ya'ya guda bakwai, Yarima Zafiyar shi ne babba dai gimbiya Rumailat, Yarima Hasanul-Mausur, Sumaiyat, Laswil, Rukaisu, Zaidar sannan kuma ni Matawus na cikon bakwai ɗin su.
Kowannen mu na samun kulawa daga soyayyar mahaifinmu, duk da irin matsananciyar gaba da ƙiyayyar da ke tsakanin mu wacce ba kowa ba ne ya haddasa hakan ba face bakin kishin da ke tsakanin iyayen mu mata.
Wata rana mahaifin mu na zaune a fadarshi bisa karagar mulki, fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da ma abin da idanu ba su taɓa gani,
Fadar ta cika maƙil duk inda mutum ya kalla babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke.
'Yan majalissar sarki na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma
A kowa ce kusurwa a fadar dakaru ne na jinsin MUTUM DA ALJAN shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar gwarjini da ban tsoro ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro.
A wannan lokaci idan ka ɗauke iskar da ke kaɗawa a fadar babu abin da kunne ke ji face sautin fitar numfashin ɗaruruwan jama'ar fadar.
A na cikin wannan hali ne kwatsam sai a ka ga sarki ya faɗo daga kan karagar mulki yana amai na jini kuma tari mai tsanani ya turnuƙe shi,
Cikin kaɗuwa gaba ɗaya 'yan majalissa suka yi ca akan mahaifina, da hanzari dakaru suka shigo fadar ɗauke da wani ƙayataccen gado suka ɗauki sarki suka fice da shi kai tsaye suka kai shi turakar shi suka shimfiɗe shi bisa gadon sarauta suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar shi.
A can gidan sarauta kuwa labarin abin da ya faru da sarki ya riske mu don haka ni da 'yan uwana sai muka ɗunguma muka nufi turakar shi hankulan mu a tashe,
Ya yin da muka iso ne sai dakarun da ke tsaron ƙofa suka dakatar da mu cewa sarki ya ce kada a kyale kowa ya shiga har sai ya yi umarni.
Ko da jin wannan batu daga bakin dakarun sai yarima Zafiyar ya fusata ainun ya daka masu tsawa ya dube su ya ce "Shin mene ne matsayin ku da har zaku hana mu ganawa da abbanmu ina so ku gaggauta buɗe mana ƙofar tun kafin KAIFIN TAKOBI na ya tsara ruhikan ku".
Da jin hakan daga bakin yarima sai hankalin dakarun ya dugunzuma ainun, daƙyar aka samu wani mai dakakkiyar zuciya ya buɗi baki da nufin ya furta wani abu, kawai sai aka ji ƙarar zare sakatun dake dake kofar, jim kaɗan sai ƙofar ta buɗe sai ga boka Jauwad ibn Ramli ya bayyana a gare su.
Boka Jauwad yakasance dattijo mai kimanin shekaru saba'in dogo ne kakkaura yana da gashin gemu da ƙasumba farare sol ko ɗigon baki babu, fuskarshi doguwa ce mai ɗauke da dara-daran idanu jajajur! tamkar garwashin, yana da faffaɗan hanci mai ɗauke da ƙofofi tamkar mazirari, bakinshi tafkeke ne tamkar bakin rijiya mai ɗauke da wargatsattsun haƙora marasa kyawun gani, yana sanye da baƙaƙen tufafi tare da guraye da layu na sihiri tamkar wani tsohon mahaukaci, kallo ɗaya za ka yi boka Jauwad ka tabbatar da cewa ya cika hatsabibi a fagen sarrafa alƙalumman sihiri.
Duk da kasancewar mahaifinmu mashahurin matsafi da babu tamkar shi a nahiyar amma bisa al'adar masarautar mu akwai bokan da ya ke gudanar da dukkan wani sha'ani na lafiyar iyalan masarauta, da kuma jagorancin abin bauta.
Ya yin da muka yi arba da boka Jauwad sai dukkanin mu muka risina gare shi muka kwashi gaisuwa cikin girmamawa, boka Jauwad ya dube mu ɗaya-bayan-ɗaya, sannan daga bisani ya buɗe tafkeken bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce
"Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa wannan jinya da ta samu mai martaba cuta ce mai matuƙar haɗarin gaske, wacce za ta iya zamowa ajalin shi baki ɗaya,
Ba wani abu ba ne ya haddasa mashi cutar ba face wani sihiri da abokin gabar shi boka Bazzagul-Nadiyar ya yi mashi, an binne sihirin ne a cikin wata tsohuwar rijiya dake cikin fadar sarkin bokayen aljanu na duniya,
Kafin mutum ya isa inda fadar sarki bokayen take akwai haɗdura masu yawa gami da miyagun dazuka.
A halin yanzu bincike ya tabbatar mani da cewa a kaf duniya yanzu babu wani waje mai tattare da haɗari tamkar shi,
Daga nan zuwa can ɗin tafiyar shekaru huɗu ce amma bisa Saurayin aljani mai tashen balaga za a iya isa cikin watanni shida.
Sa'adda boka Jauwad yazo nan a jawabin shi sai hankulanmu ya dugunzuma ainun, wasu daga cikin'yan uwana cikinsu ya ɗuru ruwa, saboda fargabar kada sarki ya rasa rayuwar shi a halin yanzu ba tare da ya sanar da su mabuɗin taskar dukiya ba.
Boka Jauwad ya katse shirun da ya wanzu tsakanin su ta hanyar buɗe baki a karo na biyu ya ce " Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa a halin yanzu
babu abin da ya ke gaban ku face shiga duniya domin ku isa fadar sarkin bokaye ku karya sihirin da aka yi wa sarki,
Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan har kuka yi jinkiri sarki ya rasa rayuwar shi tamkar kun rushe birnin ku da hannayenku ne, domin abokin gabar abban ku boka Bazzagul-Nadiyar zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA na wannan birni, kun ga kenan shi ne zai gaji KARAGAR MULKI ta mahaifin ku.
Jawabi na ƙarshe a gare ku shi ne mai martaba sarki ya ce na faɗa maku cewa dukkanin wanda ya samu nasarar tone sihirin da aka yi masa shi ne zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA.
Ko da boka Jauwad yazo nan a zancen shi sai ya rikiɗa zuwa wani baƙin hayaƙi ya ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Jiki a sanyaye ni da sauran 'yan uwana kuma juya muka fice daga harabar turakar mai martaba.
Kamar yadda boka Jauwad ya faɗa haka al'amarin yakasance bayan kwanaki biyu da kwanciyar mai martaba jinyar rashin lafiya sai dukkan 'ya'yan tare da ni mu ka hallara a fada domin gudanar da tafiya karya sihirin tsafin da aka yiwa mahaifinmu, lokacin da mu ka shigo fadar sai mu ka tarar ta cika maƙil da jama'ar gari tare da 'yan majalissar sarki a gefe guda boka Jauwad ne tare da magajin gari mai suna Shuraih wanda yakasance ɗan uwa a wajen sarki uwa ɗaya uba ɗaya, bisa dokar masarautar duk sa'adda sarki ya kwanta jinya ko kuma wani uzuri ya same shi sai a damƙa sarauta ga magajin gari,
A iya sanin da nayi wa magajin gari shuraih nasan babu wata matsala tsakanin shi da sarki don haka koda wannan jinya ta sarki ta faru ban zarge shi da wani abu ba,
Bayan kowa ya hallara a fadar kuma an samu nutsuwa sai sarki Jauwad ya miƙe tsaye daga kan kujerarshi ya fuskanci al'umma ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku jama'ar wannan faɗa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne 'ya'yan mai martaba sarkinmu za su tafi izuwa fadar sarkin bokayen duniya domin su tone sihirin tsafin da aka yiwa sarki wanda abokin gabar shi kuma maƙiyin wannan ƙasa tamu ya yi mashi wato sarki Bazzagul-Nadiyar.
Bisa Wasiyyar da sarki ya bayar cewa dukkanin wanda ya tone wannan sihirin tsafi ya zo da shi nan shi ne zai gaji karagar shi ya mulki.
Sa'adda boka Jauwad yazo nan azancen shi sai fadar ta kaure da cece kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi, tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani Jauwad ya ɗaga hannunshi sama fadar ta yi tsit a karo na biyu sannan ya cigaba da cewa "Yanzu dukkan wani abu na guzuri da abin hawa an tanadar masu abin da ya rage yanzu shi ne za a ɗora Magajin gari a bisa KARAGAR MULKI, sannan bayan 'ya'yan mai martaba sun yi bankwana da mahaifinsu mata za'a yi masu rakiya izuwa bakin ƙofar gari.
Lokacin da boka Jauwad yazo nan azancen shi sai wani badakare ya matso daf da shi ɗauke da wata akwatun baƙin ƙarfe ya ajiye a gaban shi ya buɗe ta ya ɗauko wani kambun Sarauta ya miƙa mashi shi kuma ya ɗora kambun a bisa kan magajin gari da ke zaune a daf dashi a kan kujerarshi, badakaren ya sake zira hannunshi a cikin akwatun ya ɗauko wata sharbebiyar takobi a cikin kubenta ya risina cikin ladabi ya miƙa wa Boka Jauwad shi kuma sai ya damƙa a hannun magajin gari,
Sannan shuraih ya miƙe tsaye ya je ya zauna a bisa KARAGAR MULKI take jama'ar dake fadar suka risina da kawunansu a gare shi dake nuna mubaya'a a gare shi.
Koda kammala bada riƙon sarauta sai ni da 'yan uwana muka shiga zuwa gidan sarauta domin yin bankwana da mahaifanmu kamar yadda boka Jauwad ya tsara,
Lokacin da na Kaɗaita da mahaifiyata a cikin turakarta sai na dube ta cikin alamun matuƙar damuwa na ce "Ya ummina na ji a jikina cewa wannan gasa da aka sanya mana ita babu tabbacin zan yi nasara domin duk abin da zai kai ga a samu nasarar 'yan uwa sun ɗara ni wato jarumtaka da ƙarfin sihiri".
Koda jin wannan batu daga bakina sai murmushi mai taushi ya suɓucewa mahaifiyata al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan na dube ta nace "Ya ummina shin ina dalilin wannan murmushi na ki?.
Dajin wannan tambaya sai mahaifiyata ta yi buɗe baki ta ƙura mani idanu ko kiftawa bata yi ta fara magana a karo na farko "Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa haƙiƙa bani da wani buri da huce naga cewa kai ne ka gaji sarki ba 'yan uwanka ba, kuma dukkan maganar da ka faɗa tana kan gaskiya,
Abin da ya sanya ni murmushi kuwa shi ne kana tare da abin da yafi na 'yan uwanka kuma matsawar ka yi riƙo da shi zai zaka samu nasarar cinye wannan gasa",
Cikin matuƙar mamaki na dubi ummina na ce "Ya ummina shin ina dalilin wannan furuci na ki kuma wane abubuwa ne nake d su wanda idan na riƙe su zan samu nasara?,
Ummina ta ce "Ya ɗana ka yi sani cewa tun da na mahaife ka na tabbatar da cewa na haifi yaro nagari kuma mai nasara a rayuwa, tun kana yaro ƙarami na fahimci halayen ka masu kyaune saɓanin 'yan uwanka,
Ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya komai kake taƙama da shi akwai wanda ya huce ka domin masu iya magana na cewa "Kamai sammakon ka wani a hanya ya kwana"
Wato idan jarumta, sihirin tsafi ko ƙarfin mulki kake taƙama da su cewa sune zasu bada nasara a cikin 'yan uwanka akwai waɗanda suka shafe ka,
Abin da kake da shi wanda 'yan uwanka basu da shi da idan ka rike su zaka samu nasara su ne kamar haka,
Gaskiya, Tausayi, Amana da hakuri waɗannan sune halaye mafi daraja da dukkan wanda ya riƙe su zai cimma nasara a rayuwar shi kuma babu wani abu da zai sanya a gaban shi face ya samu nasara,
Gaskiya dai zata ƙara maka daraja da ɗaukaka a cikin dukkanin harkokin rayuwa kuma ita ce ke bayyanawa jama'a darajar da mutumtakar ɗan Adam,
Tausayi kuwa na sanya soyayyarka a cikin zukatan al'umma har da maƙiyan ka,
Amana kuwa na ƙara wa maka ƙima da daraja a cikin kowacce irin al'umma ka shiga,Hakuri kuwa zai sanya ka cimma nasara a dukkan abin da ka sanya a gaba, domin duk kyawun abu idan baka yi hakuri ka cimma karshen shi ba to abu biyu zai faru,
Da farko shi ne zaka rasa wannan abun, sannan ka yi asarar lokaci da lafiyar da ka ɓata a kan shi,
Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa waɗannan halaye sune sinadaran shaharar duk wani tauraro a duniya, Na so a celokaci bai kure ba da baka tsakure daga hikayar jarumi Masnur ibn Abdullah da wani fasihin marubucin hikayoyin wannan ƙarni wato Sufi ya tattara kuma ya sanya littafin suna KUNDIN HIKAYA,
Tabbas da zaka ƙara tabbatar da batu na kuma ka ƙara ƙanƙame halayen da kyau".
Lokacin da na ji wannan dogon jawabi daga bakin ummina sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ban sa'adda na rungume ta ba ina mai cewa haƙiƙa na aminta da ke ummina ɗari-bisa-ɗari, da yardar abin bauta ba zan ketare wannan wasiyya ta ki ba, kuma zan samu nasara bisa abin da na fita nema fatana na dawo na same ki cikin ƙoshin Lafiya".
Sa'adda da na zo nan azance na sai mu duka biyun muka fashe da kukan farin ciki, dakyar da siɗin goshi muka rabu da juna suna masu zubar da hawayen baƙin ciki na shaƙuwa da juna.
Lokacin da na isa fada sai na tarar dukkan 'yan uwana sun hallara ni kaɗai ake jira domin haka ina isowa sai aka ɗunguma izuwa wajen fada muka kama dawakai muka haye dake dauke da abin guzuri, kai tsaye boka Jauwad tare da magajin gari Shuraih haɗe da sauran mutanen gari suka yi mana rakiya har zuwa bakin iyakar gari suna masu yi mana fatan samun nasara,
Lokacin da muka nausa zuwa cikin daji sai muka cigaba da tsala gudu a bisa dawakai sai da muka shafe tsawon sa'a ɗaya muna tafiya babu sassauci lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta cika a dai-dai wannan lokaci ne mu ka iso wata mararraba a dajin da ta kasu gida huɗu,
Sai yarima Zafiyar ya durfafi hanyar yamma, Laswil kudu, Rumailat arewa sai ni kuma na yi gabas, dukkan 'yan suna kallon juna cikin matuƙar ƙiyayya amma ni sai na dunga sakar masu tattausan murmushi a haka har mu ka ɓacewa juna da gani.
Lokacin da cigaba da tafiya a cikin dajin sai na wanzu ina tsala azababban gudu a bisa dokina ta hanyar ratsa duwatsu, ƙoramu, bishiyu da sarƙakiya,
Sai da na shafe tsawon sa'a biyar ina wannan tafiya a dai-dai lokacin ne na fahimci cewa dokina ƙarfin gudun shi ya ƙaru ainun domin haka sai na ja linzamin shi na tsaya cak! na sauka ƙasa na zauna a ƙarƙashin wata itaciya na fito da abin guzuri na domin na yi kalaci shi kuma dokina ya shiga yin kiwo yana cin ciyayin da ke dajin,
Ina cikin yin kalacin ne kwatsam bazato babu tsammani sai na ji kwantsama wata tsawa gami walƙiya cikin ƙankanin lokaci sararin samaniya ta canza launi izuwa baƙi,
Cikin wani irin baƙin zafin nama na miƙe tsaye zumbur gami da mayar da abin kalacin izuwa cikin jakar guzuri na gami da zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayana,
Kwatsam sai na ga dokina ya faɗi ƙasa ƙasa yana shure-shuren mutuwa, Cikin kaɗuwa na ruga zuwa inda ya ke kafin na isa har rai ya yi halin shi, cikin matuƙar takaici na tsugunna a gaban shi cikin alhini a lokacin ne na lura cewa wani irin baƙin ruwa mai yauƙi na fitowa daga bakin shi, koda na shin-shina ruwan sai na ji alamun akwai guba a cikin shi hakan ya sanya na fahimci cewa tabbas ciyawar da ke dajin ita ce ke ɗauke da wannan guba,
Cikin matuƙar fushi na miƙe tsaye zumbur gami da kwarara wawan ihu, faruwar hakan ke da wuya sai duhun da ke sararin samaniya ya washe tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Kwatsam! sai wani ƙaton kai mai ɗauke da kawo biyu da fala-falan kunnuwa irin na Zomo haɗi baki irin na jemage ya faɗo tim, sannan hannaye, kafafuwa, gangar jiki suka biyo baya, ko da ganin hakan sai na ƙara riƙon takobina ina zuba idanun,
Sannu a hankali sai sassan jikin suka dunga haɗuwa da 'yan uwan su har sai da halittar surar ta kammala, kafin na ƙarewa surar kallo wani sulken yaƙi da makamai sun bayyana a gare ta,
A lokacin ne na fahimci cewa tabbas surar aljani ne ba bil'adama ba saboda waɗansu fuka-fukai da suka bayyana a gwiɓin hammatarsa guda biyu,
Tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin halitta mai kwarjini da ban tsoro tamkar halittar ba domin haka sai yanayin tsoro ya kama ni har gumi ya fara tsattsafo mani a fuska amma saboda ƙi faɗi Irin ta 'ya'yan sarakai sai na basar.
Ko da aljanin ya lura da hakan sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, Sai da ya yi dariyar ta ishe shi sannan ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da Saƙon mutuwa,
Kawai sai ya zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje ya yi ɗauki izuwa Kai na yana ihu da kururuwa mai firgitarwa,
Ko da ganin hakan sai nima na ruga gare shi domin tarar juna muna haɗuwa muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
Muka wanzu muna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA masu juriya a filin fama, Idan ka ɗauke sautin kaɗawar iskar dake sanya rassan bishiyu rangaji babu abin da kunne ke ji face ƙarar karafniyar makaman yaƙin mu da ke haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara mara daɗin saurare,
Sai da muka shafe tsawon rabin sa'a muna wannan baƙin artabu babu sassauci a lokacin ne na fahimci cewa tabbas na gamu da gamo na, Domin ƙarfin saran aljanin ya nunka nawa sau uku,
A wasu lokutan idan ya kawo mani hari idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa sannan na taso sama na mayar da martani,
A cikin wannan artabu ne aljanin ya kawo mani wani nagartaccen sara da nufin ya tsinke mani wuya, cikin zafin nama na sunkuya makaminshi ya sari iska, Kafin ya sake wani yunƙuri ya sake kawo mani wani harin a kwaɓin cinyata ta hagu duk ƙoƙarin da nayi domin naga na kaure amma sai da makamin ya yanke ni a cinya jini ya yi tsartuwa na kurma ihu sakamakon raɗaɗi da zugin da na ji.
Kafin cikar daƙiƙa ashirin ya samu nasarar yi mani raunuka biyar ɗaya a cinya biyu a kafaɗata ta dama sauran biyun a damtsen hannuna na hagu kowanne rauni na zubar da jini,
Nan fa wani irin zazzaɓi mai matuƙar zafi ya kama ni, jiri ya fara ɗiba ta ina faɗuwa ƙasa, amma saboda da JURIYA DA JARUMTA irin ta MAZAN JIYA sai na miƙe tsaye a haka na ci gaba da kare kaina ba tare da mayar da martani ba.
Lokacin da rabin sa'a da daƙiƙa ɗari biyu da hamsin ta shuɗe ana wannan artabu kwatsam! Bazato babu tsammani sai na wata hikima ta faɗo mani a rai, koda jin hakan sai na yi wuf na dunƙule hannuna ya kirɓawa aljanin naushi a kwiɓin hammatarshi saboda ƙarfin naushin sai da ƙashin hannun ya karye ya yi ƙara ruƙus! Aljanin ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji.
Koda na fahimci cewa ashe sam makami ba ya tasiri akan shi nan take na yi jifa da takobina na shiga kai mashi bugu da naushi hannu da ƙafa.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canja, nan fa yazamana cewa cikin ƙanƙanin lokaci na yi mashi jini-jina baya iya mayar da martani, kawai sai na yi wuf na kama wuyan shi na murɗe da ƙarfin tsiya, nan take na jefar da gawarshi gefe guda ko shurawa bai yi ba.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai na cika da matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa na ɗauki takobina na ci-gaba da tafiya ina takawa daƙyar bisa ƙafafuna na durfafi wata hanya, tafiyar daƙiƙa ɗari kacal nayi na iso wata ƙorama da ruwan cikinta yakasance garai-garai gwanin ban sha'awa, cikin matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa ya sanya hannayena biyu ina kamfatar ruwan ciki ina sha. Sannan na miƙe tsaye na durfafi wata bishiyar tuffa na tsinka na ci na ƙoshi.
A sannanne na ji ƙarfin jikina ya dawo kuma sanyi da zazzaɓin da nake ji sun rabu da ni.
Nan take na ci gaba da tafiya ina sake kunna kai izuwa cikin dajin ina tafiya cikin hanzari.
Tsawon kwanaki uku na shafe ina tafiya a ranar kwana na ukun ne na iso izuwa gabar wani ƙaramin tsibiri mai ɗauke da bukka guda ɗaya jal, a gaɓar tsibirin wani makeken kogi ne mai tsawon gaske da ba a iya hango ƙarshen shi. Nan take na fahimci cewa ba zai yiwu na iya ƙetare wannan kogi ba face na ha samu kwale-kwale, don haka sai na isa izuwa bakin wannan bukka na yi gyaran murya har sau uku. Jim kaɗan sai ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wani dattijo dogo mai matsakaicin kaurin jiki ma'abocin kamala da haiba sanye da jajayen tufafi a hannun shi yana dogare da wani kwagiri. Sannu a hankali ya tako da ƙafafuwanshi har yazamana ya iso daf da ni ya ƙura min idanu.
Fuska ta cike da annuri na dube shi na yi gyaran murya na ce "ya kai wannan dattijo ma'abocin kamala ni matafiya ne hanya ta biyo da ni domin nemo wani abu mai matuƙar alfanu gare ni, ina so ka taimake ni da jirgin ruwan da zan iya ƙetare wannan kogi, kasancewar na rasa abin hawa na?
Koda jin wannan tambaya sai dattijon ya buɗi baki ya yi gyaran murya cikin kakkausar murya ya ce "ya kai
👍
❤️
5