
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 17, 2025 at 11:33 AM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
GWARAZAN JIYA
KUNDIN AL'AJABI
Following 👉
https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
BABI NA TAKWAS
Lokacin da boka Matawus yazo dai-dai nan a hikayar da yake bawa sarki Sabrul-marhut sai ya ja dogon goron numfashi sannan ya ɗora da cewa.
Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakanin mu na tsawon daƙiƙa arba'in sai daga bisani ne shugaban tawagar ifritan aljanun ya ratso ta tsakiyar ya matso daf da mu ya dube mu da turɓunanniyar fuskarshi da ninka ta sauran muni, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya ce "ya ke Raudatul-abyad tare da tawagarki kiyi sani cewa yau tsawon shekaru dubu da ɗoriya ina jiran zuwan wannan rana da zan karɓi taswirar fadar sarkin bokaye daga hannunki, tsawon shekaru ina bibiyar mahaifinki domin ya mallaki taswirar amma saboda sirrin dake tare shi ban samu wannan dama ba sai a yanzu".
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban tawagar sai Raudat ta tari numfashinshi tana mai daka masa tsawa ta ce "ya kai wannan rafkananne kuma tsohon AZZALUMI ka yi sani ce wa, ire-iren ka ba za su taɓa cimma buƙatar su domin mallakar wannan taswira ba, domin shimfiɗa BAƘIN ZALUNCI, shawara ɗaya zan baka ita ce ka janye waɗannan 'yan tsakin mayaƙan na ka, idan kuwa ba haka ba zaka yabawa aya zaƙinta…".
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-abyad sai shugaban tawagar ya fusata ainun jikinshi ya kama tsuma ya ƙyarma tamkar mazari, idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur, ya buɗi baki a karo na biyu cikin matuƙar fushi har wani irin tururin baƙin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinshi, baki da kunnuwa ya ce " kaicon ki yake wannan ƙaramar ƙwaruwa haƙiƙa kin tafka babban kuskure, wanda ba zan iya yafe miki ba face na shayar dake gidauniyar azabata da dukkanin abokan tafiyar ki, sai dai kafin hakan akwai buƙatar na sanar dake wane ne ni, da farko dai suna na ifritu Sulsainil-auman ibn Turbus, shugaban ifritan aljanun duniya baƙaƙen fata. Da wannan nake yi miki bankwana ga maza nan bisa kan ki".
Koda shugaban ifritai Sulsaini ya zo nan a zancen shi sai ya yi ihu da kururuwa mai firgita GWARAZAN JIYA a FAGEN FAMA ya afka Raudatul-abyad, take sauran yaran shi suka afka mana ni da Sulairat da Jauharul-layal.
A can ƙololuwar sararin samaniya inda Allah (SWT) ya yiwa dukkan halittu iyaka kuwa, anan ne uwar mayu Ummul-sharri ta kafa fadarta domin gudanar da ƙasaitaccen mulkinta,
A wannan lokaci Ummul-sharri tana zaune a bisa karagar mulki a cikin gawurtacciyar fadarta, Ita dai fadar ta ƙasaitacciya tamkar gari guda, gaba ɗaya ginin fadar an yi shi ne da zallar waɗansu irin duwatsu masu ƙwari gaske suna sheƙi da ƙyalli tamkar gilashi, duk inda mutum zai ajiye ƙafarshi wani irin koren gilashi ne mai kama da darduma, idan mutum ya kalla yana iya ganin surarshi, gefe guda kuwa 'yan majalisa na jinsin mutum da aljan na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma, a kowa ce kusurwa a fadar dakarun tsaro ne na jinsin mutum da aljan ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikakken tsaro, a bisa wata matattakala mai hawa goma anan aka ajiye karagar mulki da aka yi ta da sallar jauhari, kai tsayawa masalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce hankali, kai wani abun ma ko jin sunan shi bai taɓa yi ba, kana gani ka san aiki ne na sihiri.
Shiru ne ya mamaye wajen tamkar mutuwa ta kawo ziyara, uwar mayu Ummul-sharri ce ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar sanya hannunta a aljihun rigarta ta ɗauko madubin tsafinta da girmanshi bai zarce faɗin tafin hannuna ba, ta shafe da hannunta na hagu gami da runtse idanuwanta ta karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama furtawa sai ga taswirar gumurzun dake wanzu tsakanin tawagar ifritu Sulsainil-auman da su jarumai Raudatul-abyad ya bayyana a kan madubin.
Koda ganin hakan sai uwar mayu ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, mai kama da haniniyar dawakai, sautin ta ya mamaye fadar baki ɗaya, al'amarin da ya firgita wasu daga cikin jama'ar fadar kenan cikinsu ya ɗuru ruwa, domin sun san cewa duk sa'adda uwar mayu tayi wannan dariya to za ta zartar da wani baƙin zalunci, tsawon daƙiƙa arba'in tana cikin wannan hali sai daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da WASIƘAR AJALI, kawai sai ya mayar da madubin izuwa ma'ajiyar shi, kana ta dawo da dubanta zuwa ga wani mummunan aljani daga cikin 'yan majalisarta, tamkar ya san abin da take nufi kawai sai ya miƙe tsaye ya matsa daf da karagar mulki ya zube ƙasa ya yi sujjada a gare ta, sannan daga bisani ya ɗago kanshi a ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "gani gare ki ya SARAUNIYA MAI DUNIYA, gajimare kike mai shayar da duniya mugunyar annoba.
Guguwar musiba mai share TAWAGAR ZARATA.
ina gagararre ko hatsabibi ya zo ga GAWURTACCIYA uwar matsafan dunya"
Kin ci dubu sai ceto kin yi KARO DA DUBU kalacen safe, ina mazan suke ne ga sa gudu maganin ƙi gudu"
ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya ja dake zai baƙunci barzahu".
Lokacin da ɗan majalisar ya zo nan a kirarin na shi sai uwar mayu ta yi murmushi mai kama da yaƙe da ya ƙara tona asirin munin fuskarta, bisa jin daɗin kirarin da yake yi mata.
Sannan ta buɗe tafkeken bakinta mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora baƙaƙe babu kyawun gani ta ce "an gaishe ka ya kai Darmanu maganin ƙananan ƙwari abin da nake so a gare ka shine ka tafi cikin hanzari izuwa gaɓar dajin Zarutul-shammar domin ka ƙwato min taswirar fadar sarkin bokaye a hannun jaruma Raudatul-abyad, ina mai farin cikin sanar da kai cewa burina ya kusa cika na shiga fadar sarkin bokaye domin na gaje komai nashi, sirrikan tsafi da kayan yaƙinshi, dole ne duniya ta zamto a tafin hannuna, na juya ta tamkar yadda ake sarrafa waina a tanda,
Wannan ita ce dama ta ƙarshe a gare mu domin shiga fadar sarkin bokaye don haka ina mai gargaɗarka ka kula sosai kar a samu kuskure a cikin wannan aiki”.
Sa’adda Uwar mayu Ummul-Sharri ta zo nan a jawabinta sai aljani Darmanu ya risina ya ce “an gama ya shugabata wannan aiki abu ne mai sauƙi a gare ni tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai”.
Ummul-Sharri ta ce “tsafi ya baka kariya ka dawo cikin aminci ya kai Darmanu”.
Koda gama faɗin hakan sai Darmanu ya risina ga uwar mayu sannan ya rikiɗa izuwa wani baƙin haske ya ɓace ɓat daga fadar tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
Wannan shi ne abin da ya wakana a fadar uwar mayu ta duniya matsafiya Ummul-Sharri.
Lokacin da muka kacame da azababban yaƙi tsakaninmu da shugaban ifritai Sulsaini da yaranshi sai muka wanzu muka kaiwa juna hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, ana fara wannan artabu ne dukkaninmu suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin matuƙar zafin nama gami da ƙarfin damtsen ifritan ya ninka namu sau biyar, babban abin da ya dugunzuma hankalinmu shine yadda duk sa'adda makaman yaƙinmu suka sari jikkunan ifritan sai mu ji tamkar dutse muka sara, ko gezau ba sa yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara ƙal! Ƙal!.
A duk sa’adda makaman yaƙinmu suka haɗu da juna sai ka ji an kwantsama wata tsawa gami da walƙiya, nan fa sararin samaniyar ya cika da ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu gami da hargowar MAZAJEN DUNIYA.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu da goma ana wannan ɗauki ba daɗi babu sassauci.
A cikin wannan artabu ne na fahimci Sulairat tafi mu ƙarfin damtse da salon dabarun yaƙi, domin a hankali yanzu tana iya samun nasarar yankan jikkunan ifritan, koda suka fahimci irin ɓarnar da Sulairat ke yi masu sai suka yanyame ta suna kai mata sara da suka gami da yakushi da faratansu.
A ɓangaren aljani Jauharul-layal kuwa ya wanzu yana kai FARMAKI da fuka-fukanshi, bakinshi gami da faratan hannunshi, cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Lokacin da shugaban ifritai Sulsaini ya ga cewa sa'a ɗaya ta shuɗe ana wannan baƙin artabu sai ya fusata ainun zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone, ya fahimci cewa wankin wula zai kai su dare, wani abu da ya fusata shi shine tun da yake yin GABA DA GABA da jarumai bai taɓa haɗuwa da bil’adama masu matuƙar zafin nama da ƙarfin damtse tamkar mu ba.
Lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi, sai ƙarfin damtsenmu ya fara raguwa yaran ifritu Sulsaini suka fara galabaitar da mu, faruwar hakan ke da wuya sai Aljani Sulsaini ya yi ƙara luhhh! Domin ya zillewa ifritan, amma sai hakan ya faskara domin kadoni ya kai ga hakan wani daga cikin ifritan me nacin tsiya ya kafta masa sara a kafaɗarshi, saboda matuƙar ƙarfin sara sai da Jauharul-layal ya kurma wawan ihu, saboda raɗaɗi da zugin da ya ji.
Sa’adda jaruma Sulairat taga halin da muke ciki, kuma ta fahimci cewa a koda yaushe ɗayanmu na iya raya rayuwar shi, sai kawai ta shiga amfani da ƙarfin shirin tsafi amma ya zamo a banza, domin da idan ta yi TSATSUBA ta turawa ifritan Kibbau na huta da zarar sun doshi inda suke sai suka zama farin haske su ɓace ɓat!
Ana cikin wannan wannan fafatawa ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya tayi duhu dunɗum! Tamkar DARE BIYU ne ya haɗu waje guda, kuma aka dinga kwantsama tsawa da walƙiya kai ka ce za’a kece da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya.
Daga can sai aka ga wata shirgegiyar halitta ta bayyana a sararin samaniya, halittar tana da matuƙar girma fiye da aljani Jauharul-layal, tana ɗauke da fuka-fukai goma a tsakiyar kanta tana ɗauke da wani zabgegen ƙaho mai kama da na rago, batun munin fuskarta kuwa sai abin da idanu suka gani kawai, a gadon bayanta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi. Kaico! Haƙiƙa wannan halitta ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Darmanu manzon uwar mayu Ummul-Sharri, wanda ta tura domin ya ɗauko mata taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar.
Sa’adda kowa ya yi arba da aljani Darmanu sai aka tsayar da yaƙi kallo ya koma kanshi.
Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo sai daga bisani aljani Darmanu ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da saukar aradu wacce ta ɗimauta duk wata halitta dake wajen hatta ifritu Sulsaini da yaranshi, a lokaci guda ya tsuke bakinshi ya fara magana cikin wata irin kakkausar murya mai kama haniniyar doki yana mai cewa
“Ya ku waɗannan ƙananan halittu ma’abota ƘARAR KWANA ku yi sani cewa ban zo nan domin kallon fafatawar da kuke yi ba, face sai domin ya karɓi taswirar fadar sarkin bokaye domin na kaiwa uwar matsafan duniya Ummul-Sharri, kira na a gare ku shine ku gaggauta miƙo min taswirar cikin ruwan sanyi domin na yi maku kisa mafi sauƙi ba tare da kun sha wahala ba, ta hanyar da daddatsa sassan jikkunanku.
Kafin Darmanu ya gama rufe bakinshi ifritu Sulsaini ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka masa tsawa ya ce “ ya kai wannan maƙetaci kuma wanda rarraunar zuciyarshi ke yaudarar sa ka ji sani cewa ka tafka babban kuskure, da kake tunanin za ka ƙwaci taswira daga hannun Jaruma Raudatul-abyad, bayan muna gab da mallakarta, wato kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi”.
Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Sulsaini sai aljani Darmanu ya fusata ainun, idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe, kawai sai ya miƙa hannunshi izuwa sama sai ga wata zabgegiyar takobi ta bayyana ta haske, take ya yi ɗauki izuwa kan Sulsaini da tawagarshi, ana haɗuwa aka yi KARON BATTA, nan fa aka garƙame da sabon gumurzu mai matuƙar muni ban tsoro gami da tashin hankali, a wannan karon sai artabun ya canja salo, domin a wannan karon duk inda aljani Darmanu ya sanya a gaba sai dai kaga yaran ifritu Sulsaini na sheƙawa barzahu, takobinshi na raba sassan jikkunansu.
Nan fa muka shiga raba idanu domin ba su san wane ɓangare zamu shigarwa yaƙin ba, tun da dukkanin su abokan gabarmu ne.
Muna cikin wannan hali ne wata dabara ta faɗo min, koda samun mafitar sai kawai na yiwa aljani Jauharul-layal inkiya ta wutsiyaar idanu, koda ya fahimci abin da nake nufi sai ya faki idanun TAWAGAR ABOKAN GABA ya kaɗa fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! ya keta cikin gajimare ya fara tsala azababban gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya muka ɓace ɓat! Har muka daina hango so.
Lokacin da muka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna gudun tsira da rayuka, sai ƙarfin gudun Jauharul-layal ya fara raguwa ainun saboda gumurzun da aka sha, domin hakan sai aka yanke shawarar mu yada zango domin mu huce gajiyar dake tattare da mu, cikin hanzari Jauharu ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! Ya sauka a turba, inda muka saukar ya kasance daji mai tattare da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu gami da sarƙaƙiya, muna sauka ne dukkaninmu kowa ya sha jinin jikinshi, domin da ganin dajin ba a rasa miyagun halittu masu cutarwa ba.
Da yake akwai inuwar bishiyu sai ya zamana cewa bamu kafa tanti ba, aka fito da abin kalaci kowa ya shiga kimtsa cikinshi.
A wannan lokaci ne jaruma Sulairat ta duba mu tayi gyaran murya sannan ta ce “tun da a halin yanzu dukkaninmun mun samu natsuwa zan cigaba da baku labarin abin da ya wakana da abbana tare da manyan sarakunan duniya uku, inda ta ɗora da hikayar kamar haka:-
Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na 8
Domin jin wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
❤️
👍
🙏
5