
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 12, 2025 at 08:55 PM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Shekarar Rubutu
10-02-2024
Wthapp Number
08137237071
https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
KUNDIN AL'AJABI
GWARAZAN JIYA
Babi na huɗu
Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan mun kammala kalaci sai muka yi ɗauki kayan aiki muka nufi gona tare da Raudatul-Abyad, yau ma kamar kullum fuskarta rufe take da rawani kuma tana sanye da baƙaƙen tufafi a gadon bayanta tana ɗauke da wata zabgegiyar takobi, shigar da ta yi matuƙar yi mata kyawu.
Tafe muke cikin hanzari ta gaba ina biye da ita a baya, tsawon daƙiƙa ɗari biyu muna cikin wannan hali babu wanda yace ƙala. Sannu a hankali har muka iso wata makekiyar gona mai ɗauke da alkama mai tsawon hetta goma. Koda muka iso ɗin sai Raudatul-Abyad ta miƙa min fartanyar dake hannunta gami da lauje na karɓa sannan ta yi min nuni da na fara aiki batare da buɗi baki ta ce min uffan ba, kawai sai ta durfafi gindin wata itaciya ta kwanta bisa wata tabarmar kaba mai haɗe da matashi, kawai sai na duƙufa na fara aiki, wasa-wasa sai ga shi na shafe tsawon sa'a ɗaya a cikin wannan yanayi, koda na ɗaga kaina na duba aikin da na yi sai naga ashe bai huce kunya goma ba, a wannan lokaci hasken rana ta fito ta fara zafi ainun.
Al'amarin da ya sanya kishi ya fara damuna, kuma gadon bayana ya fara ciwo. Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ina cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai na ga waɗansu masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, cikin wani irin zafin nama na dinga zillewa kibbau ɗin tare da falfalwa da azababban gudu izuwa inda Raudatul-Abyad ke kishingiɗe domin na bata kariya, a wannan lokaci barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, koda ya rage saura taku biyar na isa daf da ita kwatsam ba zato babu tsammani sai waɗansu irin samudawan dakaru suka yi fitar burgu daga duhuwar dajin,
Dakarun suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, fuskokinsu a rufe suke da hulunan ƙarfe, a hannayensu suna ɗauke da miyagun makamai dangin Gatari, sungumi, majaujawa, al'amudi da sauran su. Adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya, kafin nayi wani yunƙuri sun yi min ƙawanya suna muzurai tamkar za su ci babu.
Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakaninmu sai na lura wani badakare ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad.
Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo, daga can sai wani narkeken ƙato ya fito daga cikin su, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa shine shugabansu saboda hular kwanon da ke kanshi da takobinshi da ta kasance ta musamman,
Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi har iya isa daf! Da inda Raudatul-Abyad take ta yadda suna jin numfashin juna. Kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba, daga bisani kuma sai ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da SAƘON MUTUWA, sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya dubi Raudatul-Abyad ya ce "ya ke Raudatul-Abyad 'ya ga tsoho Abu-Raudat kiyi sani cewa dama na faɗa miki in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana za su haɗu, kuma rabon kwaɗo baya hawa sama koda ya hau zai sakko.
Yau ga shi kin faɗa tarkona wanda ya za ki iya tserewa ba, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan kashe wannan baƙo naki a gaban idanuwanki sannan na tafi dake a matsayin sabuwar amaryata…".
Kafin narkeken ƙaton ya gama rufe bakinshi ya gama rufe bakinshi Raudatul-Abyad ta tari numfashin shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "Dawazul-kiryan kayi sani cewa haƙiƙa ka tafka babban kuskure da rafkananniyar zuciyarka ta yaudare ka cewa za ka ci galaba a kaina, ka sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA ba za su taɓa zamtowa abu guda ba, ni MURUCIN KAN DUTSE ce ban fito ba sai da na shirya. Kuma ni ƙadangaren bakin tulu ce..
Shawarar da zan baka ita ce ka gaggauta miƙa wuya gare ni wata ƙila ka samu tsira da ruhinka";
Dawazul-kiryan ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya ce "haƙiƙa ƙi faɗin ki tana matuƙar burgeni domin masu iya magana na cewa wai matsoraci baya zama gwani. Amma kar ki manta cewa alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, kuma koda ba a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza. Kuma dai SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI.
"Haƙiƙa ka makara wajen cimma wannan burina naka, amma ko ba komai an ce ba a ƙwacewa yaro garma. Kuma inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa"
Raudatul-Abyad ce ta yi wannan furuci cikin matuƙar fushi.
Dawazul-kiryan ya ce "ai zuwa a makare yafi zuwa a makara, kuma duk mai nema yana tare da samu".
Koda gama faɗin hakan sai yaran Dawazul-kiryan suka yi wuf suka zare makaman su suka yi ihu da kururuwa sannan suka yi ɗauki izuwa kaina.
Yayin da naga hakan sai na zare takobina ya ruga gare su domin tarar juna,
Lokacin da aka haɗu sai a kayi KARON MAZA, aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, ana fara wannan artabu ne na fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba.
Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje ta cika dodon kunne, duk sa'adda na kaiwa dakarun hari sai ka ga sun kare tare da mayar da martani, in da ba don ina da matuƙar zafin nama ba da tuni sun murƙushe ni saboda yadda suka yi min rubdugu tamkar yadda dandazon ƙudade ke yanyame ƙwallon mangwaro.
Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi kuma na fahimci cewa idan aka cigaba da wannan artabu a haka wankin hula zai kai ni dare kuma dakarun za su samu nasarar kashe Raudatul-Abyad.
Koda na zo nan a tunani na sai na fusata ainun na sake dage damtse ina kai sara da suka cikin matuƙar zafin nama, gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canja dole rawa ma ta canja, faruwar hakan ke da wuya sai na fara samun galaba akan dakarun, yazamana cewa duk inda na sanya a gaba sai dai kaga fili fetal dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga.
Al'amarin da ya fusata sauran mayaƙan kenan suka sake yin ɗauki izuwa kaina, kafin shuɗewar daƙiƙa ɗari kacal na kashe fiye da rabin dakarun. Nan fa JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda.
Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan artabu na zubar da dukkan mayaƙan a ƙasa hatta badakaren da ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad, illa shugaba Dawazul-kiryan ne kaɗai a tsaye fuskarshi a murtuke tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakani na da Dawazul-kiryan na wani lokaci daga can sai ya dube ni cikin kakkausar murya mai tattare da fushi ya ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin taurin kai da shisshigi kayi sani cewa zaki koda ya mutu gawarshi abar tsoro ce, KARO DA GOMA kalacen safe in ji masu iya magana, kuma masu iya magana na cewa kaɗe mage ba yanka wa ba ne.
Saboda haka idan ka miƙa kan ka izuwa gare ni, zan yi maka kisa mafi sauƙi ta hanyar datse gaɓoɓin jikinka ɗaya-bayan-ɗaya ba tare da kasha wahala ba.
Idan kuwa ka ƙi to zaka gwammace wa aya zaƙin ta";
Kafin ya gama rufe bakinshi na tari numfashin shi ina mai daka mishi tsawa na ce "ya kai wannan tsohon AZZALUMI kar ka manta cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Kuma shi zalunci baya ɗorewa a doron ƙasa, don haka sai ka shirya ga maza nan bisa kan ka.
Koda gama faɗin sai na ɗaga takobina na durfafi inda yake tsaye ina kururuwa koda ganin hakan sai Dawazul-kiryan ya yi wuf ya zare wani zabgegen gatari a gadon bayanshi ya yi ɗauki kaina, muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Koda fara wannan artabu sai Raudatul-Abyad ta koma gefe guda ta harɗe hannaye tana kallon yadda gumurzun ke wakana.
Nan fa muka wanzu muna kai wa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta GWARAZAN JIYA. kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce artabun gwani da gwani daɗin kallo gare shi, kuma idan BABBAR GIWA ta fito filin fama babu wanda yake yin fito-na-fito da ita face GWARZON ƘARNI.
Kuma masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne ma fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana.
Ga wanda ke kallon yadda gumurzun ke wakana zai fahimci cewa Dawazul-kiryan ya nunka ni a ƘARFIN DAMTSE sau uku. Domin kuwa duk ya kai min hari da gatarinshi idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci na fara galabaita ya zamto ba na iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kaina, ana cikin wannan hali ne Dawazul-kiryan ya shammace ni ya makamin ƙotar gatarinshi a akaina saboda ƙarfin dukan sai dai kan ya tsage jini ya yi tsartuwa, saboda matuƙar zugi da raɗaɗi ban san sa'adda na kurma ihu ba na yi taga-taga zan faɗi amma sai na turje, sai dai kash! Kafin na dawo cikin hayyacina ya sake samun nasarar makamin a wuya. Nan take na sulale ƙasa magashiyan ina nishin wahala.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai Dawazul-kiryan ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska ya dube ni ya ce "ai da ma na faɗa maka a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe" kuma komai tsananin duhun dare gari zai waye".
Yanzu ga shi kana kusa da baƙuntar barzahu za ka yi mutuwar wulaƙanci, alfarma ɗaya zan yi maka ita ce ka rubuta wasiyyarka kafin na zare maka ruhi daga gangar jiki".
Duk wannan abu dake wakana sai Raudatul-Abyad na tsaye a gefe guda tana kallo.
Dawazul-kiryan na gama faɗin hakan sai ya durfafi inda nake kwance ya raba ƙafafuwanshi biyu a kaina yana mai yi min murmushim mugunta, kawai sai ya ɗaga gatarinshi domin ya datse min wuya, kawai sai wata hikima ta faɗo min na damƙi ƙasa a hannuna na watsa mashi a fuska.
Kafin ya wartsake na miƙe tsaye zumbur na sanya takobina na sare mashi wuya take kan yi fitar burgu jini ya yi feshi gami da tsartuwa gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica!.
Nan take na faɗi ƙasa bisa gwiwoyina cikin matuƙar galabaita.
Cikin matuƙar kaɗuwa Raudatul-Abyad ta rugawa izuwa inda nake ta rungume a ƙirjinta tana mai fashe da kuka mai tsuma zuciya duk da kasancewar ina cikin mawuyacin hali sai da naji sanyi a raina gami da farin ciki. Bisa jin Raudatul-Abyad a daf da ni.
Sannan daga bisani ta janye jikinta daga gare ni muka fuskanci juna cikin alamun matuƙar tausayi ta dube ni kana ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai ɗan-karen daɗi tamkar alagita ta ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin sadaukantaka haƙiƙa na yaba da sadaukantakar ka kuma ma yarda cewa kai mai amana ne, kai ne irin namijin da ya dace ya zamto abokin rayuwata. Ina mai matuƙar farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara.
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Daga wannan furuci ne kuma ta shiga bani kulawa inda ta tashi tafaɗuna muka isa ƙarƙashin itaciya ta zaunar da ni sannan ya ɗauko salkar ruwa ta buɗe murfin ta ta sanya hannunta ta tallafo wuyana ta kafa min a baki na shiga kwankwaɗar ruwan har na ƙoshi, kana ta buɗe wata jakar fata dake sanye a kwiɓin cinyarta ta buɗe ta ɗauko wani gashasshen naman barewa ta shiga bani a baki ina ci cikin matuƙar tsantsar soyayya da tausaya wa.
A iya tsawon rayuwata ban taɓa sanin cewa haka so yake da daɗi ba.
Haƙiƙa so shine sinadari mafi girma dake sanya zuciya da ƙarfafa garkuwar jikin ɗan Adam.
So shi ne linzami da yafi ƙugiya ƙarfi wajen sarrafa bil'adama a doron ƙasa.
Haƙiƙa so kan sauya duniyarmu daga kowanne ƘARSHEN KARNI izuwa SABON ƘARNI mai cike da abubuwan ban mamaki.
Tabbas so shine ni'ima mafi daraja a cikin dukkanin wata al'umma.
A wannan rana haka muka kasance tare da Raudatul-Abyad tana ba ni kulawa mai cike da tsantsar bege da soyayya.
Sai da la'asar sakaliya sannan muka nufi komawa izuwa gida, da yake a wahale nake sai ya zamana daƙyar nake iya takawa domin haka kafin mu isa gida duhun dare ya kawo kai. lokacin da muka samu nutsuwa sai Raudatul-Abyad ta kwashe dukkan labarin abin da ya faru da damu ta zayyanawa mahaifinta Abu-Raudat daga farko har ƙarshe.
Koda jin wannan labari sai farin ciki ya turnuƙe shi bai san sa'adda murmushi mai taushi ya suɓuce mashi ba ya dube ni cikin murya mai tattare da dattijantaka ya ce "ya kai Matawus kayi sani cewa kai ne matashi na arba'in da biyar da suka zo gare ni domin na bayyana masu hanyar da za su haye tekun dake gaɓar mu domin su isa izuwa fadar Sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar.
Babu wani mahaluki ɗaya a cikin su da ya samu nasarar cinye jarabawar da na yi masu sai kai, 'ya ta Raudat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance da babu wani ɗa namiji da zai yi tozali da ita face ya kamu da matuƙar sha'awar ta, amma gashi ka keɓance da ita ba tare da ka haike mata ba,
Sannan kana da halin da za ka ƙi ceto rayuwar 'yata a lokacin da dakarun sumame suka farauce ta.
Tsawon lokaci ina jiran zuwan jarumin da zan damƙawa amanar 'yata a hannun nagartaccen namiji, kuma GWARZON ƘARNI amma sai a yau na cimma burina. Kasancewar a halin yanzu shekaru na sun ja tsufa ya kamani kuma cutar da nake fama da ita a koda yaushe rai zai iya yin halin shi, domin hakan dole na miƙa ragamar abar kaunata kuma farin cikina ga wanda zai bata farin cikin rayuwa har abada.
Ina mai farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara akan abin da ka fito nema".
Lokacin Tsoho Abu-Raudat yazo nan a zancen shi sai ya sanya hannunshi ya ɗaga gefen shimfiɗar da yake zaune ya ɗauko wata jemammiyar fatar barewa ya miƙa min sannan ya ci gaba da cewa "wannan ita ce taswirar da zata kai ka izuwa fadar boka Bazzagul-Nadiyar da dukkan bayanan kowacce ƙofa da dokokin shiga fadar.
Sannan ina mai damƙa maka amanar 'yata ka riƙe min ita cikin aminci, bana sa rai za ku dawo ku same ni a raye.
Zan haɗa ku da hadimin da zai yi maku rakiya a cikin wannan tafiya har ku cimma nasara.
Koda gama faɗin hakan sai Abu-Raudat ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar fita daga bukkar cikin hanzari ni da Raudat muka rufa mashi baya.
Ya yin da muka fito ne sai Abu-Raudat ya buɗe bakinshi yana mai karanto waɗansu ɗalasimai da shi kaɗai ya san me ya ke furtawa.
Yana gama rufe bakinshi sai ga wata shirgegiyar halitta tana keto wa daga cikin gajimare sannu a hankali wata irin iska mai ta karaɗe wajen, wacce ta haddasa kaɗawar rassan bishiyu sai da halittar ta sauka a bisa turba sannan komai ya samu dai-daituwa ita dai halittar takasance wani narkeken ƙaton aljani mai girma da munin tsiya, yana rusheshen kai mai ɗauke da 'yan mini-minin idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshi mai girma ne ƙofafin masu faɗi tamkar garwashin wuta, bakinshi tafkeke ne tamkar ƙofar gari mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora,
Yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda goma a kowanne kwiɓin hammatarshi, gaba ɗaya jikinshi cike yake da wani irin baƙin gashi buzu-buzu.
Babban abun da ya ƙara mashi muni shine wani zabgegen gemun shi mai tsawon kamu shida.
Kaico! Haƙiƙa babu wata halitta mai numfashi da za ta yi tozali da wannan aljani face ta yi nadamar wanzuwar ta a doron ƙasa.
Aljanin ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Abu-Raudat,
Sannan ya buɗe bakinshi a karo na farko ya fara magana cikin wata irin kakkausar mai kama da saukar aradu, kanshi a sunkuiye ya ce "ya shugabana yau fiye da shekaru hamsin rabon da ka yi min wannan kiran, tun lokacin kana samartaka. Me kake da buƙata gane gare ka ya ubangidana".
Abu-Raudat ya dube shi ya ce "ya kai Jauharul-layal kayi sani cewa na kira ka nan domin ka yi wa 'yata Raudat rakiya tare da wannan saurayi izuwa fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar.
Koda jin wannan batu daga bakin Abu-Raudat sai Jauharul-Layal ya risina cikin ladabi sannan ya dube shi cikin matuƙar damuwa ya ce "ya shugabana kana ganin cewa zamu cimma nasarar shiga fadar Sarkin bokaye kuwa kar ka manta cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai ɗauke da musiba da annoba tamkar fadar Bazzagul-Nadiyar".
Koda jin wannan batu sai Abu-Raudat ya dube shi ya ce "haba sarkin matasan aljanu kai ne fa ANNOBA ƊARI mai share TAWAGAR MAYAƘA kai ne hadari mai shayar da RUWA DA ISKA na musiba. Faɗuwar gaba asarar namiji, shin har akwai wani mahaluki da zai razana ka".
Koda jin wannan kirari daga bakin Abu-Raudat sai jikin Jauharul-Layal ya kama tsuma tamkar nazari, ya ɗago da kanshi cikin ladabi ya ce "ya shugabana na rantse da ƙabarin kakana Marganun-uƙub ba zan dawo gare ka ba face na samu nasara shiga fadar bokaye.
Koda gama faɗin hakan sai Jauharul-Layal ya shimfiɗe gadon bayanshi,
Nan take Raudatul-Abyad ta ruga izuwa inda mahaifinta yake ta faɗa kan ƙirjinshi tana mai fashe da kuka, Abu-Raudat ya rungume ta, na wani lokaci daga bisani ta janye jikinta daga nashi ta dube shi cikin alamun matuƙar tausayi lokacin da idanuwanta suka ciko da ƙwalla ta ce "ya abbana haƙiƙa na shaƙu da kai ainun tsawon shekaru tun ina yarinya ƙarama, ban san kowa ba sai kai, yau ga shi zan tafi nayi nesa da kai inda bana da tabbacin zamu sake saduwa da juna ba";
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai mahaifinta ya dube ta lokacin da ƙwalla ta cika mashi idanu ya dube ta ya ce "ya farin cikin rayuwata kuma sanyin idaniyata kiyi sani cewa na fi ki jin zafi da raɗaɗin rabuwa dake, domin a halin yanzu na rasa komai na jin daɗin rayuwa, dukiya, mulki da SADAUKANTAKA.
A halin yanzu yanzu shekaru na sun ja a Kowa ne lokaci ajali zai iya riskata, domin koda a halin yanzu bamu rabu ba, tabbas akwai mutuwa. Kin ga dole na zaɓa miki abin da zai inganta rayuwarki kuma ya ba ki farin ciki.
Wasiyya ta a gare ki ita ce duk sa'adda rai da rabo suka kai ki izuwa birnin Madinatul-Aswaj ki cika burin zuri'armu na ɗaukar fansa akan sarauniya Jauharat.
Lokacin da tsoho Abu-Raudat ya zo nan azancen shi sai duk biyun suka fashe da kuka mai tsuma zuciya suka sake ƙanƙame juna.
Al'amarin da ya sanya na ji ƙwallar tausayi ta zubo min, domin rabuwa da masoyi babu daɗi, duk da dake War zuciya irin ta aljani Jauharul-Layal sai da ƙwalla ta zubo mashi.
Tsawon daƙiƙa hamsin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Raudatul-Abyad ta janye jikinta daga na mahaifinta ta nufi inda nake, ba tare da wani ɓata lokaci ba ni da ita muka hau bisa Jauharul-Layal muka zauna.
Jauharul-Layal ya yunƙura cikin zafin nama irin na GWARAZAN JIYA ya buɗe manyan fuka-fukan shi ya tashi izuwa sararin samaniya ya fara keta giza-gizai. Tun Abu-Raudat na iya hangen mu har muka ɓace mashi da gani, ana fara wannan tafiya sai na cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin matsanancin gudun da Jauharul-Layal ke yi, domin a iya tsawon rayuwata ko a tarihi ban taɓa jin aljani mai matuƙar gudu a sararin samaniya tamkar shi ba.
Sai da muka shafe tsawon sa'a bakwai a sararin samaniya muna tafiya babu sassauci ba tare da mun yada zango ba, lokacin da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ne, Jauharul-Layal ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a bisa turba.
Inda aka saukar ya kasance daji mai tattare da dogwayen bishiyu, duwatsu, ƙoromu da sarƙaƙiya. Ko iya shirun da ya wanzu a dajin ya isa ya jefa razani a zukatan duk wata halitta.
Cikin alamun matuƙar damuwa na dubi Raudatul-Abyad na ce "ya sarauniyar kyawawa shin bakya ganin cewa yada zango a wannan daji a haɗari sosai, ki duba ga ki ga yadda yanayin shi yake ?
Har Raudat ta buɗi baki da nufin ta furta wani abu sai sarkin matasan aljanu ya yi caraf na tari numfashin ta ya ce "ai an kare zai yi cizo ake siyo shi a kiwata. Domin koda akwai abubuwa masu cutar a wannan daji dole ne mu yada zango domin mu samu ƙwarin jikin da zamu tunkari fadar Sarkin bokaye".
Raudatul-Abyad ta ce "kwarai kuwa zancen ka dutse ya sarkin matasa, domin haka sai mu kasance cikin shirin ko ta kwana".
Koda gama faɗin hakan sai muka nufi wata itaciya, bayan mun zauna a ƙarƙashin ta sai muka fito da abin guzuri muka shiga kimtsa cikinmu, bayan mun kammala ne sai muka kishingiɗa domin mu huce gajiyar dake tattare, shi kuwa Jauharul-Layal sai ya shiga yin rangadi a wajen domin tabbatar da cikekken tsaro.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana a wajen.
Budurwar ta kasance doguwa mai kyawun diri da sura.
Hancinta dogo ne mai lankwasa da kyawu a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta mai kyawu ne dogo tamkar na barewa, kirjinta cike yake kuna a tsaye ƙyam! Ba su ranƙwafa ba, sai sheƙi suke tamkar nunanniyar gwanda, gwanin ban sha'awa, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya buɗe ya yi tudu ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi da fatar su ta kasance luwai-luwai tamkar ta jaririya sabuwar haihuwa, sanye take cikin tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama da suka kama jikinta ainun duk wata sura da zata ja hankalin namiji ta bayyana.
Littafin kuɗi ₦400
Za'a biya kuɗin ta wannan hanya Kamar haka
0084279025
Usman Umar Mansur
Access bank
Sai a tura shaidar biya ta wannan number
08137237071
Don Allah idan ka san ba za ka biya ba kar ka yi min magana
Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na biyar domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
❤️
👍
4