
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 14, 2025 at 08:57 AM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
KUNDIN AL'AJABI
Following 👉 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
Babi na shida
A ranar da tafiya kogon GARUL-SHAMMAR ta zo mun sha kukan baƙin cikin rabuwa da mahaifina, tamkar ba za mu ƙyale shi ya tafi ba.
Tun daga wannan rana ummina ce ke ɗawainiya da rayuwata, kullum cikin kewar abbanmu nake, wasa-wasa sai gashi ya shafe tsawon mako uku ba tare da mun ji ɗuriyar shi ba, al'amarin da ya sanya mahaifiyata ta fara tsammanin ko ya rasa rayuwarshi ne.
Al'amarin abbana kuwa tun sa'adda mu kayi bankwana muna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, sai kawai ya kunna kai izuwa cikin daji yana tafiya cikin hanzari, tafiyar daƙiƙa hamsin kacal ya yi ya iske su sarki Fitinatul-muluk zaune a bisa kan wani narkeken aljani mai matuƙar kwarjini muni da ban tsoro shi kaɗai suke jira, ba tare da wani ɓata lokaci mahaifina ya haye bisa kan aljanin ya zauna kamar yadda sarakunan suka yi.
Cikin kuzari aljanin ya buɗe manyan fuka-fukanshi ya luluƙa izuwa sararin samaniya yana mai keta gajimare cikin matuƙar sauri tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Tafiyar sa'a uku kacal aka yi aka iso tekun Bahar-rum, cikin hanzari aljanin ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luhh! Ya sauka a dai-dai ƙofar shiga kogon, cikin hanzari sarki Ayumul-barƙas ya fara sakkowa sai Fitinatul-muluk, Hubaizu, Abul-uyum mafarauci Yasiran ne a ƙarshe.
Ba tare da wani jinkiri ba sarakunan suka zira hannayensu a aljihun rigar su sai ga shi kowannen su ya fito da ɓarin kubarshi, fuskokinsu cike da murmushin mugunta suka haɗa su a waje guda, faruwar hakan ke da wuya sai aka kwantsama wata tsawa da walƙiya a sararin samaniya, kubar ta kammala jikinta baki ɗaya.
Fuska a murtuke babu annuri sarki Fitinatul-muluk ya miƙawa abbana kubar ya sa hannu ya ƙarba, sannan ya dube shi fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce "ya kai Yasiran kayi sani cewa wannan kuba ta Miftahul-sihir da muka baka da ita ne zaka buɗe kofar wannan kogon dutse har ka samu nasara ɗauko KUNDIN AL'AJABI daga cikin shi".
Koda jin wannan daga bakin Fitinatul-muluk sai mahaifina ya yi jim! Tamkar mai tunanin wani abu, koda ganin halin da mahaifina ya shiga sai sarakunan suka bayyanar da murmushi akan fuskokinsu, da ganin hakan sai abbana ya ji ya samu nutsuwa kawai sai ya juya ya durfafi ƙofar kogon GARUL-SHAMMAR yana isa ya sanya kubar a cikin wani kwaroron rami da ke jikin makekiyar ƙofar kogon da aka yi ta da zallar mulmulallan baƙin ƙarfe, ya murɗa kubar sau huɗu da dukkan ƙarfin shi, take sakatun suka shiga ƙara, zuwa can sai ƙofar ta yi wani ƙara da ya cika dajin baki ɗaya, sannan ta buɗe kanta, wani irin tururin hayaƙi ya surnano daga ciki, ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, mahaifina ya kunna kai izuwa cikin kogon tare da sanya kubar Miftahul-sihir a cikin aljihunshi, lokacin da ya kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!.
Daga ciki kogon GARUL-SHAMMAR ya kasance makeke mai matuƙar tsawo da faɗi, yana ɗauke da saƙarƙaƙiya da lunguna, gaba ɗaya gine ginen dake ciki an yi su ne da waɗansu manyan duwatsun wuta masu ƙwarin gaske, gaba ɗaya kogon dutsen a haskake ta yadda koda allura ce ta faɗi a ƙasa da ya duba zai gani, kuma a ƙasa a zube akwai kwarangwal ɗin bil'adama da wasu halittu gasu nan birjik.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, inda a ce abbana ya san abin da zai faru da bai ya gangancin kutsawa kai cikin kogon ba, domin abin da bai sani ba shine, waɗannan kwarangwal ɗin sun kasance tarin miyagun aljanu.
Lokacin da ya zamana ya iso tsakiyar kwarangwal ɗin, nan take ruhikansu suka fara dawo jikkunansu kuma surar tana haɗuwa, kafin cikar daƙiƙa hamsin baki ɗaya halittun sun miƙe tsaye.
Aljanun sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawan farko, jikkunansu irin na bil'adama ne amma kawunansu irin na tsuntsun batoyi ne, idanuwansu jajur suke tamkar garwashin wuta, a ƙugunsu suna maƙale da wata murtukekiyar jela irin ta kada, sannan dukkanin suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro, a hannayensu suna ɗauke da waɗansu irin makaman yaƙi masu kama da zarto.
Haƙiƙa Waɗannan aljanu sun kasance ababan tsoro da razani ga duk wata halitta mai numfashi.
Lokacin da mahaifina ya yi arba da halittun sai jikinshi ya kama tsuma yana kyarma saboda matuƙar tsoro, amma sai ya yi wuf! Ya zare takobinshi aka fara kallon-kallo tsakani, tsawon daƙiƙa arba'in ɗayan su bai yunƙurin afkawa abokin gwamin shi ba.
A lokaci guda tamkar haɗin baki dakarun suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan Yasiran suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, tare da kai mashi miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Take mahaifina ya tare su aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a lokacin da dakarun suka yanyame shi tamkar yadda dandazon ƙudaje ke yanyame ƙwallon mangwaro.
Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka saba gwagwarmaya a filin fama, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihu da hargowar dakarun aljanun ta cika kogon baki ɗaya, kuma kogon ya ɗauki zafi ainun, tamkar zai yi bindiga ya tarwatse, sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari uku ana wannan ɗauki ba daɗi.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa aljanun kai kenan kuma ya ba su mamaki, domin fiye da shekaru dubu biyu suna gadin wannan kogon na GARUL-SHAMMAR ba su taɓa ganin halitta mai matuƙar zafin nama da ƙwarewar yaƙi tamkar na mahaifina ba.
Al'amarin mahaifina kuwa lokacin da ya fahimci cewa babu alamun nasara, kuma koda alamun gajiya babu a tare da dakarun sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita, koda samun mafitar sai kawai ya mayar ta takobinshi izuwa cikin kube, ya yi wuf ya zaro kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan dakarun da ita da dukkan ƙarfin shi.
Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa abbana ya gano lagon tsuntsayen ya zamana cewa duk wanda ya daka da kubar sai kaga ya kurma wawan ihu ya tarwatse, nan fa ihu da kururuwar shaiɗanu ta ƙara cika kogon, kafin shuɗewar rabin sa'a, nan fa dakarun suka ɗimauce suka kama guye-guje da ifice-ifice, wasu suka shiga ƙoƙarin ƙwace kubar Miftahul-sihir daga hannun abbana, wasu na kai mashi sara da suka cikin matuƙar zafin nama, domin ganin sun kai shi ƙas.
Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin aljanun ya shammaci mahaifina ya kafta mashi sara a cinya, take inda ya yanke shin ya dare jini ya yi tsartuwa, abbana ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA sai ya ci gaba da yaƙin a haka ba tare tsaida zubar jinin ba, haka ya ci gaba da yaƙin jiri na ɗibar shi a wasu lokutan har yanke jiki yake ya faɗi ƙasa amma sai ya miƙe tsaye zumbur ya ci gaba da yaƙin a haka.
Kaico! Haƙiƙa jarumtaka baiwa ce daga Ubangiji, dukiya, mulki basu bayar da ita face baiwa daga Allah, komai hassadar mutum idan ya ga yadda mahaifina ke ragargazar dakarun cikin baƙin zafin nama da kafin tsiya, dole ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya cika gwarzon mayaƙi mai ƙarfi na Allah ya isa.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA YAFI SARKIN ƘARFI qna cikin wannan artabu ne mayaƙan suka samu nasarar kai abbana ƙasa suna niyyar hallaka shi, koda ya ga irin mawuyacin halin da yake ciki da yake tsakanin RAYUWA DA MUTUWA, bai san sa'adda ya buga kubar Miftahul-sihir a ƙasa ba, faruwar hakan keda wuya nan take wani farin haske ya yi fitar burgu daga kubar, ya shiga sassan jikkunan sauran aljanun, nan take suka kama ci da wuta suna ihu da kururuwa neman taimako, kafin wani lokaci mai tsawo baki ɗayan su sun sheƙa barzahu.
Cikin matuƙar farin ciki abbana ya miƙe tsaye da ƙyar ya sake kunna kai izuwa cikin kogon,
Tsawon daƙiƙa ɗari huɗu yana tafiya sannu-sannu,
lokacin da rabin sa'a ta shuɗe a dai-dai lokacinne ya ya iso wani waje mai tsananin sanyi, hatta durakun dake wajen na dusar ƙanƙara ne, babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafarshi face dusar ƙanƙara ce.
Sa'adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin wannan hali sai hankalinshi ya dugunzuma ainun, domin baya sanye ɗauke da rigar kariya daga sanyin.
Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya kama mahaifina jikinshi ya kama ƙyarma, tun yana iya takawa da ƙafafuwanshi har ya zamana ya zube a ƙasa magashiyan nunfashin shi na fita daƙyar.
Yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai wani irin ƙatuwar halitta tayo fitar burgu daga dusar ƙanƙarar ta fito waje, Ita dai halittar takasance wata shirgegiyar macijiya mai kauri tamkar bishiyar kuka, jelar murtukekiya ce, bayan ƙaton kanta tana ɗauke da ƙarin wasu guda biyu, na farko yakasance na zaki, ɗayan kuma na raƙumin dawa.
Kaico! Wannan halitta ta kasance mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, babu wani jarumi da zai yi arba da ita face ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa.
Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na bakwai
Domin jin wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
❤️
👍
5