
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 15, 2025 at 10:24 PM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
GWARAZAN JIYA
KUNDIN AL'AJABI
Following 👉
https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
Babi na bakwai
A can bakin ƙofar shiga kogon GARUL-SHAMMAR sarakunan duniya huɗu suna tsaitsaye suna jiran fitowar mahaifina fuskokinsu a murtuke babu annuri cike da matuƙar kiyayyar juna.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai suka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar DARE UKU ne ya haɗu waje guda mutum koda tafin hannunshi baya iya gani.
Sannu a hankali duhun dake sararin samaniya ya fara raguwa, sai ga waɗansu halittu masu tarin yawa suna ketowa daga cikin gajimare suna sauka a kan tekun Bahar-rum.
Koda ganin hakan sai sarki Fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka yi wuf suka fito da maduban tsafin su suka shiga gudanar da bincike, koda kammala binciken sai suka taƙarƙare suka bushe da dariyar mugunta, ba komai suka gani ba face halittun da suka bayyana sun kasance rundunar sarakunan duniya biyu, sarkin aljanu baƙaƙen fata da farare.
Sun turo tawagar ne domin su ƙwaci KUNDIN AL'AJABI da kubar Miftahul-sihir da zarar mahaifina ya samu nasarar ɗaukowa.
Sarki Hubaizu na birnin Hindu ya katse shirun da ya wanzu a q hanyar duban sauran 'yan uwanshi fuskarshi a murtuke babu annuri ya ce "yaku manyan abokan gaba a gare ni ku yi sani cewa waɗancan dakarun aljanu da suka bayyana ba su ba ne face Tawagar sarakunan aljanu da suka zo domin ɗaukar kubar Miftahul-sihir haɗe da KUNDIN AL'AJABI, saboda haka yanzu dole mu haɗa kai mu kawar da waɗannan sabbin abokan gaba, idan ya so daga baya kuma sai a raba rai tsakanin mu ga wanda zai zamo zakara a, da zai zamo mamallakin KUNDIN AL'AJABI".
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Hubaizu na birnin Hindu sai sauran sarakunan uku suka zare makaman yaƙin su suka yi ɗauki kan dakarun aljanun, koda ganin hakan sai aljanun suka tare su suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
***
A cikin kogon GARUL-SHAMMAR kuwa kafin mahaifina ya yi wani yunƙuri wannan macijiya ta kafta masa sara a hannayenshi da ƙafafuwanshi, nan take nunfashin shi ya fara sarƙewa kuma ya faɗi ƙasa magashiyan".
Lokacin da kyakkyawar baƙuwar jaruma ta zo dai-dai nan a labarin da take bamu sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta.
Al'amarin da ya sanya jikinmu ya yi sanyi ni da Raudat har ƙwalla ta zubo mana.
Cikin alamun matuƙar tausayi na dubi jarumar na ce "haƙiƙa labarin mahaifinki cike yake da abun tausayi darasi da abubuwan al'ajabi. Kuma ya cancanta ki ɗauki ko wane mataki domin daukarwa mahaifinki fansa, duk da cewar ba mu ji ƙarshen abin da ya faru tsakanin abban ki da manyan sarakunan duniya huɗu ba, duk da cewar da farko mun nufi mu yaƙe ki, amma a halin na ji a raina ni da abokiyar tafiyata za mu taimaka miki ki cimma wannan buri na ki. Amma bisa sharaɗin cewa ba za ki cutar da wani mahaluki ba idan har kin samu nasarar mallakar makaman yaƙin sarkin bokayen duniya".
Sa'adda na zo nan azance na sai fuskar baƙuwar jarumar ta faɗaɗa da murmushi mai taushi, ta dube mu sannan ta yi gyaran murya ta ce "ya ku waɗannan jarumai haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki da wannan taimako da za ku ba ni, kuma ina mai tabbatar maku da cewa ba za ku same ni da wani abu na cin amana ko yaudara ba.
Kuma a halin yanzu ba zan iya ci gaba da ba ku labarin mahaifina ba sai dai anan gaba, sai dai ban sanar da ku suna na, mahaifna na kira da suna Sulairat bintu Yasiran".
Sa'adda Sulairat yar mafarauci Yasiran ta zo dai-dai nan azancen ta sai na yafito aljani Jauharul-layal dake tsaye a gefe guda da hannu da ya iso inda muke, taku ɗaya kacal ya yi ya iso gare mu ba tare da wani jinkiri ba Raudat, Sulairat suka haye gadon bayan shi, take na yi koyi da su ina mai zama da daf da inda suke yazamana tazarar dake tsakaninmu bata huce kamu ɗaya ba,
A halin yanzu tafiya ta sauya salo daga mutum biyu izuwa uku, wato ni Raudatul-abyad sai jaruma Sulairat.
Sai da muka shafe tsawon sa'a huɗu muna keta gajimare cikin matsanan gudu na keta sa'a, ɗa ya daga cikin mu bai ce uffan ba, a wannan lokaci ne Raudatul-abyad ta lura da cewa Sulairat na satar kallo na lokaci zuwa lokaci, koda ganin hakan sai ta daka mata wata harara dake nuna tsantsar kishi da soyayya.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai mu ka ga aljani Jauharul-layal ya tsaya cak! A sararin samaniya, cikin fushi Raudatul-abyad ta dube shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "ya kai Jauharul-layal shin ina dalilin wannan tsayuwa ta ka bayan ka san cewa muna so mu isa fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar cikin sauri ?
Koda jin wannan tambaya sai Jauharul-layal ya risina cikin ladabi ya ce "ki gafarce ni ya shugabata bakomai ne ya sanya na dakatar da tafiya ba face bisa jiyo ƙanshin 'yan uwana aljanu a daf da mu, hakan ya tabbatar min da cewa akwai waɗanda ke biye da mu…"
Karfin jauharu ya gama rufe bakinshi kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ga tawagar waɗansu zaratan aljanu kimanin dubu hamsin, sun bayyana a suna masu yi mana ƙawanya, su dai aljanun sun kasance bakaƙe wuluk, masu girma, kwarjini da munin gaske, fuka-fukansu irin na mikiya ne, a gadon bayansu suna ɗauke da wani ƙusumbi da ya tamkar duwatsu aka saka masu, duk sa'adda da suka buɗe bakunan sai wani ruwa mai yauƙi mai warin gaske ya zubo. Baki ɗayan su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, kuma girman kowannen su ya ninka na aljani Jauharul-layal sau goma.
Wohoho! Haƙiƙa waɗannan tawagar ifritai ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, nan fa muka zo tamkar an ajiye kyanwa a gaban garken raƙuma.
Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na 8
Domin jin wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
❤️
👍
4