SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL WhatsApp Channel

SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL

253 subscribers

About SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL

Zauren littafan Yaki na Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki,

Similar Channels

Swipe to see more

Posts

SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/14/2025, 8:57:29 AM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI Following 👉 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s Babi na shida A ranar da tafiya kogon GARUL-SHAMMAR ta zo mun sha kukan baƙin cikin rabuwa da mahaifina, tamkar ba za mu ƙyale shi ya tafi ba. Tun daga wannan rana ummina ce ke ɗawainiya da rayuwata, kullum cikin kewar abbanmu nake, wasa-wasa sai gashi ya shafe tsawon mako uku ba tare da mun ji ɗuriyar shi ba, al'amarin da ya sanya mahaifiyata ta fara tsammanin ko ya rasa rayuwarshi ne. Al'amarin abbana kuwa tun sa'adda mu kayi bankwana muna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, sai kawai ya kunna kai izuwa cikin daji yana tafiya cikin hanzari, tafiyar daƙiƙa hamsin kacal ya yi ya iske su sarki Fitinatul-muluk zaune a bisa kan wani narkeken aljani mai matuƙar kwarjini muni da ban tsoro shi kaɗai suke jira, ba tare da wani ɓata lokaci mahaifina ya haye bisa kan aljanin ya zauna kamar yadda sarakunan suka yi. Cikin kuzari aljanin ya buɗe manyan fuka-fukanshi ya luluƙa izuwa sararin samaniya yana mai keta gajimare cikin matuƙar sauri tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. Tafiyar sa'a uku kacal aka yi aka iso tekun Bahar-rum, cikin hanzari aljanin ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luhh! Ya sauka a dai-dai ƙofar shiga kogon, cikin hanzari sarki Ayumul-barƙas ya fara sakkowa sai Fitinatul-muluk, Hubaizu, Abul-uyum mafarauci Yasiran ne a ƙarshe. Ba tare da wani jinkiri ba sarakunan suka zira hannayensu a aljihun rigar su sai ga shi kowannen su ya fito da ɓarin kubarshi, fuskokinsu cike da murmushin mugunta suka haɗa su a waje guda, faruwar hakan ke da wuya sai aka kwantsama wata tsawa da walƙiya a sararin samaniya, kubar ta kammala jikinta baki ɗaya. Fuska a murtuke babu annuri sarki Fitinatul-muluk ya miƙawa abbana kubar ya sa hannu ya ƙarba, sannan ya dube shi fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce "ya kai Yasiran kayi sani cewa wannan kuba ta Miftahul-sihir da muka baka da ita ne zaka buɗe kofar wannan kogon dutse har ka samu nasara ɗauko KUNDIN AL'AJABI daga cikin shi". Koda jin wannan daga bakin Fitinatul-muluk sai mahaifina ya yi jim! Tamkar mai tunanin wani abu, koda ganin halin da mahaifina ya shiga sai sarakunan suka bayyanar da murmushi akan fuskokinsu, da ganin hakan sai abbana ya ji ya samu nutsuwa kawai sai ya juya ya durfafi ƙofar kogon GARUL-SHAMMAR yana isa ya sanya kubar a cikin wani kwaroron rami da ke jikin makekiyar ƙofar kogon da aka yi ta da zallar mulmulallan baƙin ƙarfe, ya murɗa kubar sau huɗu da dukkan ƙarfin shi, take sakatun suka shiga ƙara, zuwa can sai ƙofar ta yi wani ƙara da ya cika dajin baki ɗaya, sannan ta buɗe kanta, wani irin tururin hayaƙi ya surnano daga ciki, ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, mahaifina ya kunna kai izuwa cikin kogon tare da sanya kubar Miftahul-sihir a cikin aljihunshi, lokacin da ya kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!. Daga ciki kogon GARUL-SHAMMAR ya kasance makeke mai matuƙar tsawo da faɗi, yana ɗauke da saƙarƙaƙiya da lunguna, gaba ɗaya gine ginen dake ciki an yi su ne da waɗansu manyan duwatsun wuta masu ƙwarin gaske, gaba ɗaya kogon dutsen a haskake ta yadda koda allura ce ta faɗi a ƙasa da ya duba zai gani, kuma a ƙasa a zube akwai kwarangwal ɗin bil'adama da wasu halittu gasu nan birjik. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, inda a ce abbana ya san abin da zai faru da bai ya gangancin kutsawa kai cikin kogon ba, domin abin da bai sani ba shine, waɗannan kwarangwal ɗin sun kasance tarin miyagun aljanu. Lokacin da ya zamana ya iso tsakiyar kwarangwal ɗin, nan take ruhikansu suka fara dawo jikkunansu kuma surar tana haɗuwa, kafin cikar daƙiƙa hamsin baki ɗaya halittun sun miƙe tsaye. Aljanun sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawan farko, jikkunansu irin na bil'adama ne amma kawunansu irin na tsuntsun batoyi ne, idanuwansu jajur suke tamkar garwashin wuta, a ƙugunsu suna maƙale da wata murtukekiyar jela irin ta kada, sannan dukkanin suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro, a hannayensu suna ɗauke da waɗansu irin makaman yaƙi masu kama da zarto. Haƙiƙa Waɗannan aljanu sun kasance ababan tsoro da razani ga duk wata halitta mai numfashi. Lokacin da mahaifina ya yi arba da halittun sai jikinshi ya kama tsuma yana kyarma saboda matuƙar tsoro, amma sai ya yi wuf! Ya zare takobinshi aka fara kallon-kallo tsakani, tsawon daƙiƙa arba'in ɗayan su bai yunƙurin afkawa abokin gwamin shi ba. A lokaci guda tamkar haɗin baki dakarun suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan Yasiran suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, tare da kai mashi miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Take mahaifina ya tare su aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a lokacin da dakarun suka yanyame shi tamkar yadda dandazon ƙudaje ke yanyame ƙwallon mangwaro. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka saba gwagwarmaya a filin fama, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihu da hargowar dakarun aljanun ta cika kogon baki ɗaya, kuma kogon ya ɗauki zafi ainun, tamkar zai yi bindiga ya tarwatse, sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari uku ana wannan ɗauki ba daɗi. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa aljanun kai kenan kuma ya ba su mamaki, domin fiye da shekaru dubu biyu suna gadin wannan kogon na GARUL-SHAMMAR ba su taɓa ganin halitta mai matuƙar zafin nama da ƙwarewar yaƙi tamkar na mahaifina ba. Al'amarin mahaifina kuwa lokacin da ya fahimci cewa babu alamun nasara, kuma koda alamun gajiya babu a tare da dakarun sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita, koda samun mafitar sai kawai ya mayar ta takobinshi izuwa cikin kube, ya yi wuf ya zaro kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan dakarun da ita da dukkan ƙarfin shi. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa abbana ya gano lagon tsuntsayen ya zamana cewa duk wanda ya daka da kubar sai kaga ya kurma wawan ihu ya tarwatse, nan fa ihu da kururuwar shaiɗanu ta ƙara cika kogon, kafin shuɗewar rabin sa'a, nan fa dakarun suka ɗimauce suka kama guye-guje da ifice-ifice, wasu suka shiga ƙoƙarin ƙwace kubar Miftahul-sihir daga hannun abbana, wasu na kai mashi sara da suka cikin matuƙar zafin nama, domin ganin sun kai shi ƙas. Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin aljanun ya shammaci mahaifina ya kafta mashi sara a cinya, take inda ya yanke shin ya dare jini ya yi tsartuwa, abbana ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA sai ya ci gaba da yaƙin a haka ba tare tsaida zubar jinin ba, haka ya ci gaba da yaƙin jiri na ɗibar shi a wasu lokutan har yanke jiki yake ya faɗi ƙasa amma sai ya miƙe tsaye zumbur ya ci gaba da yaƙin a haka. Kaico! Haƙiƙa jarumtaka baiwa ce daga Ubangiji, dukiya, mulki basu bayar da ita face baiwa daga Allah, komai hassadar mutum idan ya ga yadda mahaifina ke ragargazar dakarun cikin baƙin zafin nama da kafin tsiya, dole ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya cika gwarzon mayaƙi mai ƙarfi na Allah ya isa. Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA YAFI SARKIN ƘARFI qna cikin wannan artabu ne mayaƙan suka samu nasarar kai abbana ƙasa suna niyyar hallaka shi, koda ya ga irin mawuyacin halin da yake ciki da yake tsakanin RAYUWA DA MUTUWA, bai san sa'adda ya buga kubar Miftahul-sihir a ƙasa ba, faruwar hakan keda wuya nan take wani farin haske ya yi fitar burgu daga kubar, ya shiga sassan jikkunan sauran aljanun, nan take suka kama ci da wuta suna ihu da kururuwa neman taimako, kafin wani lokaci mai tsawo baki ɗayan su sun sheƙa barzahu. Cikin matuƙar farin ciki abbana ya miƙe tsaye da ƙyar ya sake kunna kai izuwa cikin kogon, Tsawon daƙiƙa ɗari huɗu yana tafiya sannu-sannu, lokacin da rabin sa'a ta shuɗe a dai-dai lokacinne ya ya iso wani waje mai tsananin sanyi, hatta durakun dake wajen na dusar ƙanƙara ne, babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafarshi face dusar ƙanƙara ce. Sa'adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin wannan hali sai hankalinshi ya dugunzuma ainun, domin baya sanye ɗauke da rigar kariya daga sanyin. Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya kama mahaifina jikinshi ya kama ƙyarma, tun yana iya takawa da ƙafafuwanshi har ya zamana ya zube a ƙasa magashiyan nunfashin shi na fita daƙyar. Yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai wani irin ƙatuwar halitta tayo fitar burgu daga dusar ƙanƙarar ta fito waje, Ita dai halittar takasance wata shirgegiyar macijiya mai kauri tamkar bishiyar kuka, jelar murtukekiya ce, bayan ƙaton kanta tana ɗauke da ƙarin wasu guda biyu, na farko yakasance na zaki, ɗayan kuma na raƙumin dawa. Kaico! Wannan halitta ta kasance mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, babu wani jarumi da zai yi arba da ita face ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa. Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na bakwai Domin jin wannan ƙayataccen labari. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071

❤️ 👍 5
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/15/2025, 10:24:03 PM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI GWARAZAN JIYA KUNDIN AL'AJABI Following 👉 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s Babi na bakwai A can bakin ƙofar shiga kogon GARUL-SHAMMAR sarakunan duniya huɗu suna tsaitsaye suna jiran fitowar mahaifina fuskokinsu a murtuke babu annuri cike da matuƙar kiyayyar juna. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai suka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar DARE UKU ne ya haɗu waje guda mutum koda tafin hannunshi baya iya gani. Sannu a hankali duhun dake sararin samaniya ya fara raguwa, sai ga waɗansu halittu masu tarin yawa suna ketowa daga cikin gajimare suna sauka a kan tekun Bahar-rum. Koda ganin hakan sai sarki Fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka yi wuf suka fito da maduban tsafin su suka shiga gudanar da bincike, koda kammala binciken sai suka taƙarƙare suka bushe da dariyar mugunta, ba komai suka gani ba face halittun da suka bayyana sun kasance rundunar sarakunan duniya biyu, sarkin aljanu baƙaƙen fata da farare. Sun turo tawagar ne domin su ƙwaci KUNDIN AL'AJABI da kubar Miftahul-sihir da zarar mahaifina ya samu nasarar ɗaukowa. Sarki Hubaizu na birnin Hindu ya katse shirun da ya wanzu a q hanyar duban sauran 'yan uwanshi fuskarshi a murtuke babu annuri ya ce "yaku manyan abokan gaba a gare ni ku yi sani cewa waɗancan dakarun aljanu da suka bayyana ba su ba ne face Tawagar sarakunan aljanu da suka zo domin ɗaukar kubar Miftahul-sihir haɗe da KUNDIN AL'AJABI, saboda haka yanzu dole mu haɗa kai mu kawar da waɗannan sabbin abokan gaba, idan ya so daga baya kuma sai a raba rai tsakanin mu ga wanda zai zamo zakara a, da zai zamo mamallakin KUNDIN AL'AJABI". Koda jin wannan batu daga bakin sarki Hubaizu na birnin Hindu sai sauran sarakunan uku suka zare makaman yaƙin su suka yi ɗauki kan dakarun aljanun, koda ganin hakan sai aljanun suka tare su suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. *** A cikin kogon GARUL-SHAMMAR kuwa kafin mahaifina ya yi wani yunƙuri wannan macijiya ta kafta masa sara a hannayenshi da ƙafafuwanshi, nan take nunfashin shi ya fara sarƙewa kuma ya faɗi ƙasa magashiyan". Lokacin da kyakkyawar baƙuwar jaruma ta zo dai-dai nan a labarin da take bamu sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta. Al'amarin da ya sanya jikinmu ya yi sanyi ni da Raudat har ƙwalla ta zubo mana. Cikin alamun matuƙar tausayi na dubi jarumar na ce "haƙiƙa labarin mahaifinki cike yake da abun tausayi darasi da abubuwan al'ajabi. Kuma ya cancanta ki ɗauki ko wane mataki domin daukarwa mahaifinki fansa, duk da cewar ba mu ji ƙarshen abin da ya faru tsakanin abban ki da manyan sarakunan duniya huɗu ba, duk da cewar da farko mun nufi mu yaƙe ki, amma a halin na ji a raina ni da abokiyar tafiyata za mu taimaka miki ki cimma wannan buri na ki. Amma bisa sharaɗin cewa ba za ki cutar da wani mahaluki ba idan har kin samu nasarar mallakar makaman yaƙin sarkin bokayen duniya". Sa'adda na zo nan azance na sai fuskar baƙuwar jarumar ta faɗaɗa da murmushi mai taushi, ta dube mu sannan ta yi gyaran murya ta ce "ya ku waɗannan jarumai haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki da wannan taimako da za ku ba ni, kuma ina mai tabbatar maku da cewa ba za ku same ni da wani abu na cin amana ko yaudara ba. Kuma a halin yanzu ba zan iya ci gaba da ba ku labarin mahaifina ba sai dai anan gaba, sai dai ban sanar da ku suna na, mahaifna na kira da suna Sulairat bintu Yasiran". Sa'adda Sulairat yar mafarauci Yasiran ta zo dai-dai nan azancen ta sai na yafito aljani Jauharul-layal dake tsaye a gefe guda da hannu da ya iso inda muke, taku ɗaya kacal ya yi ya iso gare mu ba tare da wani jinkiri ba Raudat, Sulairat suka haye gadon bayan shi, take na yi koyi da su ina mai zama da daf da inda suke yazamana tazarar dake tsakaninmu bata huce kamu ɗaya ba, A halin yanzu tafiya ta sauya salo daga mutum biyu izuwa uku, wato ni Raudatul-abyad sai jaruma Sulairat. Sai da muka shafe tsawon sa'a huɗu muna keta gajimare cikin matsanan gudu na keta sa'a, ɗa ya daga cikin mu bai ce uffan ba, a wannan lokaci ne Raudatul-abyad ta lura da cewa Sulairat na satar kallo na lokaci zuwa lokaci, koda ganin hakan sai ta daka mata wata harara dake nuna tsantsar kishi da soyayya. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai mu ka ga aljani Jauharul-layal ya tsaya cak! A sararin samaniya, cikin fushi Raudatul-abyad ta dube shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "ya kai Jauharul-layal shin ina dalilin wannan tsayuwa ta ka bayan ka san cewa muna so mu isa fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar cikin sauri ? Koda jin wannan tambaya sai Jauharul-layal ya risina cikin ladabi ya ce "ki gafarce ni ya shugabata bakomai ne ya sanya na dakatar da tafiya ba face bisa jiyo ƙanshin 'yan uwana aljanu a daf da mu, hakan ya tabbatar min da cewa akwai waɗanda ke biye da mu…" Karfin jauharu ya gama rufe bakinshi kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ga tawagar waɗansu zaratan aljanu kimanin dubu hamsin, sun bayyana a suna masu yi mana ƙawanya, su dai aljanun sun kasance bakaƙe wuluk, masu girma, kwarjini da munin gaske, fuka-fukansu irin na mikiya ne, a gadon bayansu suna ɗauke da wani ƙusumbi da ya tamkar duwatsu aka saka masu, duk sa'adda da suka buɗe bakunan sai wani ruwa mai yauƙi mai warin gaske ya zubo. Baki ɗayan su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, kuma girman kowannen su ya ninka na aljani Jauharul-layal sau goma. Wohoho! Haƙiƙa waɗannan tawagar ifritai ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, nan fa muka zo tamkar an ajiye kyanwa a gaban garken raƙuma. Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na 8 Domin jin wannan ƙayataccen labari. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071

❤️ 👍 4
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/17/2025, 11:33:10 AM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI GWARAZAN JIYA KUNDIN AL'AJABI Following 👉 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s BABI NA TAKWAS Lokacin da boka Matawus yazo dai-dai nan a hikayar da yake bawa sarki Sabrul-marhut sai ya ja dogon goron numfashi sannan ya ɗora da cewa. Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakanin mu na tsawon daƙiƙa arba'in sai daga bisani ne shugaban tawagar ifritan aljanun ya ratso ta tsakiyar ya matso daf da mu ya dube mu da turɓunanniyar fuskarshi da ninka ta sauran muni, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya ce "ya ke Raudatul-abyad tare da tawagarki kiyi sani cewa yau tsawon shekaru dubu da ɗoriya ina jiran zuwan wannan rana da zan karɓi taswirar fadar sarkin bokaye daga hannunki, tsawon shekaru ina bibiyar mahaifinki domin ya mallaki taswirar amma saboda sirrin dake tare shi ban samu wannan dama ba sai a yanzu". Koda jin wannan batu daga bakin shugaban tawagar sai Raudat ta tari numfashinshi tana mai daka masa tsawa ta ce "ya kai wannan rafkananne kuma tsohon AZZALUMI ka yi sani ce wa, ire-iren ka ba za su taɓa cimma buƙatar su domin mallakar wannan taswira ba, domin shimfiɗa BAƘIN ZALUNCI, shawara ɗaya zan baka ita ce ka janye waɗannan 'yan tsakin mayaƙan na ka, idan kuwa ba haka ba zaka yabawa aya zaƙinta…". Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-abyad sai shugaban tawagar ya fusata ainun jikinshi ya kama tsuma ya ƙyarma tamkar mazari, idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur, ya buɗi baki a karo na biyu cikin matuƙar fushi har wani irin tururin baƙin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinshi, baki da kunnuwa ya ce " kaicon ki yake wannan ƙaramar ƙwaruwa haƙiƙa kin tafka babban kuskure, wanda ba zan iya yafe miki ba face na shayar dake gidauniyar azabata da dukkanin abokan tafiyar ki, sai dai kafin hakan akwai buƙatar na sanar dake wane ne ni, da farko dai suna na ifritu Sulsainil-auman ibn Turbus, shugaban ifritan aljanun duniya baƙaƙen fata. Da wannan nake yi miki bankwana ga maza nan bisa kan ki". Koda shugaban ifritai Sulsaini ya zo nan a zancen shi sai ya yi ihu da kururuwa mai firgita GWARAZAN JIYA a FAGEN FAMA ya afka Raudatul-abyad, take sauran yaran shi suka afka mana ni da Sulairat da Jauharul-layal. A can ƙololuwar sararin samaniya inda Allah (SWT) ya yiwa dukkan halittu iyaka kuwa, anan ne uwar mayu Ummul-sharri ta kafa fadarta domin gudanar da ƙasaitaccen mulkinta, A wannan lokaci Ummul-sharri tana zaune a bisa karagar mulki a cikin gawurtacciyar fadarta, Ita dai fadar ta ƙasaitacciya tamkar gari guda, gaba ɗaya ginin fadar an yi shi ne da zallar waɗansu irin duwatsu masu ƙwari gaske suna sheƙi da ƙyalli tamkar gilashi, duk inda mutum zai ajiye ƙafarshi wani irin koren gilashi ne mai kama da darduma, idan mutum ya kalla yana iya ganin surarshi, gefe guda kuwa 'yan majalisa na jinsin mutum da aljan na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma, a kowa ce kusurwa a fadar dakarun tsaro ne na jinsin mutum da aljan ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikakken tsaro, a bisa wata matattakala mai hawa goma anan aka ajiye karagar mulki da aka yi ta da sallar jauhari, kai tsayawa masalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce hankali, kai wani abun ma ko jin sunan shi bai taɓa yi ba, kana gani ka san aiki ne na sihiri. Shiru ne ya mamaye wajen tamkar mutuwa ta kawo ziyara, uwar mayu Ummul-sharri ce ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar sanya hannunta a aljihun rigarta ta ɗauko madubin tsafinta da girmanshi bai zarce faɗin tafin hannuna ba, ta shafe da hannunta na hagu gami da runtse idanuwanta ta karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama furtawa sai ga taswirar gumurzun dake wanzu tsakanin tawagar ifritu Sulsainil-auman da su jarumai Raudatul-abyad ya bayyana a kan madubin. Koda ganin hakan sai uwar mayu ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, mai kama da haniniyar dawakai, sautin ta ya mamaye fadar baki ɗaya, al'amarin da ya firgita wasu daga cikin jama'ar fadar kenan cikinsu ya ɗuru ruwa, domin sun san cewa duk sa'adda uwar mayu tayi wannan dariya to za ta zartar da wani baƙin zalunci, tsawon daƙiƙa arba'in tana cikin wannan hali sai daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da WASIƘAR AJALI, kawai sai ya mayar da madubin izuwa ma'ajiyar shi, kana ta dawo da dubanta zuwa ga wani mummunan aljani daga cikin 'yan majalisarta, tamkar ya san abin da take nufi kawai sai ya miƙe tsaye ya matsa daf da karagar mulki ya zube ƙasa ya yi sujjada a gare ta, sannan daga bisani ya ɗago kanshi a ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "gani gare ki ya SARAUNIYA MAI DUNIYA, gajimare kike mai shayar da duniya mugunyar annoba. Guguwar musiba mai share TAWAGAR ZARATA. ina gagararre ko hatsabibi ya zo ga GAWURTACCIYA uwar matsafan dunya" Kin ci dubu sai ceto kin yi KARO DA DUBU kalacen safe, ina mazan suke ne ga sa gudu maganin ƙi gudu" ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya ja dake zai baƙunci barzahu". Lokacin da ɗan majalisar ya zo nan a kirarin na shi sai uwar mayu ta yi murmushi mai kama da yaƙe da ya ƙara tona asirin munin fuskarta, bisa jin daɗin kirarin da yake yi mata. Sannan ta buɗe tafkeken bakinta mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora baƙaƙe babu kyawun gani ta ce "an gaishe ka ya kai Darmanu maganin ƙananan ƙwari abin da nake so a gare ka shine ka tafi cikin hanzari izuwa gaɓar dajin Zarutul-shammar domin ka ƙwato min taswirar fadar sarkin bokaye a hannun jaruma Raudatul-abyad, ina mai farin cikin sanar da kai cewa burina ya kusa cika na shiga fadar sarkin bokaye domin na gaje komai nashi, sirrikan tsafi da kayan yaƙinshi, dole ne duniya ta zamto a tafin hannuna, na juya ta tamkar yadda ake sarrafa waina a tanda, Wannan ita ce dama ta ƙarshe a gare mu domin shiga fadar sarkin bokaye don haka ina mai gargaɗarka ka kula sosai kar a samu kuskure a cikin wannan aiki”. Sa’adda Uwar mayu Ummul-Sharri ta zo nan a jawabinta sai aljani Darmanu ya risina ya ce “an gama ya shugabata wannan aiki abu ne mai sauƙi a gare ni tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai”. Ummul-Sharri ta ce “tsafi ya baka kariya ka dawo cikin aminci ya kai Darmanu”. Koda gama faɗin hakan sai Darmanu ya risina ga uwar mayu sannan ya rikiɗa izuwa wani baƙin haske ya ɓace ɓat daga fadar tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Wannan shi ne abin da ya wakana a fadar uwar mayu ta duniya matsafiya Ummul-Sharri. Lokacin da muka kacame da azababban yaƙi tsakaninmu da shugaban ifritai Sulsaini da yaranshi sai muka wanzu muka kaiwa juna hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, ana fara wannan artabu ne dukkaninmu suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin matuƙar zafin nama gami da ƙarfin damtsen ifritan ya ninka namu sau biyar, babban abin da ya dugunzuma hankalinmu shine yadda duk sa'adda makaman yaƙinmu suka sari jikkunan ifritan sai mu ji tamkar dutse muka sara, ko gezau ba sa yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara ƙal! Ƙal!. A duk sa’adda makaman yaƙinmu suka haɗu da juna sai ka ji an kwantsama wata tsawa gami da walƙiya, nan fa sararin samaniyar ya cika da ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu gami da hargowar MAZAJEN DUNIYA. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu da goma ana wannan ɗauki ba daɗi babu sassauci. A cikin wannan artabu ne na fahimci Sulairat tafi mu ƙarfin damtse da salon dabarun yaƙi, domin a hankali yanzu tana iya samun nasarar yankan jikkunan ifritan, koda suka fahimci irin ɓarnar da Sulairat ke yi masu sai suka yanyame ta suna kai mata sara da suka gami da yakushi da faratansu. A ɓangaren aljani Jauharul-layal kuwa ya wanzu yana kai FARMAKI da fuka-fukanshi, bakinshi gami da faratan hannunshi, cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Lokacin da shugaban ifritai Sulsaini ya ga cewa sa'a ɗaya ta shuɗe ana wannan baƙin artabu sai ya fusata ainun zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone, ya fahimci cewa wankin wula zai kai su dare, wani abu da ya fusata shi shine tun da yake yin GABA DA GABA da jarumai bai taɓa haɗuwa da bil’adama masu matuƙar zafin nama da ƙarfin damtse tamkar mu ba. Lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi, sai ƙarfin damtsenmu ya fara raguwa yaran ifritu Sulsaini suka fara galabaitar da mu, faruwar hakan ke da wuya sai Aljani Sulsaini ya yi ƙara luhhh! Domin ya zillewa ifritan, amma sai hakan ya faskara domin kadoni ya kai ga hakan wani daga cikin ifritan me nacin tsiya ya kafta masa sara a kafaɗarshi, saboda matuƙar ƙarfin sara sai da Jauharul-layal ya kurma wawan ihu, saboda raɗaɗi da zugin da ya ji. Sa’adda jaruma Sulairat taga halin da muke ciki, kuma ta fahimci cewa a koda yaushe ɗayanmu na iya raya rayuwar shi, sai kawai ta shiga amfani da ƙarfin shirin tsafi amma ya zamo a banza, domin da idan ta yi TSATSUBA ta turawa ifritan Kibbau na huta da zarar sun doshi inda suke sai suka zama farin haske su ɓace ɓat! Ana cikin wannan wannan fafatawa ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya tayi duhu dunɗum! Tamkar DARE BIYU ne ya haɗu waje guda, kuma aka dinga kwantsama tsawa da walƙiya kai ka ce za’a kece da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya. Daga can sai aka ga wata shirgegiyar halitta ta bayyana a sararin samaniya, halittar tana da matuƙar girma fiye da aljani Jauharul-layal, tana ɗauke da fuka-fukai goma a tsakiyar kanta tana ɗauke da wani zabgegen ƙaho mai kama da na rago, batun munin fuskarta kuwa sai abin da idanu suka gani kawai, a gadon bayanta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi. Kaico! Haƙiƙa wannan halitta ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Darmanu manzon uwar mayu Ummul-Sharri, wanda ta tura domin ya ɗauko mata taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar. Sa’adda kowa ya yi arba da aljani Darmanu sai aka tsayar da yaƙi kallo ya koma kanshi. Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo sai daga bisani aljani Darmanu ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da saukar aradu wacce ta ɗimauta duk wata halitta dake wajen hatta ifritu Sulsaini da yaranshi, a lokaci guda ya tsuke bakinshi ya fara magana cikin wata irin kakkausar murya mai kama haniniyar doki yana mai cewa “Ya ku waɗannan ƙananan halittu ma’abota ƘARAR KWANA ku yi sani cewa ban zo nan domin kallon fafatawar da kuke yi ba, face sai domin ya karɓi taswirar fadar sarkin bokaye domin na kaiwa uwar matsafan duniya Ummul-Sharri, kira na a gare ku shine ku gaggauta miƙo min taswirar cikin ruwan sanyi domin na yi maku kisa mafi sauƙi ba tare da kun sha wahala ba, ta hanyar da daddatsa sassan jikkunanku. Kafin Darmanu ya gama rufe bakinshi ifritu Sulsaini ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka masa tsawa ya ce “ ya kai wannan maƙetaci kuma wanda rarraunar zuciyarshi ke yaudarar sa ka ji sani cewa ka tafka babban kuskure, da kake tunanin za ka ƙwaci taswira daga hannun Jaruma Raudatul-abyad, bayan muna gab da mallakarta, wato kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi”. Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Sulsaini sai aljani Darmanu ya fusata ainun, idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe, kawai sai ya miƙa hannunshi izuwa sama sai ga wata zabgegiyar takobi ta bayyana ta haske, take ya yi ɗauki izuwa kan Sulsaini da tawagarshi, ana haɗuwa aka yi KARON BATTA, nan fa aka garƙame da sabon gumurzu mai matuƙar muni ban tsoro gami da tashin hankali, a wannan karon sai artabun ya canja salo, domin a wannan karon duk inda aljani Darmanu ya sanya a gaba sai dai kaga yaran ifritu Sulsaini na sheƙawa barzahu, takobinshi na raba sassan jikkunansu. Nan fa muka shiga raba idanu domin ba su san wane ɓangare zamu shigarwa yaƙin ba, tun da dukkanin su abokan gabarmu ne. Muna cikin wannan hali ne wata dabara ta faɗo min, koda samun mafitar sai kawai na yiwa aljani Jauharul-layal inkiya ta wutsiyaar idanu, koda ya fahimci abin da nake nufi sai ya faki idanun TAWAGAR ABOKAN GABA ya kaɗa fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! ya keta cikin gajimare ya fara tsala azababban gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya muka ɓace ɓat! Har muka daina hango so. Lokacin da muka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna gudun tsira da rayuka, sai ƙarfin gudun Jauharul-layal ya fara raguwa ainun saboda gumurzun da aka sha, domin hakan sai aka yanke shawarar mu yada zango domin mu huce gajiyar dake tattare da mu, cikin hanzari Jauharu ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! Ya sauka a turba, inda muka saukar ya kasance daji mai tattare da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu gami da sarƙaƙiya, muna sauka ne dukkaninmu kowa ya sha jinin jikinshi, domin da ganin dajin ba a rasa miyagun halittu masu cutarwa ba. Da yake akwai inuwar bishiyu sai ya zamana cewa bamu kafa tanti ba, aka fito da abin kalaci kowa ya shiga kimtsa cikinshi. A wannan lokaci ne jaruma Sulairat ta duba mu tayi gyaran murya sannan ta ce “tun da a halin yanzu dukkaninmun mun samu natsuwa zan cigaba da baku labarin abin da ya wakana da abbana tare da manyan sarakunan duniya uku, inda ta ɗora da hikayar kamar haka:- Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na 8 Domin jin wannan ƙayataccen labari. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071

❤️ 👍 🙏 5
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/18/2025, 7:28:56 AM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI GWARAZAN JIYA KUNDIN AL'AJABI Littafi Kuɗi ne ₦400 8137237071 Usman Umar Mansur Opay Following 👉 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s BABI NA TARA Sa’adda abbana ya yi arba da macijiyar sai jikinsa ya kama tsuma yana ƙyarma saboda matuƙar firgici, domin a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin halitta mai matuƙar kwarjini da muni tamkar macijiyar ba. Kafin ya yi yunƙuri ta kafta masa sara a dukkan sassan jikinsa, ya faɗi ƙasa magashiyan yana mai aman jini ta baki da hanci, kuma wani zazzaɓi mai zafi ya kama sa yana ƙyarma tamkar zai sheƙa barzahu. Koda samun wannan gagarumar nasara sai macijiyar ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, dariyar ta ta ta haddasa wata irin gagarumar iska. A lokaci guda ta tsuke baki tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa, sannan ta buɗe bakinta dake maƙale a jikin kanta mai siffar gwaggwan biri cikin wata irin kakkausar murya ta dubi abbana ta ce “ya kai wannan bil’adama ka yi sani cewa haƙiƙa kai mutum mai matukar sa'a da rabo a rayuwarsa, domin kai ne mahaluki na farko da ya shigo wannan kogo fiye da shekaru dubu uku domin ɗaukar littafin KUNDIN AL'AJABI, sai dai ina farin cikin sanar da kai cewa kai ne bil’adama na ƙarshe da zai sake shigowa wannan waje, yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba zan rugurguza ƙasusuwanka ka yi mutuwar wulakanci”. Koda tazo nan a zancenta sai ta sake bushewa da dariya a karo na biyu, kawai sai ta sanya jelarta ta kanannaɗe mahaifina ta ɗaga shi izuwa sama, sannan ta buɗe bakinta ɗaya ta jefa abbana ciki tayi loma ɗaya da shi ta rufe rufe! Tamkar ta haɗiye ƙwallon dabino. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu. In da ace wannan macijiya ta san abin da zai faru da bata haɗiye abbana ba, domin kuskuren da ta yi shine ta haɗiye shi tare da kubar Miftahul-sihir. Sa’adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin macijiyar sai nan take ya ji dukkan zazzaɓin dake jikinshi ya rabu da shi, tamkar a cire silin gashi daga cikin tandun mai, kuma ya samu ƙwarin jikinshi, nan take wata hikima ta faɗo mashi ya ɗauki kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan sassan cikin macijiyar. Kaico! Nan fa macijiyar ta shiga mawuyacin hali domin duk sa’adda abbana ya daki wani ɓangare a jikinta sai ta ji tsananin azaba tamkar da wuta ake ƙona ta. Nan fa ta shiga guje-guje da ifice-ifice a cikin kogon saboda matuƙar azabar da take sha, take ta shiga ƙaƙari ta amayo mahaifina daga cikinta ya faɗo ƙasa tim! Kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin jikin macijiyar ya sandare ya daina motsi, kuma wata ƙofa ta musamman ta bayyana a ƙarƙashinta, hatta tsananin sanyin dake kogon dutsen ya ɗauke. Cikin matuƙar farin ciki mahaifina ya miƙe tsaye cikin ƙwarin gwiwa ya kunna kai izuwa cikin wannan ƙofa hannunshi ɗauke da kubar Miftahul-sihir. A can gaɓar tekun Bahar-rum kuwa manyan sarakunan duniya haɗu da na aljanu gami da rundunoninsu sun wanzu suna bawa hammata iska. Nan fa manyan sarakunan huɗu, Abul-uyum, Ayumul-barƙas, fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka zamto tamkar GOBARAR DAJI a tsakiyar mayaƙan, duk inda ɗayan su ya sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa tamkar ana sassabe a gonar auduga, sun haddasa fili fetal. Nan fa gagarumar walima ta ɓarke a tsakanin halittun dake ƙarƙashin tekun, suka shiga watanda da sassan jikkunan dakarun. Babu abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure mashi kai face yadda gwarazan sarakunan huɗu ke fafatawa tamkar jikkunnansu ba su kasance na jini da tsoka ba. A ɓangaren sarakunan aljanu kuwa, koda suka ga irin ɓarnar da su sarki Ayumul-barƙas ke yi masu sai suka fusata ainun, kuma suka faɗa izuwa kogin tunani, abu na farko da ya faɗo masu a rai shine matuƙar basu canja salon yaƙin su ba, ba za su samu nasarar kawar da su Ayumul-barƙas, sannan ma inda kizo ke saƙar shine idan sun yi nasarar ta ya ya ɗayansu zai iya haƙura ɗan uwansa ya mallaki KUNDIN AL'AJABI tare da kubar Miftahul-sihir, daga can sai wata dabarar ta faɗo masu, dabarar kuwa ita ce su yaƙi junan su, idan ɗaya daga cikin su ya yi nasara sai ya shiga kogon Garul-shammar ya hallaka mahaifina, ya mallaki KUNDIN AL'AJABI da kubar Miftahul-sihir. Koda gama tunanin hakan sai sarkin aljanu baƙaƙen fata ya ɗaga hannunshi izuwa sama, sai ga wani makami mai kama da zarto mai tsini da kaifi tamkar takobi ya bayyana gare shi, koda ganin hakan sai sarkin aljanu fararen fata ya zare wani makami na sihiri a jikinshi mai kama da Adda mai KAIFI DA TSINI. A lokaci guda tamkar haɗin baki suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan juna suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, suna haɗuwa suka rungumtsume da azababben yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, duk sa’adda makamansu suka haɗu da juna sai a kwatsama wata irin razananniyar ƙara gami da tsawa, tamkar za’a kece da matsanancin ruwan sama. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce. “Idan ana babbakar Giwa wa yake jin ƙaurin ɓera” kuma tabbas “Sawun Giwa ya take na raƙumi”. Sa’adda waɗannan GWARAZAN SARAKAI biyu suka fara bawa hammata iska sai suka tashi hankalin duk wata halitta dake wajen, ba shiri dakarun dake daf! Da inda suke fafata artabun suka dinga yin ƙaura domin tsira da rayukansu daga sharrin shuwagabannin na su. Al’amarin mahaifina kuwa lokacin da ya shiga cikin wannan ƙofa dake ƙarƙashin wannan macijiya mai kawuna uku, sai kwatsam ya tsinci kanshi a cikin wani makeken waje mai ɗauke da manyan duwatsu, bishiyu gami da sarƙaƙiyar duhuwa, haka abbana ya ci gaba da tafiya a cikin wannan duhuwa har ya zamana ya shafe tsawon daƙiƙa ɗari uku, a dai-dai wannan lokaci ne kishi da yunwa suka addabi mahaifina, kuma dama ga shi ya jefar da jakar guzurin shi tun a wajen da ya fafata yaƙi da wannan macijiya. Yana cikin wannan hali ne ya hango wata bishiyar tuffa can nesa kaɗan da inda yake, cikin matuƙar farin ciki ya durfafi inda take, yana isa ya sanya hannunshi ya tsinki guda ɗaya ya kai bakinshi da nufin ya ci. Kawai sai ya ji an daka mashi tsawa, wacce ta sanya hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi. Abbana ya waiga gabas, yamma, kudu da arewa bai ga kowa ba. Al’amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan, kawai sai ya sake kai tuffar bakinshi karo na biyu domin ya ci, amma sai aka sake daka mashi tsawa, a wannan karon sai da firgita ya jefar da tuffar dake hannunshi. Kwatsam! Sai ga wata BAƘAR INUWA na ketowa daga cikin gajimare, lokacin da ta kammala sauka sai ta rikiɗa izuwa wani zabgegen maridi. Maridin ya kasance narkeke tamkar basamude yana da tafkeken kai irin na bil’adama, mai ɗauke da ido guda ɗaya jal! A tsakiyar goshinshi, ƙofofin hancinshi manya ne tamkar mazirari, yana makeken baki tamkar mazirari, ƙirjinshi makeke ne ya tara ƙwanji tamkar duwatsu aka cusa mashi a ciki, sangalalon hannayenshi da ƙafafuwanshi masu kauri ne tamkar bishiyar kuka, Kuma yana sanye cikin gagarumar shigar shigar yaƙi ta baƙin sulke mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a gadon bayanshi yana rataye da waɗansu zaratan adduna biyu masu kaifin tsiya. Kaico! Haƙiƙa wannan maridi ya cika GAGARABADAU, komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da shi, dole ne ya ɗimauce ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa. Sa'adda mahaifina ya yi arba da maridin, nan take ya ɗimauce jikinshi ya kama tsuma ya ja da baya. Maridin ya tako lafta-laftan ƙafafuwanshi ya durfafi inda mahaifina yake, duk sa’adda da ya ajiye ƙafarshi ɗaya idan akan dutse ne sai kaga ya nutse izuwa cikin ƙarƙashin ƙasa, ya yin da ya rage saura taku biyar tsakaninsu sai ya ja ya tsaya ya ƙarewa mahaifina kallo tun daga ƙasa har sama, nan take mahaifina ya zamto tamkar an ajiye ƙyanwa a gaban raƙumi, saboda matuƙar tsawon maridin. Daga can sai maridin ya wangame bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da gurnanin zaki ya dubi mahaifina ya ce “ya kai Yasiran ka yi sani cewa fiye da shekaru dubu uku a cikin halarar tsafina na gano cewa kai ne bil’adama mau tsananin sa'a da zai iya shiga cikin kogon dutse na Garul-shammar kuma har ya samu nasarar ɗauko littafin KUNDIN AL'AJABI. Bisa wannan dalili ne ya sanya na yi GABA DA GABA da kai domin na canja wannan ƙaddara taka, saboda haka yanzu ina so ka miƙo min kubar Miftahul-sihir, cikin ruwan sanyi domin na yi maka kisa mafi sauƙi, ta hanyar tsinka gaɓoɓin jikinka, ba tare da ka sha wata azaba ba”; Koda jin wannan batu sai mahaifina ya bushe da dariyar ƙarfin hali, sannan daga bisani ya haɗe rai ya dubi maridin ya ce “ya kai wannan rafkanannan halitta ka yi sani cewa GWARZON DUNIYA ba ya taɓa gudu a filin fama, ballantana ya miƙa wuya ga abokin gaba, face ya yi GWAGWARMAYA domin ya yi MUTAWAR JARUMTA”. Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai maridin ya fusata ainun, jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma, idanuwanshi na fitar da wani tiririn baƙin hayaƙi. Kawai sai ya yi wuri! Ya zare waɗansu zaratan Adduna biyu a gadon bayanshi ya kaiwa mahaifina wani bahagon sara da nufin tsinke mashi wuya, cikin baƙin zafin nama ya wurƙila ya zamewa harin, sannan ya afkawa mahaifina suka rugumtsume da azababben yaƙi mai matuƙar kwarjini, muni da ban tsoro. Duk sa’adda maridin ya kai mashi hari idan ya goce, duk abin da ya sara koda dutse ne sai kaga ya yi bindiga ya tarwatse, amma sai ya zamana cewa maridin ya ƙi yarda kubar Miftahul-sihir ta taɓa jikinshi. Sai da daƙiƙa ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin GWARAZAN JARUMAN biyu, tamkar jikkunnansu ba su kasance na jini da tsoka ba, lokacin da sa’a biyu ta shuɗe nan take sai ya zamana cewa abbana ya fara galabaita saboda ƙishi da yunwa da suka adda be shi. Koda maridin ya fahimci halin da mahaifina ya shiga sai kawai ya shammace shi ya gabza mashi naushi a fuska, saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da abbana ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya, sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim! Da rubda ciki a matuƙar galabaice yana aman jini ta baki da hanci, amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta GAGARABADAU sai ya ƙi yarda ya saki kumar Miftahul-sihir daga hannunshi”. Sa’adda jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran yazo nan a labarin ta sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta zuwa kan kuncinta. Al’amarin da ya sanya ni da Raudatul-abyad da sauran tawagarmu muka kamu da matuƙar tausayinta kenan har ƙwalla ta cika mana idanu. Daga can sai Sulaiza ta share hawayenta sannan ta ci-gaba da cewa. “Tabbas mahaifina ya sha matuƙar wahala a cikin kogon Garul-shammar kafin ya ɗauko littafin KUNDIN AL'AJABI, wanda har ta kai cewa ya rasa dukkan idanuwanshi. Bayan ya fito ne sai yaƙi ya ɓarke tsakanin sarakunan shida, da zarar wannan ya ƙwaci kundi da kuba, sai wancan ya yi mashi fin ƙarfi ya ƙwace. Koda aljani Zaruhul-Amwat da ya ɗauko mahaifina da sarakuna huɗu ya kawo su gaɓar kogon Garul-shammar ya ga halin da mahaifina ke ciki, kuma ya tabbatar da cewa zai iya rasa rayuwarshi sai tausayin shi ya kama shi, kawai sai ya ɗauke shi ya kawo shi izuwa bakin kubbarmu ya ajiye, sannan ya tashi izuwa sama yq ɓace ɓat! A cikin gajimare, Tsananin iskar fuka-fukan aljani Zaruhul-Amwat ta sanya muka yi tsammanin harin sumame aka kawo mana, sai daga bisani muka lura cewa a she mahaifina aka ajiye a daf da mu. Cikin matuƙar tashin hankali muka fito daga bukkar muka rugo izuwa gare shi, muka rungume shi, yana mai bamu labarin irin butulci da sarakunan duniya huɗu suka yi mashi. Bayan ya kammala bamu labarinne idanuwanshi suka ƙafe, jikinshi ya sandare komai ya daina motsi, alamar rai ya yi halin shi, baƙin cikin rasuwar abbana ya sanya mahaifiyata ta faɗi ƙasa matacce ko shurawa bata yi ba. Nan fa na sake fashewa da sabon matsanancin kuka ina mai kiran sunayen mahaifana, ina mai jijjiga su ina cewa, ku tashi kar ku mutu ku barni, amma babu wanda ke saurare na ballantana ya kawo min ɗauki, har da muryata ta disashe, idanuwana suka yi jajur tamkar garwashi, bayan na haƙa ƙabari na binne mahaifana, kullum sai na tsugunna a gaban ƙaburburan iyayena ina kuka gami da karanto baitocin bege a gare su. Haka rayuwata ta kasance cikin maraici da ƙunci, kullum sai ya fita farautar abin yin kalaci. Daga wannan rana na sha alwashin ɗaukar fansa akan sarakunan duniya huɗu”; Lokacin da jaruma Sulaiza ta zo nan a labarin ta sai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya daban tausayi. Nan take dukkaninmu muka ƙara kamuwa da matuƙar tausayinta, hatta aljani Jauharul-layal da bai kasance bil’adama ba sai da ƙwalla ta zubo mashi saboda matuƙar tausayin Sulaiza. Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na 10 last Free Page Domin jin wannan ƙayataccen labari. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071

👍 ❤️ 😮 4
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/19/2025, 10:25:57 AM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Wthapp Number 08137237071 Following 👉🏽 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI GWARAZAN JIYA BABI NA GOMA Lokacin da boka Matawus ya zo nan a labarin shi, sai ya ɗago kai ya dubi sarki Sabrul-marhut, nan take ya ga ƙwalla na zuba daga idanuwanshi, bakomai ne ya sanya shi hakan sai bisa mutuƙar tausayin jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran. Matawus ya yi ajiyar zuciya sannan ya ja dogon gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce “ya kai Sabrul-marhut ka yi sani cewa “mun sha matuƙar wahala sosai a domin isa fadar Sarkin bokaye, wanda dukkanin mu babu wanda bai rasa wani sashi a jikinsa ba, kuma nine kaɗai na samu nasarar fitowa daga fadar sarki bokaye a raye bayan na samu nasarar tone shirin tsafin da aka yiwa mahaifinmu na tawo da shi, domin na koma zuwa birninmu, na yi kukan baƙin ciki bisa mutuwar Raudatul-Abyad tare da jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran, bayan na samu nasarar kama hanya domin komawa zuwa gida, na ci karo da sauran ‘yan uwana in da suka yi min abin nan da masu iya magana ke cewa kura da shan bugu gardi da ƙawace kuɗi, suka yaudare ta hanyar bayyana min nadamar su akan ƙiyayyar da suke yi min, tare da alƙawarin cewa za su goya min baya na haye bisa karagar mulki, amma sai suka soka min takobi a gadon bayana suka jefar da ni ƙasa a tunanin su na mutu. Mahaifinka Maigirma Marhut shine ya ɗauke ni a wannan hali a lokacin da ya fitowa farautar ƙarshen shekara da ya saba yi, ya ceto rauwata, ya yi jinyar raunin dake jikina har na warke sumul, har na samu nasarar komawa izuwa birninmu, amma abin mamaki koda na isa sai na tarar dukkanin ‘yan uwana sun rasa rayukansu, domin ashe yaƙi ya kaure a tsakanin su domin hawa karagar mulki, amma abin da ya bani farin ciki shine mahaifinmu ya samu lafiya, kowa ya yi farin ciki da dawowa ta bayan an cire rai cewa bana raye, ‘yan majalisar sarki suka sake naɗani sabon sarkin Romaniya. Ya kai Sabrul-marhut ka yi sani cewa wannan abun alheri da mahaifinka ya yi min ban manta da shi, dare da rana ina binciken hanyar da zan saka masa da abin da ya yi min sai a halin yanzu. Ya kai Sabrul-marhut ina so ka kwantar da hankalinka, ka sani cewa za ka samu magaji da zai zamo halifanka, sai dai ina so ka saurari jawabin da zan yi maka, a halin yanzu uwar gidanka na ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni takwas, ba tare da ita kanta ta sani ba, ni ne wanda ya ɓoye junan biyun ta hanyar shiri domin kawar da idanu da bakin maƙiya daga sharrin matarka, junan biyun ba zai bayyana gare ta ba sai a daren da naƙuda zata kama ta, ina so da zarar ta haife abin da ke cikinta ka ɗauke sa ka sanya sa a cikin akwatin baƙin ƙarfe tare da TAKOBIN SARAUTA daka gada a wajen mahaifinka. Ka ɗora su abisa kenan doki a can bayan gari ka tafi ka barsu, abin da aka haifa maka zai dawo gare ka cikin aminci a lokacin da dukkanin maƙiyanka na ɓoye da fili za su bayyana. Sai dai zan gargaɗe ka koda ita matarka kar ka kuskura ka sanar da ita wannan sirri, ballantana waninta”. Sa’adda boka Matawus ya zo dai-dai nan a zancen sa sai sarki Sabrul-marhut ya cika da ɗumbin al’ajabi gami da farin ciki, bai sa’adda ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Matawus ba. Koda ya tashi tsaye ya buɗe ba ki da nufin ya ce wani abu, sai ya ga boka Matawus ya zama wani koren haske ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Take dukkan dakaru da barorin gidan sarautar da suka kamu da barci suka wartsake. Nan fa sarki Sabrul-marhut ya sake cika da matuƙar mamaki, yana ta juya wannan hikaya da umarni da boka Matawus ya yi masa, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya wanzu yana kai komo a cikin turakarsa, a haka har a alfijir ya keto. Kamar yadda boka Matawus ya labartawa sarki Sabrul-marhut haka al’amarin ya kasance. Kwanaki na bin kwanaki mako bayan mako, wata ranar asabar lokacin sulusainin dare naƙuda ta kama uwar gidan sarki wato gimbiya Nadirat, al’amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin Nadirat kenan, ta yi zaton ko cutar ajali ce ta zo mata, domin ta san bata ɗauke da wani abu da nuna cewa tana ɗauke da juna biyu, a wannan lokaci dukkanin kudancin dake turakar a ɗimauce suke, tamkar a ce ƙyat! Su cika wandon su da iska. Kwatsam! Sai sarki Sabrul-marhut ya kunno kai cikin turakar, cikin matuƙar tashin hankali ya durfafi inda take, lokacin da kuyangin suka ja da baya suka zube ƙasa gami da kwasar gaisuwa. Sarki ya daf da ita bisa ƙasaitaccen gadon sarautar, sannan ya sanya hannunsa ɗaya a tallabo kanta, ɗayan hannun kuma yana shafa gashin kanta, cikin lallausar murya sai ɗauke raɗaɗin ciwo ga masoya ya ce “kwantar da hankalinka ya abar bege na dare da rana, kuma uwar ‘ya’yana ki yi sani cewa a halin yanzu za ki haife abin da ke cikinki, wanda ke kan ki ba ku san cewa kina ɗauke da shi ba, boka Matawus ya bayyana min cewa ya ɓoye wannan juna biyu na ki ne domin kawar da idanun maƙiya. Mu haɗu a book 2 na kuɗi ne domin jin cigaban wannan kayataccen littafi. Za a biya kuɗin littafin ta wannan hanyar ₦400 Account Number: 0084279025 Account Name: USMAN UMAR MANSUR Bank: Access Bank Nigeria Sai a tura shaidar biya ta wannan number 08137237071 Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi 08137237071

❤️ 👍 🙏 5
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/11/2025, 1:37:22 PM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Shekarar Rubutu 10-02-2024 Website:- www.Arewanovels.com.ng Wthapp Number 08137237071 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI GWARAZAN JIYA BABI NA UKU Kimanin shekaru ɗari biyu da ɗoriya a birnin Romaniya mahaifinmu sarki Raziban shi ne ke riƙe da Sarautar birnin, Sarki Raziban yakasance gwarzon mayaƙi kuma JARUMIN JARUMAI gawutaccen matsafi wanda masu bincike da hasashe suka tabbatar da cewa a ƘARSHEN ƘARNI na uku bayan shuɗewar boka Shuyuɗan mai taskar ANNOBA DARI ba a samu wanda ya kai mahaifinmu ƙarfin sihirin tsafi, Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan nahiyar ke yi masa mubaya'a bisa dole, Wasu ma na kiran mahaifinmu da Amirul-Sihir ma'ana Sarkin bokaye. Duk da irin ƙasaitar mulki da mahaifin mu ke da shi amma giyar mulki ba ta ja shi ba yakasance mutum adali ma'abocin tausayi da afuwa, Mahaifinmu ya na da 'ya'ya guda bakwai, Yarima Zafiyar shi ne babba dai gimbiya Rumailat, Yarima Hasanul-Mausur, Sumaiyat, Laswil, Rukaisu, Zaidar sannan kuma ni Matawus na cikon bakwai ɗin su. Kowannen mu na samun kulawa daga soyayyar mahaifinmu, duk da irin matsananciyar gaba da ƙiyayyar da ke tsakanin mu wacce ba kowa ba ne ya haddasa hakan ba face bakin kishin da ke tsakanin iyayen mu mata. Wata rana mahaifin mu na zaune a fadarshi bisa karagar mulki, fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da ma abin da idanu ba su taɓa gani, Fadar ta cika maƙil duk inda mutum ya kalla babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke. 'Yan majalissar sarki na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma A kowa ce kusurwa a fadar dakaru ne na jinsin MUTUM DA ALJAN shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar gwarjini da ban tsoro ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro. A wannan lokaci idan ka ɗauke iskar da ke kaɗawa a fadar babu abin da kunne ke ji face sautin fitar numfashin ɗaruruwan jama'ar fadar. A na cikin wannan hali ne kwatsam sai a ka ga sarki ya faɗo daga kan karagar mulki yana amai na jini kuma tari mai tsanani ya turnuƙe shi, Cikin kaɗuwa gaba ɗaya 'yan majalissa suka yi ca akan mahaifina, da hanzari dakaru suka shigo fadar ɗauke da wani ƙayataccen gado suka ɗauki sarki suka fice da shi kai tsaye suka kai shi turakar shi suka shimfiɗe shi bisa gadon sarauta suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar shi. A can gidan sarauta kuwa labarin abin da ya faru da sarki ya riske mu don haka ni da 'yan uwana sai muka ɗunguma muka nufi turakar shi hankulan mu a tashe, Ya yin da muka iso ne sai dakarun da ke tsaron ƙofa suka dakatar da mu cewa sarki ya ce kada a kyale kowa ya shiga har sai ya yi umarni. Ko da jin wannan batu daga bakin dakarun sai yarima Zafiyar ya fusata ainun ya daka masu tsawa ya dube su ya ce "Shin mene ne matsayin ku da har zaku hana mu ganawa da abbanmu ina so ku gaggauta buɗe mana ƙofar tun kafin KAIFIN TAKOBI na ya tsara ruhikan ku". Da jin hakan daga bakin yarima sai hankalin dakarun ya dugunzuma ainun, daƙyar aka samu wani mai dakakkiyar zuciya ya buɗi baki da nufin ya furta wani abu, kawai sai aka ji ƙarar zare sakatun dake dake kofar, jim kaɗan sai ƙofar ta buɗe sai ga boka Jauwad ibn Ramli ya bayyana a gare su. Boka Jauwad yakasance dattijo mai kimanin shekaru saba'in dogo ne kakkaura yana da gashin gemu da ƙasumba farare sol ko ɗigon baki babu, fuskarshi doguwa ce mai ɗauke da dara-daran idanu jajajur! tamkar garwashin, yana da faffaɗan hanci mai ɗauke da ƙofofi tamkar mazirari, bakinshi tafkeke ne tamkar bakin rijiya mai ɗauke da wargatsattsun haƙora marasa kyawun gani, yana sanye da baƙaƙen tufafi tare da guraye da layu na sihiri tamkar wani tsohon mahaukaci, kallo ɗaya za ka yi boka Jauwad ka tabbatar da cewa ya cika hatsabibi a fagen sarrafa alƙalumman sihiri. Duk da kasancewar mahaifinmu mashahurin matsafi da babu tamkar shi a nahiyar amma bisa al'adar masarautar mu akwai bokan da ya ke gudanar da dukkan wani sha'ani na lafiyar iyalan masarauta, da kuma jagorancin abin bauta. Ya yin da muka yi arba da boka Jauwad sai dukkanin mu muka risina gare shi muka kwashi gaisuwa cikin girmamawa, boka Jauwad ya dube mu ɗaya-bayan-ɗaya, sannan daga bisani ya buɗe tafkeken bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa wannan jinya da ta samu mai martaba cuta ce mai matuƙar haɗarin gaske, wacce za ta iya zamowa ajalin shi baki ɗaya, Ba wani abu ba ne ya haddasa mashi cutar ba face wani sihiri da abokin gabar shi boka Bazzagul-Nadiyar ya yi mashi, an binne sihirin ne a cikin wata tsohuwar rijiya dake cikin fadar sarkin bokayen aljanu na duniya, Kafin mutum ya isa inda fadar sarki bokayen take akwai haɗdura masu yawa gami da miyagun dazuka. A halin yanzu bincike ya tabbatar mani da cewa a kaf duniya yanzu babu wani waje mai tattare da haɗari tamkar shi, Daga nan zuwa can ɗin tafiyar shekaru huɗu ce amma bisa Saurayin aljani mai tashen balaga za a iya isa cikin watanni shida. Sa'adda boka Jauwad yazo nan a jawabin shi sai hankulanmu ya dugunzuma ainun, wasu daga cikin'yan uwana cikinsu ya ɗuru ruwa, saboda fargabar kada sarki ya rasa rayuwar shi a halin yanzu ba tare da ya sanar da su mabuɗin taskar dukiya ba. Boka Jauwad ya katse shirun da ya wanzu tsakanin su ta hanyar buɗe baki a karo na biyu ya ce " Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa a halin yanzu babu abin da ya ke gaban ku face shiga duniya domin ku isa fadar sarkin bokaye ku karya sihirin da aka yi wa sarki, Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan har kuka yi jinkiri sarki ya rasa rayuwar shi tamkar kun rushe birnin ku da hannayenku ne, domin abokin gabar abban ku boka Bazzagul-Nadiyar zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA na wannan birni, kun ga kenan shi ne zai gaji KARAGAR MULKI ta mahaifin ku. Jawabi na ƙarshe a gare ku shi ne mai martaba sarki ya ce na faɗa maku cewa dukkanin wanda ya samu nasarar tone sihirin da aka yi masa shi ne zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA. Ko da boka Jauwad yazo nan a zancen shi sai ya rikiɗa zuwa wani baƙin hayaƙi ya ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Jiki a sanyaye ni da sauran 'yan uwana kuma juya muka fice daga harabar turakar mai martaba. Kamar yadda boka Jauwad ya faɗa haka al'amarin yakasance bayan kwanaki biyu da kwanciyar mai martaba jinyar rashin lafiya sai dukkan 'ya'yan tare da ni mu ka hallara a fada domin gudanar da tafiya karya sihirin tsafin da aka yiwa mahaifinmu, lokacin da mu ka shigo fadar sai mu ka tarar ta cika maƙil da jama'ar gari tare da 'yan majalissar sarki a gefe guda boka Jauwad ne tare da magajin gari mai suna Shuraih wanda yakasance ɗan uwa a wajen sarki uwa ɗaya uba ɗaya, bisa dokar masarautar duk sa'adda sarki ya kwanta jinya ko kuma wani uzuri ya same shi sai a damƙa sarauta ga magajin gari, A iya sanin da nayi wa magajin gari shuraih nasan babu wata matsala tsakanin shi da sarki don haka koda wannan jinya ta sarki ta faru ban zarge shi da wani abu ba, Bayan kowa ya hallara a fadar kuma an samu nutsuwa sai sarki Jauwad ya miƙe tsaye daga kan kujerarshi ya fuskanci al'umma ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku jama'ar wannan faɗa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne 'ya'yan mai martaba sarkinmu za su tafi izuwa fadar sarkin bokayen duniya domin su tone sihirin tsafin da aka yiwa sarki wanda abokin gabar shi kuma maƙiyin wannan ƙasa tamu ya yi mashi wato sarki Bazzagul-Nadiyar. Bisa Wasiyyar da sarki ya bayar cewa dukkanin wanda ya tone wannan sihirin tsafi ya zo da shi nan shi ne zai gaji karagar shi ya mulki. Sa'adda boka Jauwad yazo nan azancen shi sai fadar ta kaure da cece kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi, tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani Jauwad ya ɗaga hannunshi sama fadar ta yi tsit a karo na biyu sannan ya cigaba da cewa "Yanzu dukkan wani abu na guzuri da abin hawa an tanadar masu abin da ya rage yanzu shi ne za a ɗora Magajin gari a bisa KARAGAR MULKI, sannan bayan 'ya'yan mai martaba sun yi bankwana da mahaifinsu mata za'a yi masu rakiya izuwa bakin ƙofar gari. Lokacin da boka Jauwad yazo nan azancen shi sai wani badakare ya matso daf da shi ɗauke da wata akwatun baƙin ƙarfe ya ajiye a gaban shi ya buɗe ta ya ɗauko wani kambun Sarauta ya miƙa mashi shi kuma ya ɗora kambun a bisa kan magajin gari da ke zaune a daf dashi a kan kujerarshi, badakaren ya sake zira hannunshi a cikin akwatun ya ɗauko wata sharbebiyar takobi a cikin kubenta ya risina cikin ladabi ya miƙa wa Boka Jauwad shi kuma sai ya damƙa a hannun magajin gari, Sannan shuraih ya miƙe tsaye ya je ya zauna a bisa KARAGAR MULKI take jama'ar dake fadar suka risina da kawunansu a gare shi dake nuna mubaya'a a gare shi. Koda kammala bada riƙon sarauta sai ni da 'yan uwana muka shiga zuwa gidan sarauta domin yin bankwana da mahaifanmu kamar yadda boka Jauwad ya tsara, Lokacin da na Kaɗaita da mahaifiyata a cikin turakarta sai na dube ta cikin alamun matuƙar damuwa na ce "Ya ummina na ji a jikina cewa wannan gasa da aka sanya mana ita babu tabbacin zan yi nasara domin duk abin da zai kai ga a samu nasarar 'yan uwa sun ɗara ni wato jarumtaka da ƙarfin sihiri". Koda jin wannan batu daga bakina sai murmushi mai taushi ya suɓucewa mahaifiyata al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan na dube ta nace "Ya ummina shin ina dalilin wannan murmushi na ki?. Dajin wannan tambaya sai mahaifiyata ta yi buɗe baki ta ƙura mani idanu ko kiftawa bata yi ta fara magana a karo na farko "Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa haƙiƙa bani da wani buri da huce naga cewa kai ne ka gaji sarki ba 'yan uwanka ba, kuma dukkan maganar da ka faɗa tana kan gaskiya, Abin da ya sanya ni murmushi kuwa shi ne kana tare da abin da yafi na 'yan uwanka kuma matsawar ka yi riƙo da shi zai zaka samu nasarar cinye wannan gasa", Cikin matuƙar mamaki na dubi ummina na ce "Ya ummina shin ina dalilin wannan furuci na ki kuma wane abubuwa ne nake d su wanda idan na riƙe su zan samu nasara?, Ummina ta ce "Ya ɗana ka yi sani cewa tun da na mahaife ka na tabbatar da cewa na haifi yaro nagari kuma mai nasara a rayuwa, tun kana yaro ƙarami na fahimci halayen ka masu kyaune saɓanin 'yan uwanka, Ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya komai kake taƙama da shi akwai wanda ya huce ka domin masu iya magana na cewa "Kamai sammakon ka wani a hanya ya kwana" Wato idan jarumta, sihirin tsafi ko ƙarfin mulki kake taƙama da su cewa sune zasu bada nasara a cikin 'yan uwanka akwai waɗanda suka shafe ka, Abin da kake da shi wanda 'yan uwanka basu da shi da idan ka rike su zaka samu nasara su ne kamar haka, Gaskiya, Tausayi, Amana da hakuri waɗannan sune halaye mafi daraja da dukkan wanda ya riƙe su zai cimma nasara a rayuwar shi kuma babu wani abu da zai sanya a gaban shi face ya samu nasara, Gaskiya dai zata ƙara maka daraja da ɗaukaka a cikin dukkanin harkokin rayuwa kuma ita ce ke bayyanawa jama'a darajar da mutumtakar ɗan Adam, Tausayi kuwa na sanya soyayyarka a cikin zukatan al'umma har da maƙiyan ka, Amana kuwa na ƙara wa maka ƙima da daraja a cikin kowacce irin al'umma ka shiga,Hakuri kuwa zai sanya ka cimma nasara a dukkan abin da ka sanya a gaba, domin duk kyawun abu idan baka yi hakuri ka cimma karshen shi ba to abu biyu zai faru, Da farko shi ne zaka rasa wannan abun, sannan ka yi asarar lokaci da lafiyar da ka ɓata a kan shi, Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa waɗannan halaye sune sinadaran shaharar duk wani tauraro a duniya, Na so a celokaci bai kure ba da baka tsakure daga hikayar jarumi Masnur ibn Abdullah da wani fasihin marubucin hikayoyin wannan ƙarni wato Sufi ya tattara kuma ya sanya littafin suna KUNDIN HIKAYA, Tabbas da zaka ƙara tabbatar da batu na kuma ka ƙara ƙanƙame halayen da kyau". Lokacin da na ji wannan dogon jawabi daga bakin ummina sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ban sa'adda na rungume ta ba ina mai cewa haƙiƙa na aminta da ke ummina ɗari-bisa-ɗari, da yardar abin bauta ba zan ketare wannan wasiyya ta ki ba, kuma zan samu nasara bisa abin da na fita nema fatana na dawo na same ki cikin ƙoshin Lafiya". Sa'adda da na zo nan azance na sai mu duka biyun muka fashe da kukan farin ciki, dakyar da siɗin goshi muka rabu da juna suna masu zubar da hawayen baƙin ciki na shaƙuwa da juna. Lokacin da na isa fada sai na tarar dukkan 'yan uwana sun hallara ni kaɗai ake jira domin haka ina isowa sai aka ɗunguma izuwa wajen fada muka kama dawakai muka haye dake dauke da abin guzuri, kai tsaye boka Jauwad tare da magajin gari Shuraih haɗe da sauran mutanen gari suka yi mana rakiya har zuwa bakin iyakar gari suna masu yi mana fatan samun nasara, Lokacin da muka nausa zuwa cikin daji sai muka cigaba da tsala gudu a bisa dawakai sai da muka shafe tsawon sa'a ɗaya muna tafiya babu sassauci lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta cika a dai-dai wannan lokaci ne mu ka iso wata mararraba a dajin da ta kasu gida huɗu, Sai yarima Zafiyar ya durfafi hanyar yamma, Laswil kudu, Rumailat arewa sai ni kuma na yi gabas, dukkan 'yan suna kallon juna cikin matuƙar ƙiyayya amma ni sai na dunga sakar masu tattausan murmushi a haka har mu ka ɓacewa juna da gani. Lokacin da cigaba da tafiya a cikin dajin sai na wanzu ina tsala azababban gudu a bisa dokina ta hanyar ratsa duwatsu, ƙoramu, bishiyu da sarƙakiya, Sai da na shafe tsawon sa'a biyar ina wannan tafiya a dai-dai lokacin ne na fahimci cewa dokina ƙarfin gudun shi ya ƙaru ainun domin haka sai na ja linzamin shi na tsaya cak! na sauka ƙasa na zauna a ƙarƙashin wata itaciya na fito da abin guzuri na domin na yi kalaci shi kuma dokina ya shiga yin kiwo yana cin ciyayin da ke dajin, Ina cikin yin kalacin ne kwatsam bazato babu tsammani sai na ji kwantsama wata tsawa gami walƙiya cikin ƙankanin lokaci sararin samaniya ta canza launi izuwa baƙi, Cikin wani irin baƙin zafin nama na miƙe tsaye zumbur gami da mayar da abin kalacin izuwa cikin jakar guzuri na gami da zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayana, Kwatsam sai na ga dokina ya faɗi ƙasa ƙasa yana shure-shuren mutuwa, Cikin kaɗuwa na ruga zuwa inda ya ke kafin na isa har rai ya yi halin shi, cikin matuƙar takaici na tsugunna a gaban shi cikin alhini a lokacin ne na lura cewa wani irin baƙin ruwa mai yauƙi na fitowa daga bakin shi, koda na shin-shina ruwan sai na ji alamun akwai guba a cikin shi hakan ya sanya na fahimci cewa tabbas ciyawar da ke dajin ita ce ke ɗauke da wannan guba, Cikin matuƙar fushi na miƙe tsaye zumbur gami da kwarara wawan ihu, faruwar hakan ke da wuya sai duhun da ke sararin samaniya ya washe tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Kwatsam! sai wani ƙaton kai mai ɗauke da kawo biyu da fala-falan kunnuwa irin na Zomo haɗi baki irin na jemage ya faɗo tim, sannan hannaye, kafafuwa, gangar jiki suka biyo baya, ko da ganin hakan sai na ƙara riƙon takobina ina zuba idanun, Sannu a hankali sai sassan jikin suka dunga haɗuwa da 'yan uwan su har sai da halittar surar ta kammala, kafin na ƙarewa surar kallo wani sulken yaƙi da makamai sun bayyana a gare ta, A lokacin ne na fahimci cewa tabbas surar aljani ne ba bil'adama ba saboda waɗansu fuka-fukai da suka bayyana a gwiɓin hammatarsa guda biyu, Tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin halitta mai kwarjini da ban tsoro tamkar halittar ba domin haka sai yanayin tsoro ya kama ni har gumi ya fara tsattsafo mani a fuska amma saboda ƙi faɗi Irin ta 'ya'yan sarakai sai na basar. Ko da aljanin ya lura da hakan sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, Sai da ya yi dariyar ta ishe shi sannan ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da Saƙon mutuwa, Kawai sai ya zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje ya yi ɗauki izuwa Kai na yana ihu da kururuwa mai firgitarwa, Ko da ganin hakan sai nima na ruga gare shi domin tarar juna muna haɗuwa muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, Muka wanzu muna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA masu juriya a filin fama, Idan ka ɗauke sautin kaɗawar iskar dake sanya rassan bishiyu rangaji babu abin da kunne ke ji face ƙarar karafniyar makaman yaƙin mu da ke haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara mara daɗin saurare, Sai da muka shafe tsawon rabin sa'a muna wannan baƙin artabu babu sassauci a lokacin ne na fahimci cewa tabbas na gamu da gamo na, Domin ƙarfin saran aljanin ya nunka nawa sau uku, A wasu lokutan idan ya kawo mani hari idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa sannan na taso sama na mayar da martani, A cikin wannan artabu ne aljanin ya kawo mani wani nagartaccen sara da nufin ya tsinke mani wuya, cikin zafin nama na sunkuya makaminshi ya sari iska, Kafin ya sake wani yunƙuri ya sake kawo mani wani harin a kwaɓin cinyata ta hagu duk ƙoƙarin da nayi domin naga na kaure amma sai da makamin ya yanke ni a cinya jini ya yi tsartuwa na kurma ihu sakamakon raɗaɗi da zugin da na ji. Kafin cikar daƙiƙa ashirin ya samu nasarar yi mani raunuka biyar ɗaya a cinya biyu a kafaɗata ta dama sauran biyun a damtsen hannuna na hagu kowanne rauni na zubar da jini, Nan fa wani irin zazzaɓi mai matuƙar zafi ya kama ni, jiri ya fara ɗiba ta ina faɗuwa ƙasa, amma saboda da JURIYA DA JARUMTA irin ta MAZAN JIYA sai na miƙe tsaye a haka na ci gaba da kare kaina ba tare da mayar da martani ba. Lokacin da rabin sa'a da daƙiƙa ɗari biyu da hamsin ta shuɗe ana wannan artabu kwatsam! Bazato babu tsammani sai na wata hikima ta faɗo mani a rai, koda jin hakan sai na yi wuf na dunƙule hannuna ya kirɓawa aljanin naushi a kwiɓin hammatarshi saboda ƙarfin naushin sai da ƙashin hannun ya karye ya yi ƙara ruƙus! Aljanin ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji. Koda na fahimci cewa ashe sam makami ba ya tasiri akan shi nan take na yi jifa da takobina na shiga kai mashi bugu da naushi hannu da ƙafa. Wohoho haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canja, nan fa yazamana cewa cikin ƙanƙanin lokaci na yi mashi jini-jina baya iya mayar da martani, kawai sai na yi wuf na kama wuyan shi na murɗe da ƙarfin tsiya, nan take na jefar da gawarshi gefe guda ko shurawa bai yi ba. Koda samun wannan gagarumar nasara sai na cika da matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa na ɗauki takobina na ci-gaba da tafiya ina takawa daƙyar bisa ƙafafuna na durfafi wata hanya, tafiyar daƙiƙa ɗari kacal nayi na iso wata ƙorama da ruwan cikinta yakasance garai-garai gwanin ban sha'awa, cikin matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa ya sanya hannayena biyu ina kamfatar ruwan ciki ina sha. Sannan na miƙe tsaye na durfafi wata bishiyar tuffa na tsinka na ci na ƙoshi. A sannanne na ji ƙarfin jikina ya dawo kuma sanyi da zazzaɓin da nake ji sun rabu da ni. Nan take na ci gaba da tafiya ina sake kunna kai izuwa cikin dajin ina tafiya cikin hanzari. Tsawon kwanaki uku na shafe ina tafiya a ranar kwana na ukun ne na iso izuwa gabar wani ƙaramin tsibiri mai ɗauke da bukka guda ɗaya jal, a gaɓar tsibirin wani makeken kogi ne mai tsawon gaske da ba a iya hango ƙarshen shi. Nan take na fahimci cewa ba zai yiwu na iya ƙetare wannan kogi ba face na ha samu kwale-kwale, don haka sai na isa izuwa bakin wannan bukka na yi gyaran murya har sau uku. Jim kaɗan sai ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wani dattijo dogo mai matsakaicin kaurin jiki ma'abocin kamala da haiba sanye da jajayen tufafi a hannun shi yana dogare da wani kwagiri. Sannu a hankali ya tako da ƙafafuwanshi har yazamana ya iso daf da ni ya ƙura min idanu. Fuska ta cike da annuri na dube shi na yi gyaran murya na ce "ya kai wannan dattijo ma'abocin kamala ni matafiya ne hanya ta biyo da ni domin nemo wani abu mai matuƙar alfanu gare ni, ina so ka taimake ni da jirgin ruwan da zan iya ƙetare wannan kogi, kasancewar na rasa abin hawa na? Koda jin wannan tambaya sai dattijon ya buɗi baki ya yi gyaran murya cikin kakkausar murya ya ce "ya kai

👍 ❤️ 5
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/12/2025, 8:55:17 PM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Shekarar Rubutu 10-02-2024 Wthapp Number 08137237071 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI GWARAZAN JIYA Babi na huɗu Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan mun kammala kalaci sai muka yi ɗauki kayan aiki muka nufi gona tare da Raudatul-Abyad, yau ma kamar kullum fuskarta rufe take da rawani kuma tana sanye da baƙaƙen tufafi a gadon bayanta tana ɗauke da wata zabgegiyar takobi, shigar da ta yi matuƙar yi mata kyawu. Tafe muke cikin hanzari ta gaba ina biye da ita a baya, tsawon daƙiƙa ɗari biyu muna cikin wannan hali babu wanda yace ƙala. Sannu a hankali har muka iso wata makekiyar gona mai ɗauke da alkama mai tsawon hetta goma. Koda muka iso ɗin sai Raudatul-Abyad ta miƙa min fartanyar dake hannunta gami da lauje na karɓa sannan ta yi min nuni da na fara aiki batare da buɗi baki ta ce min uffan ba, kawai sai ta durfafi gindin wata itaciya ta kwanta bisa wata tabarmar kaba mai haɗe da matashi, kawai sai na duƙufa na fara aiki, wasa-wasa sai ga shi na shafe tsawon sa'a ɗaya a cikin wannan yanayi, koda na ɗaga kaina na duba aikin da na yi sai naga ashe bai huce kunya goma ba, a wannan lokaci hasken rana ta fito ta fara zafi ainun. Al'amarin da ya sanya kishi ya fara damuna, kuma gadon bayana ya fara ciwo. Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ina cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai na ga waɗansu masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, cikin wani irin zafin nama na dinga zillewa kibbau ɗin tare da falfalwa da azababban gudu izuwa inda Raudatul-Abyad ke kishingiɗe domin na bata kariya, a wannan lokaci barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, koda ya rage saura taku biyar na isa daf da ita kwatsam ba zato babu tsammani sai waɗansu irin samudawan dakaru suka yi fitar burgu daga duhuwar dajin, Dakarun suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, fuskokinsu a rufe suke da hulunan ƙarfe, a hannayensu suna ɗauke da miyagun makamai dangin Gatari, sungumi, majaujawa, al'amudi da sauran su. Adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya, kafin nayi wani yunƙuri sun yi min ƙawanya suna muzurai tamkar za su ci babu. Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakaninmu sai na lura wani badakare ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad. Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo, daga can sai wani narkeken ƙato ya fito daga cikin su, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa shine shugabansu saboda hular kwanon da ke kanshi da takobinshi da ta kasance ta musamman, Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi har iya isa daf! Da inda Raudatul-Abyad take ta yadda suna jin numfashin juna. Kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba, daga bisani kuma sai ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da SAƘON MUTUWA, sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya dubi Raudatul-Abyad ya ce "ya ke Raudatul-Abyad 'ya ga tsoho Abu-Raudat kiyi sani cewa dama na faɗa miki in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana za su haɗu, kuma rabon kwaɗo baya hawa sama koda ya hau zai sakko. Yau ga shi kin faɗa tarkona wanda ya za ki iya tserewa ba, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan kashe wannan baƙo naki a gaban idanuwanki sannan na tafi dake a matsayin sabuwar amaryata…". Kafin narkeken ƙaton ya gama rufe bakinshi ya gama rufe bakinshi Raudatul-Abyad ta tari numfashin shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "Dawazul-kiryan kayi sani cewa haƙiƙa ka tafka babban kuskure da rafkananniyar zuciyarka ta yaudare ka cewa za ka ci galaba a kaina, ka sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA ba za su taɓa zamtowa abu guda ba, ni MURUCIN KAN DUTSE ce ban fito ba sai da na shirya. Kuma ni ƙadangaren bakin tulu ce.. Shawarar da zan baka ita ce ka gaggauta miƙa wuya gare ni wata ƙila ka samu tsira da ruhinka"; Dawazul-kiryan ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya ce "haƙiƙa ƙi faɗin ki tana matuƙar burgeni domin masu iya magana na cewa wai matsoraci baya zama gwani. Amma kar ki manta cewa alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, kuma koda ba a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza. Kuma dai SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI. "Haƙiƙa ka makara wajen cimma wannan burina naka, amma ko ba komai an ce ba a ƙwacewa yaro garma. Kuma inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa" Raudatul-Abyad ce ta yi wannan furuci cikin matuƙar fushi. Dawazul-kiryan ya ce "ai zuwa a makare yafi zuwa a makara, kuma duk mai nema yana tare da samu". Koda gama faɗin hakan sai yaran Dawazul-kiryan suka yi wuf suka zare makaman su suka yi ihu da kururuwa sannan suka yi ɗauki izuwa kaina. Yayin da naga hakan sai na zare takobina ya ruga gare su domin tarar juna, Lokacin da aka haɗu sai a kayi KARON MAZA, aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, ana fara wannan artabu ne na fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba. Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje ta cika dodon kunne, duk sa'adda na kaiwa dakarun hari sai ka ga sun kare tare da mayar da martani, in da ba don ina da matuƙar zafin nama ba da tuni sun murƙushe ni saboda yadda suka yi min rubdugu tamkar yadda dandazon ƙudade ke yanyame ƙwallon mangwaro. Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi kuma na fahimci cewa idan aka cigaba da wannan artabu a haka wankin hula zai kai ni dare kuma dakarun za su samu nasarar kashe Raudatul-Abyad. Koda na zo nan a tunani na sai na fusata ainun na sake dage damtse ina kai sara da suka cikin matuƙar zafin nama, gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canja dole rawa ma ta canja, faruwar hakan ke da wuya sai na fara samun galaba akan dakarun, yazamana cewa duk inda na sanya a gaba sai dai kaga fili fetal dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga. Al'amarin da ya fusata sauran mayaƙan kenan suka sake yin ɗauki izuwa kaina, kafin shuɗewar daƙiƙa ɗari kacal na kashe fiye da rabin dakarun. Nan fa JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda. Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan artabu na zubar da dukkan mayaƙan a ƙasa hatta badakaren da ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad, illa shugaba Dawazul-kiryan ne kaɗai a tsaye fuskarshi a murtuke tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakani na da Dawazul-kiryan na wani lokaci daga can sai ya dube ni cikin kakkausar murya mai tattare da fushi ya ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin taurin kai da shisshigi kayi sani cewa zaki koda ya mutu gawarshi abar tsoro ce, KARO DA GOMA kalacen safe in ji masu iya magana, kuma masu iya magana na cewa kaɗe mage ba yanka wa ba ne. Saboda haka idan ka miƙa kan ka izuwa gare ni, zan yi maka kisa mafi sauƙi ta hanyar datse gaɓoɓin jikinka ɗaya-bayan-ɗaya ba tare da kasha wahala ba. Idan kuwa ka ƙi to zaka gwammace wa aya zaƙin ta"; Kafin ya gama rufe bakinshi na tari numfashin shi ina mai daka mishi tsawa na ce "ya kai wannan tsohon AZZALUMI kar ka manta cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Kuma shi zalunci baya ɗorewa a doron ƙasa, don haka sai ka shirya ga maza nan bisa kan ka. Koda gama faɗin sai na ɗaga takobina na durfafi inda yake tsaye ina kururuwa koda ganin hakan sai Dawazul-kiryan ya yi wuf ya zare wani zabgegen gatari a gadon bayanshi ya yi ɗauki kaina, muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. Koda fara wannan artabu sai Raudatul-Abyad ta koma gefe guda ta harɗe hannaye tana kallon yadda gumurzun ke wakana. Nan fa muka wanzu muna kai wa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta GWARAZAN JIYA. kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce artabun gwani da gwani daɗin kallo gare shi, kuma idan BABBAR GIWA ta fito filin fama babu wanda yake yin fito-na-fito da ita face GWARZON ƘARNI. Kuma masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne ma fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Ga wanda ke kallon yadda gumurzun ke wakana zai fahimci cewa Dawazul-kiryan ya nunka ni a ƘARFIN DAMTSE sau uku. Domin kuwa duk ya kai min hari da gatarinshi idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci na fara galabaita ya zamto ba na iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kaina, ana cikin wannan hali ne Dawazul-kiryan ya shammace ni ya makamin ƙotar gatarinshi a akaina saboda ƙarfin dukan sai dai kan ya tsage jini ya yi tsartuwa, saboda matuƙar zugi da raɗaɗi ban san sa'adda na kurma ihu ba na yi taga-taga zan faɗi amma sai na turje, sai dai kash! Kafin na dawo cikin hayyacina ya sake samun nasarar makamin a wuya. Nan take na sulale ƙasa magashiyan ina nishin wahala. Koda samun wannan gagarumar nasara sai Dawazul-kiryan ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska ya dube ni ya ce "ai da ma na faɗa maka a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe" kuma komai tsananin duhun dare gari zai waye". Yanzu ga shi kana kusa da baƙuntar barzahu za ka yi mutuwar wulaƙanci, alfarma ɗaya zan yi maka ita ce ka rubuta wasiyyarka kafin na zare maka ruhi daga gangar jiki". Duk wannan abu dake wakana sai Raudatul-Abyad na tsaye a gefe guda tana kallo. Dawazul-kiryan na gama faɗin hakan sai ya durfafi inda nake kwance ya raba ƙafafuwanshi biyu a kaina yana mai yi min murmushim mugunta, kawai sai ya ɗaga gatarinshi domin ya datse min wuya, kawai sai wata hikima ta faɗo min na damƙi ƙasa a hannuna na watsa mashi a fuska. Kafin ya wartsake na miƙe tsaye zumbur na sanya takobina na sare mashi wuya take kan yi fitar burgu jini ya yi feshi gami da tsartuwa gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica!. Nan take na faɗi ƙasa bisa gwiwoyina cikin matuƙar galabaita. Cikin matuƙar kaɗuwa Raudatul-Abyad ta rugawa izuwa inda nake ta rungume a ƙirjinta tana mai fashe da kuka mai tsuma zuciya duk da kasancewar ina cikin mawuyacin hali sai da naji sanyi a raina gami da farin ciki. Bisa jin Raudatul-Abyad a daf da ni. Sannan daga bisani ta janye jikinta daga gare ni muka fuskanci juna cikin alamun matuƙar tausayi ta dube ni kana ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai ɗan-karen daɗi tamkar alagita ta ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin sadaukantaka haƙiƙa na yaba da sadaukantakar ka kuma ma yarda cewa kai mai amana ne, kai ne irin namijin da ya dace ya zamto abokin rayuwata. Ina mai matuƙar farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara. Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Daga wannan furuci ne kuma ta shiga bani kulawa inda ta tashi tafaɗuna muka isa ƙarƙashin itaciya ta zaunar da ni sannan ya ɗauko salkar ruwa ta buɗe murfin ta ta sanya hannunta ta tallafo wuyana ta kafa min a baki na shiga kwankwaɗar ruwan har na ƙoshi, kana ta buɗe wata jakar fata dake sanye a kwiɓin cinyarta ta buɗe ta ɗauko wani gashasshen naman barewa ta shiga bani a baki ina ci cikin matuƙar tsantsar soyayya da tausaya wa. A iya tsawon rayuwata ban taɓa sanin cewa haka so yake da daɗi ba. Haƙiƙa so shine sinadari mafi girma dake sanya zuciya da ƙarfafa garkuwar jikin ɗan Adam. So shi ne linzami da yafi ƙugiya ƙarfi wajen sarrafa bil'adama a doron ƙasa. Haƙiƙa so kan sauya duniyarmu daga kowanne ƘARSHEN KARNI izuwa SABON ƘARNI mai cike da abubuwan ban mamaki. Tabbas so shine ni'ima mafi daraja a cikin dukkanin wata al'umma. A wannan rana haka muka kasance tare da Raudatul-Abyad tana ba ni kulawa mai cike da tsantsar bege da soyayya. Sai da la'asar sakaliya sannan muka nufi komawa izuwa gida, da yake a wahale nake sai ya zamana daƙyar nake iya takawa domin haka kafin mu isa gida duhun dare ya kawo kai. lokacin da muka samu nutsuwa sai Raudatul-Abyad ta kwashe dukkan labarin abin da ya faru da damu ta zayyanawa mahaifinta Abu-Raudat daga farko har ƙarshe. Koda jin wannan labari sai farin ciki ya turnuƙe shi bai san sa'adda murmushi mai taushi ya suɓuce mashi ba ya dube ni cikin murya mai tattare da dattijantaka ya ce "ya kai Matawus kayi sani cewa kai ne matashi na arba'in da biyar da suka zo gare ni domin na bayyana masu hanyar da za su haye tekun dake gaɓar mu domin su isa izuwa fadar Sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar. Babu wani mahaluki ɗaya a cikin su da ya samu nasarar cinye jarabawar da na yi masu sai kai, 'ya ta Raudat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance da babu wani ɗa namiji da zai yi tozali da ita face ya kamu da matuƙar sha'awar ta, amma gashi ka keɓance da ita ba tare da ka haike mata ba, Sannan kana da halin da za ka ƙi ceto rayuwar 'yata a lokacin da dakarun sumame suka farauce ta. Tsawon lokaci ina jiran zuwan jarumin da zan damƙawa amanar 'yata a hannun nagartaccen namiji, kuma GWARZON ƘARNI amma sai a yau na cimma burina. Kasancewar a halin yanzu shekaru na sun ja tsufa ya kamani kuma cutar da nake fama da ita a koda yaushe rai zai iya yin halin shi, domin hakan dole na miƙa ragamar abar kaunata kuma farin cikina ga wanda zai bata farin cikin rayuwa har abada. Ina mai farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara akan abin da ka fito nema". Lokacin Tsoho Abu-Raudat yazo nan a zancen shi sai ya sanya hannunshi ya ɗaga gefen shimfiɗar da yake zaune ya ɗauko wata jemammiyar fatar barewa ya miƙa min sannan ya ci gaba da cewa "wannan ita ce taswirar da zata kai ka izuwa fadar boka Bazzagul-Nadiyar da dukkan bayanan kowacce ƙofa da dokokin shiga fadar. Sannan ina mai damƙa maka amanar 'yata ka riƙe min ita cikin aminci, bana sa rai za ku dawo ku same ni a raye. Zan haɗa ku da hadimin da zai yi maku rakiya a cikin wannan tafiya har ku cimma nasara. Koda gama faɗin hakan sai Abu-Raudat ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar fita daga bukkar cikin hanzari ni da Raudat muka rufa mashi baya. Ya yin da muka fito ne sai Abu-Raudat ya buɗe bakinshi yana mai karanto waɗansu ɗalasimai da shi kaɗai ya san me ya ke furtawa. Yana gama rufe bakinshi sai ga wata shirgegiyar halitta tana keto wa daga cikin gajimare sannu a hankali wata irin iska mai ta karaɗe wajen, wacce ta haddasa kaɗawar rassan bishiyu sai da halittar ta sauka a bisa turba sannan komai ya samu dai-daituwa ita dai halittar takasance wani narkeken ƙaton aljani mai girma da munin tsiya, yana rusheshen kai mai ɗauke da 'yan mini-minin idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshi mai girma ne ƙofafin masu faɗi tamkar garwashin wuta, bakinshi tafkeke ne tamkar ƙofar gari mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora, Yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda goma a kowanne kwiɓin hammatarshi, gaba ɗaya jikinshi cike yake da wani irin baƙin gashi buzu-buzu. Babban abun da ya ƙara mashi muni shine wani zabgegen gemun shi mai tsawon kamu shida. Kaico! Haƙiƙa babu wata halitta mai numfashi da za ta yi tozali da wannan aljani face ta yi nadamar wanzuwar ta a doron ƙasa. Aljanin ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Abu-Raudat, Sannan ya buɗe bakinshi a karo na farko ya fara magana cikin wata irin kakkausar mai kama da saukar aradu, kanshi a sunkuiye ya ce "ya shugabana yau fiye da shekaru hamsin rabon da ka yi min wannan kiran, tun lokacin kana samartaka. Me kake da buƙata gane gare ka ya ubangidana". Abu-Raudat ya dube shi ya ce "ya kai Jauharul-layal kayi sani cewa na kira ka nan domin ka yi wa 'yata Raudat rakiya tare da wannan saurayi izuwa fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar. Koda jin wannan batu daga bakin Abu-Raudat sai Jauharul-Layal ya risina cikin ladabi sannan ya dube shi cikin matuƙar damuwa ya ce "ya shugabana kana ganin cewa zamu cimma nasarar shiga fadar Sarkin bokaye kuwa kar ka manta cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai ɗauke da musiba da annoba tamkar fadar Bazzagul-Nadiyar". Koda jin wannan batu sai Abu-Raudat ya dube shi ya ce "haba sarkin matasan aljanu kai ne fa ANNOBA ƊARI mai share TAWAGAR MAYAƘA kai ne hadari mai shayar da RUWA DA ISKA na musiba. Faɗuwar gaba asarar namiji, shin har akwai wani mahaluki da zai razana ka". Koda jin wannan kirari daga bakin Abu-Raudat sai jikin Jauharul-Layal ya kama tsuma tamkar nazari, ya ɗago da kanshi cikin ladabi ya ce "ya shugabana na rantse da ƙabarin kakana Marganun-uƙub ba zan dawo gare ka ba face na samu nasara shiga fadar bokaye. Koda gama faɗin hakan sai Jauharul-Layal ya shimfiɗe gadon bayanshi, Nan take Raudatul-Abyad ta ruga izuwa inda mahaifinta yake ta faɗa kan ƙirjinshi tana mai fashe da kuka, Abu-Raudat ya rungume ta, na wani lokaci daga bisani ta janye jikinta daga nashi ta dube shi cikin alamun matuƙar tausayi lokacin da idanuwanta suka ciko da ƙwalla ta ce "ya abbana haƙiƙa na shaƙu da kai ainun tsawon shekaru tun ina yarinya ƙarama, ban san kowa ba sai kai, yau ga shi zan tafi nayi nesa da kai inda bana da tabbacin zamu sake saduwa da juna ba"; Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai mahaifinta ya dube ta lokacin da ƙwalla ta cika mashi idanu ya dube ta ya ce "ya farin cikin rayuwata kuma sanyin idaniyata kiyi sani cewa na fi ki jin zafi da raɗaɗin rabuwa dake, domin a halin yanzu na rasa komai na jin daɗin rayuwa, dukiya, mulki da SADAUKANTAKA. A halin yanzu yanzu shekaru na sun ja a Kowa ne lokaci ajali zai iya riskata, domin koda a halin yanzu bamu rabu ba, tabbas akwai mutuwa. Kin ga dole na zaɓa miki abin da zai inganta rayuwarki kuma ya ba ki farin ciki. Wasiyya ta a gare ki ita ce duk sa'adda rai da rabo suka kai ki izuwa birnin Madinatul-Aswaj ki cika burin zuri'armu na ɗaukar fansa akan sarauniya Jauharat. Lokacin da tsoho Abu-Raudat ya zo nan azancen shi sai duk biyun suka fashe da kuka mai tsuma zuciya suka sake ƙanƙame juna. Al'amarin da ya sanya na ji ƙwallar tausayi ta zubo min, domin rabuwa da masoyi babu daɗi, duk da dake War zuciya irin ta aljani Jauharul-Layal sai da ƙwalla ta zubo mashi. Tsawon daƙiƙa hamsin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Raudatul-Abyad ta janye jikinta daga na mahaifinta ta nufi inda nake, ba tare da wani ɓata lokaci ba ni da ita muka hau bisa Jauharul-Layal muka zauna. Jauharul-Layal ya yunƙura cikin zafin nama irin na GWARAZAN JIYA ya buɗe manyan fuka-fukan shi ya tashi izuwa sararin samaniya ya fara keta giza-gizai. Tun Abu-Raudat na iya hangen mu har muka ɓace mashi da gani, ana fara wannan tafiya sai na cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin matsanancin gudun da Jauharul-Layal ke yi, domin a iya tsawon rayuwata ko a tarihi ban taɓa jin aljani mai matuƙar gudu a sararin samaniya tamkar shi ba. Sai da muka shafe tsawon sa'a bakwai a sararin samaniya muna tafiya babu sassauci ba tare da mun yada zango ba, lokacin da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ne, Jauharul-Layal ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a bisa turba. Inda aka saukar ya kasance daji mai tattare da dogwayen bishiyu, duwatsu, ƙoromu da sarƙaƙiya. Ko iya shirun da ya wanzu a dajin ya isa ya jefa razani a zukatan duk wata halitta. Cikin alamun matuƙar damuwa na dubi Raudatul-Abyad na ce "ya sarauniyar kyawawa shin bakya ganin cewa yada zango a wannan daji a haɗari sosai, ki duba ga ki ga yadda yanayin shi yake ? Har Raudat ta buɗi baki da nufin ta furta wani abu sai sarkin matasan aljanu ya yi caraf na tari numfashin ta ya ce "ai an kare zai yi cizo ake siyo shi a kiwata. Domin koda akwai abubuwa masu cutar a wannan daji dole ne mu yada zango domin mu samu ƙwarin jikin da zamu tunkari fadar Sarkin bokaye". Raudatul-Abyad ta ce "kwarai kuwa zancen ka dutse ya sarkin matasa, domin haka sai mu kasance cikin shirin ko ta kwana". Koda gama faɗin hakan sai muka nufi wata itaciya, bayan mun zauna a ƙarƙashin ta sai muka fito da abin guzuri muka shiga kimtsa cikinmu, bayan mun kammala ne sai muka kishingiɗa domin mu huce gajiyar dake tattare, shi kuwa Jauharul-Layal sai ya shiga yin rangadi a wajen domin tabbatar da cikekken tsaro. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana a wajen. Budurwar ta kasance doguwa mai kyawun diri da sura. Hancinta dogo ne mai lankwasa da kyawu a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta mai kyawu ne dogo tamkar na barewa, kirjinta cike yake kuna a tsaye ƙyam! Ba su ranƙwafa ba, sai sheƙi suke tamkar nunanniyar gwanda, gwanin ban sha'awa, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya buɗe ya yi tudu ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi da fatar su ta kasance luwai-luwai tamkar ta jaririya sabuwar haihuwa, sanye take cikin tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama da suka kama jikinta ainun duk wata sura da zata ja hankalin namiji ta bayyana. Littafin kuɗi ₦400 Za'a biya kuɗin ta wannan hanya Kamar haka 0084279025 Usman Umar Mansur Access bank Sai a tura shaidar biya ta wannan number 08137237071 Don Allah idan ka san ba za ka biya ba kar ka yi min magana Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na biyar domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071

❤️ 👍 4
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
2/13/2025, 11:38:46 AM

KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI Littafin kuɗi ne ₦400 8137237071 Usman Umar Mansur Opay Sai a tura shaidar biyan ta wthapp number 08137237071 Babi na biyar Wohoho! Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kwaɗaitu da soyayyarta Sa'adda muka yi arbda da wannan kyakkyawar sura sai muka miƙe tsaye zumbur! Aka fara kallon-kallo tsakaninmu, a iya tsawon rayuwata ban taɓa ganiko jin wata 'ya mace mai kyawu tamkar budurwar ba. Duk da irin kyawun diri na Raudatul-Abyad amma budurwar ta zarce ta matuƙa ainun. Tsawon daƙiƙa hamsin muna cikin wannan hali sai daga bisani ne kyakkyawar budurwa ta buɗi cikin wata irin zazzaƙar murya tamkar ana busa sarewa ta ce "yakai Matawus ibn Raziwan tare da Raudatul-Abyad bintu Abu-Raudat ku yi sani cewa tsawon shekaru huɗu ina jiran dakon samun ku domin na mallaki taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar domin cimma burina na ɗaukar fansar ran mahaifina a hannun sarakunan duniya huɗu na kuma mulki duniya baki ɗaya. Fatana na cikawa abbana burinshi na mulkar duniya baki ɗaya, Saboda haka kira na a gare ku ku gaggauta damƙa min taswirar fadar cikin ruwan sanyi, idan kuwa kuka ƙi ta lumana azabar KAIFIN TAKOBI na zata tabbata a gare ku". Koda jin wannan batu daga bakin kyakkyawar budurwar sai na dube ta cikin matuƙar fushi na ce "ya ke wannan AZZALUMA kiyi sani cewa haƙiƙa rafkananniyar zuciyarki ta yaudare ki da ta bayyana maki cewa za ki iya yi mana fashi da makami, wato ƙura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Kuma ina so kiyi sani cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, ko ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza" kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Zamu ga yadda za ki karɓe taswirar daga hannunmu." Koda jin wannan daga bakina sai kyakkyawar budurwar ta fusata ainun, idanuwanta suka kaɗa suka yi jajur, har ƙwalla ta zubo mata ta dube mu ta ce "haƙiƙa rashin sani ne ya sanya har ka amba ce ni da azzaluma, amma akwai buƙatar na sanar da ku labarina a takaice. A da can baya kimanin shekaru dubu ɗaya da ɗoriya da suka gabata, lokacin da Ƙarfin sihiri da na jarumataka suka zamto jari hujja, zalunci gami da yaudara suka yi katutu a zukatan bil'adama, kowanne sarki burin shi ya kai farmaki zuwa ɗan uwanshi ya mamaye ƙasar shi ta dawo izuwa ƙarƙashin masarautarshi. A wannan lokaci akwai manyan biranen duniya da suka shura, waɗanda gaba ɗaya sune ke tafiyar da mulkin duniya baki ɗaya. Biranen sun haɗar da birnin Sin, Rum, Misra da birnin Hindu. Birnin Sin na ƙarƙashin mulkin sarki Abul-uyum. Abul-uyum ya kasance gwarzon mayaƙi mai dakawa maza gumba a hannu, an ce saboda Jarumtakarshi yana iya shafe tsawon kwana uku yana yaƙi ba tare ya ci ko ya sha ba ballantana gajiya, batun ƙarfin sihiri, dukiya da rundunar mayaƙa kuwa ya yiwa gaba ɗaya sarakunan yammacin duniya zarra. Bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu ga sarakunan nahiyar. Birnin Rum yana bisa jagorancin sarki Fitinatul-muluk ibnu Larab, Fitinatul-muluk ya kasance hatsabibin matsafi, gwarzon jarumi ma'abocin tarin dukiya dangin lu'ulu'u da dabbobin ni'ima, masu hasashe da bincike sun tabbatar da cewa a iya fadar shi akwai dakarun aljanu da na bil'adama guda miliyan ɗaya, bayan waɗanda aka tanade su domin kai farmaki izuwa birane da ƙasashe domin FATAUCIN BAYI, kusan komai dake fadar shi an samar da shi ne da ƙarfin sihirin tsafi. Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan ke yi mashi laƙabi ya da ANNOBAR SARAKAI. Sarki Hubaizu ibnu Shardas kuwa shine ke riƙe da Kambun birnin Hindu. Hubaizu mutum ma'abocin sadaukantaka ta gaban kwatance, sanin alƙalumman sihiri, gami da tarin dukiya. A jerin sarakunan da aka yi a birnin Hindu shine sarki na saba'in, ya hau karagar mulki tun yana matashi ɗan shekara sha biyar, kuma a halin yanzu yana da shekaru saba'in cif a duniya, bisa binciken bokaye da masu hasashe sun gano cewa a kowacce rana sarki Hubaizu yana samun sabbin sirrikan tsafi guda miliyan ɗaya, yana samun sirrikan ne a duk sa'adda da sadu da wata kuyangarshi. Bokayen sun gano cewa duk sa'adda da hakan ta faru ƙarfin damtsenshi yana ƙaruwa sau hamsin cin ɗari. Bisa wannan dalili ya sanya ya zamto wa sarakunan nahiyar ANNOBA ƊARI. Birnin Misra na bisa jagorancin wani gwarzon mayaƙi ne da ake yiwa laƙabi da Ayumul-barƙas ibnu Zairul. Sarki Ayumul-barƙas mutum mai tattare da abubuwan al'ajabi ba ya tsafi kuma sihiri ba ya tasiri akan shi, komai yawan sirrikan tsafinka idan kayi arba da shi take za su daina amfani. Gaba ɗaya sarakunan biranen huɗu, Abul-uyum, Hubaizu, Fitinatul-muluk da sarki Ayumul-barƙas sun kasance basa ga muciji da juna, burin kowannen su shine ya kawar da abokan gabar shi domin ya zamto sarkin SARAKAI na duniya. Bisa binciken da sarakunan suka gudanar shine ɗyan su ba zau iya cimma wannan buri na shi ba face ya mallaki wani kundi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN AL'AJABI dake ajiye a kogon GARUL-SHAMMAR. shi dai KUNDIN AL'AJABI na ɗauke da sirrikan tsafi guda miliyan dubu hamsin, babu wani mahaluki a doron ƙasa walau mutum ko aljan da zai mallaki kundin face ya zamtowa duniya gagarabadau kuma ANNOBA ƊARI. Koda mutum ya mallaki KUNDIN AL'AJABI ba zai iya sarrafa shi ba face ya mallaki wata kuba da ake yiwa laƙabi da Miftahul-sihir, a halin yanzu kubar Miftahul-sihir ta rabu kaso huɗu, kowanne sarki daga cikin sarakunan huɗu yana ɗauke da ɓari guda, dukkaninsu sun mallaki ɓarin kubar a hannun mahaifan su. Sa'adda sarakunan huɗu suka ga wannan al'amari a cikin halarar tsafin su sai hankulansu suka dugunzuma ainun, abu na farko da ya dugunzuma hankulan su shine. Ta ya ya ɗayan su zai yaƙi sauran abokan gabar shi har ya raba su da sassan kubar guda uku, bayan cewa fiye da shekaru goma suna kwabza yaƙi tsakanin su amma babu nasara, sai dai a samu asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa. Abu na biyu da yafi tayar masu da hankali shine a cikin su babu wanda yake da ikon shiga kogon GARUL-SHAMMAR har ya ɗauko KUNDIN AL'AJABI face wani barde da ake yiwa laƙabi da Yasiran jin Taufid. Yasiran ya kasance mafarauci, fiye da rabin rayuwarshi ya yi ta je a daji tare da iyalan shi. Abun tambaya anan shine ta ya ya ɗayan su zai mallaki mafarauci Yasiran? Bisa dogon nazari da sarakunan suka yi sai suka samu mafita tsakanin su. Mafitar kuwa ita ce kowannen su zai bayar da ɓarin kubarshi a haɗe waje guda, sannan a nemi taimakon mafarauci Yasiran, idan ya so bayan ya samu nasarar ɗauko KUNDIN AL'AJABI sai a kwabza yaƙi tsakanin su, duk wanda ya yi nasara sai ya mallaki kundi da kuba. Kamar yadda sarakunan suka tsara haka al'amarin ya kasance, wata rana da la'asar sakaliya mafarauci Yasiran da matarshi Zarilat sai ni 'yarsu Sulaiza muna zaune a cikin bukka muna fira cikin nishaɗi sai kawai muka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai sun cika dajin baki ɗaya. Cikin matuƙar kaɗuwa abbana na miƙe tsaye zumbur yana mai ɗaukar KWARI DA BAKAN shi ya yunƙura ya durfafi ƙofar fita, har na yunƙura zan bi shi a baya sai ya dakatar da ni ta hanyar dafa kafaɗuna ya dube mu ni da mahaifiyata ya ce "ya farin cikin rayuwata bana so wani abu ya ɗaga maku hankali kawai ku zauna naje na duba domin naga mene ne ke faruwa". Koda jin wannan batu daga bakin abbana, sai idanun mahaifiyata suka ciko da ƙwalla kuma ta janyo ni ta rungume ni a ƙirjinta, sannan ta dube shi muryar ta cike damuwa ta ce " ya muradin zuciyata kayi sani cewa yau tsawon shekaru ashirin muna zaune a wannan daji ba a taɓa samun wata muguwar dabba, ko dakarun sumame sun kawo mana farmaki ba sai a yau, jikina ya bani cewa babu alheri a tare wannan fita taka". Koda jin wannan batu daga bakin mahaifiyata sai ya dube mu cikin alamun matuƙar tausayi ya ce "ya abar kaunata ki kwantar da hankalinki da yardar abun bauta zan dawo gare ku cikin ƙoshin lafiya". Koda gama faɗin hakan sai mahaifina ya juya ya fice daga turakar yana mai kunna kai izuwa ɓangaren da yake jin takun sawayen, yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mahaifina ya yi arba da waɗansu zaratan mayaƙa su huɗu zaune a bisa ingarmun dawakai, dukkanin su suna shirye cikin gagarumar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro sun rufe fusakunsu idanunsu kaɗai ake gani. Kafin abbana ya yi wani yunƙuri sun yi mashi ƙawanya suna masu kewaye shi, cikin dakewar zuciya mahaifina ya dubi mayaƙan cikin matuƙar fushi ya ce "ya ku waɗannan mayaƙa shin mene ne nufin ku a gare ni? Koda jin wannan tambaya sai kowannen su ya ɗora hannunshi a kanshi ya cire hular ƙarfenshi take fusakunsu suka bayyana a fili ƙarara. Sa'adda mafarauci Yasiran ya yi arba da fusakun na su sai hankulanshi ya dugunzuma ainun tsoro ya kama shi, Domin a iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin sadaukai masu matuƙar kwarjini da ban tsoro tamkar mayaƙan ba. Daga can sai wani daga cikin mayaƙan mai ƙirar samudawan farko fuskarshi a murtuke take babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya ce "ya kai Yasiran ibnu Taufid ka yi sani cewa bamu zo gare ka domin cutar da kai ba sai domin mu taimaki juna tsakaninmu, don haka sai ka tsaya ka saurari bayanin da zan yi maka da idanun basira. Ya kai Yasiran kayi sani cewa bakomai ne ke tafe damu izuwa gare ka ba, face muna so ka tafi izuwa tekun Bahar-rum ka shiga kogon GARUL-SHAMMAR domin ka ɗauko mana wani littafi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN AL'AJABI, domin mu tseratar da al'ummar ƙasashenmu daga annobar fari da junya dake addabar su, ka yi sani cewa matsawar ka cika mana wannan buri namu, ni Ayumul-barƙas da sauran 'yan uwana Fitinatul-muluk, Hubaizu, da sarki Abul-uyum zamu baka ladan dukiya mai tarin yawa wacce kai da zuri'arka ba su taɓa cinye ta har tattaɓa kunnen ka, sannan kai da kan ka zaka zaɓi inda kake don ka zauna tare da iyalan ka a ɗaya daga cikin biranen mu huɗu". Lokacin da sarki Ayumul-barƙas na birnin Hindu ya zo dai-dai nan a zancen shi sai sauran sarakunan suka gyaɗa kai dake nuni da tabbatar da maganar da ɗan uwansu ya faɗa, suna masu cewa a ransu haƙiƙa sarki Ayumul-barƙas ba ƙaramar hikima ya yi ba da ya ɓoyewa Yasiran gaskiyar batun KUDNIN AL'AJABI ba, amma a ɓangare guda zukatansu cike suke da mugun tanadi. Tsawon daƙiƙa hamsin mafarauci Yasiran yana nazarin maganar da sarki Ayumul-barƙas ya yi mashi. Abu na farko da ya faɗo mashi a rai shine, mene ne ya sanya waɗannan sarakuna suka zaɓe shi a matsayin wanda zai ɗauko masu KUNDIN AL'AJABI bayan cewa dukkanin su manyan jarumai ne da za su iya aiwatar da hakan? Sannan ma shin wane tabbaci kake da shi cewa zaka dawo ka tarar da iyalanka cikin ƙoshin lafiya, wani ɓangaren a zuciyarshi kuma na cewa da shi ka tuna asarar miliyoyin rayukan jama'ar da zaka ceto idan ka ɗauko KUNDIN AL'AJABI. Sa'adda mahaifina yazo nan a tunanin shi, sai kawai ya cire kai ya dubi sarki Ayumul-barƙas, sannan ya yi gyaran murya ya ce "na amince zan biya maku wannan muhimmiyar buƙata amma ina buƙatar ku bani lokaci na yi nazari". Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai sarakunan suka sake duban juna gami da yiwa juna murmushi mai tattare da tsantsar mugun tanadi. A can dajin Harbul-zawat kuwa ina zaune tare da mahaifiyata cikin tashin hankali, sai mu kaji abbana ya yi gyaran murya ya tura ƙofar hujjar, koda muka yi arba da shi sai muka riga izuwa inda yake suka faɗa kan ƙirjinshi ya rungume mu, muna masu fashewa da kuka. Sai daga bisani ne ya janye jikinshi daga namu ya dube mu fuskarshi cike da annuri, nan take ya zayyane mana abin da ya wakana tsakanin shi da sarakunan tun daga farko har ƙarshe. Koda jin wannan jawabi sai mahaifiyata ta cika da matuƙar farin ciki, amma kuma sai hankalinta ya dugunzuma ainun, abin da ya dugunzuma hankalin nata shine shin akwai tabbacin cewa abbana ba zai rasa rayuwarshi wajen shiga tekun Bahar-rum ba? Sannan wata shaida gare shi dake tabbatar da cewa sarakunan ba su ci amanar shi ba? Cikin alamun matuƙar damuwa mahaifiyata ta dubi abbana ta ce "haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki bisa jin wannan gagarumin aikin ceton al'umma da zaka yi, sai dai ina matuƙar tsoron ka rasa rayuwarka a wannan hali, sannan kar mutanen da ka aminta da su suci amanarka". Koda jin wannan batu daga bakin ummina sai mahaifina ya yi murmushi a gare ta ya ce "ki kwantar da hankalinki babu wani sharri da zai same ni, kar ki manta cewa NASARA DA ƊAUKAKA na tare da ma'abocin gaskiya da riƙon amana, kuma ciki da gaskiya wuƙa bata huda shi. ke dai ki kasancewa mai yi mani fatan alheri a kodayaushe. Koda jin wannan batu sai muka sake rungume shi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Mu haɗu a babi na shida domin jin cigaban wannan ƙayataccen littafi na KUNDIN AL'AJABI. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071

👍 🙏 ❤️ 6
Link copied to clipboard!