
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 18, 2025 at 07:28 AM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
GWARAZAN JIYA
KUNDIN AL'AJABI
Littafi Kuɗi ne
₦400
8137237071
Usman Umar Mansur
Opay
Following 👉
https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
BABI NA TARA
Sa’adda abbana ya yi arba da macijiyar sai jikinsa ya kama tsuma yana ƙyarma saboda matuƙar firgici, domin a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin halitta mai matuƙar kwarjini da muni tamkar macijiyar ba.
Kafin ya yi yunƙuri ta kafta masa sara a dukkan sassan jikinsa, ya faɗi ƙasa magashiyan yana mai aman jini ta baki da hanci, kuma wani zazzaɓi mai zafi ya kama sa yana ƙyarma tamkar zai sheƙa barzahu.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai macijiyar ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, dariyar ta ta ta haddasa wata irin gagarumar iska. A lokaci guda ta tsuke baki tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa, sannan ta buɗe bakinta dake maƙale a jikin kanta mai siffar gwaggwan biri cikin wata irin kakkausar murya ta dubi abbana ta ce “ya kai wannan bil’adama ka yi sani cewa haƙiƙa kai mutum mai matukar sa'a da rabo a rayuwarsa, domin kai ne mahaluki na farko da ya shigo wannan kogo fiye da shekaru dubu uku domin ɗaukar littafin KUNDIN AL'AJABI, sai dai ina farin cikin sanar da kai cewa kai ne bil’adama na ƙarshe da zai sake shigowa wannan waje, yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba zan rugurguza ƙasusuwanka ka yi mutuwar wulakanci”.
Koda tazo nan a zancenta sai ta sake bushewa da dariya a karo na biyu, kawai sai ta sanya jelarta ta kanannaɗe mahaifina ta ɗaga shi izuwa sama, sannan ta buɗe bakinta ɗaya ta jefa abbana ciki tayi loma ɗaya da shi ta rufe rufe! Tamkar ta haɗiye ƙwallon dabino.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu. In da ace wannan macijiya ta san abin da zai faru da bata haɗiye abbana ba, domin kuskuren da ta yi shine ta haɗiye shi tare da kubar Miftahul-sihir.
Sa’adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin macijiyar sai nan take ya ji dukkan zazzaɓin dake jikinshi ya rabu da shi, tamkar a cire silin gashi daga cikin tandun mai, kuma ya samu ƙwarin jikinshi, nan take wata hikima ta faɗo mashi ya ɗauki kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan sassan cikin macijiyar. Kaico! Nan fa macijiyar ta shiga mawuyacin hali domin duk sa’adda abbana ya daki wani ɓangare a jikinta sai ta ji tsananin azaba tamkar da wuta ake ƙona ta.
Nan fa ta shiga guje-guje da ifice-ifice a cikin kogon saboda matuƙar azabar da take sha, take ta shiga ƙaƙari ta amayo mahaifina daga cikinta ya faɗo ƙasa tim! Kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin jikin macijiyar ya sandare ya daina motsi, kuma wata ƙofa ta musamman ta bayyana a ƙarƙashinta, hatta tsananin sanyin dake kogon dutsen ya ɗauke.
Cikin matuƙar farin ciki mahaifina ya miƙe tsaye cikin ƙwarin gwiwa ya kunna kai izuwa cikin wannan ƙofa hannunshi ɗauke da kubar Miftahul-sihir.
A can gaɓar tekun Bahar-rum kuwa manyan sarakunan duniya haɗu da na aljanu gami da rundunoninsu sun wanzu suna bawa hammata iska. Nan fa manyan sarakunan huɗu, Abul-uyum, Ayumul-barƙas, fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka zamto tamkar GOBARAR DAJI a tsakiyar mayaƙan, duk inda ɗayan su ya sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa tamkar ana sassabe a gonar auduga, sun haddasa fili fetal.
Nan fa gagarumar walima ta ɓarke a tsakanin halittun dake ƙarƙashin tekun, suka shiga watanda da sassan jikkunan dakarun.
Babu abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure mashi kai face yadda gwarazan sarakunan huɗu ke fafatawa tamkar jikkunnansu ba su kasance na jini da tsoka ba.
A ɓangaren sarakunan aljanu kuwa, koda suka ga irin ɓarnar da su sarki Ayumul-barƙas ke yi masu sai suka fusata ainun, kuma suka faɗa izuwa kogin tunani, abu na farko da ya faɗo masu a rai shine matuƙar basu canja salon yaƙin su ba, ba za su samu nasarar kawar da su Ayumul-barƙas, sannan ma inda kizo ke saƙar shine idan sun yi nasarar ta ya ya ɗayansu zai iya haƙura ɗan uwansa ya mallaki KUNDIN AL'AJABI tare da kubar Miftahul-sihir, daga can sai wata dabarar ta faɗo masu, dabarar kuwa ita ce su yaƙi junan su, idan ɗaya daga cikin su ya yi nasara sai ya shiga kogon Garul-shammar ya hallaka mahaifina, ya mallaki KUNDIN AL'AJABI da kubar Miftahul-sihir.
Koda gama tunanin hakan sai sarkin aljanu baƙaƙen fata ya ɗaga hannunshi izuwa sama, sai ga wani makami mai kama da zarto mai tsini da kaifi tamkar takobi ya bayyana gare shi, koda ganin hakan sai sarkin aljanu fararen fata ya zare wani makami na sihiri a jikinshi mai kama da Adda mai KAIFI DA TSINI.
A lokaci guda tamkar haɗin baki suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan juna suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, suna haɗuwa suka rungumtsume da azababben yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, duk sa’adda makamansu suka haɗu da juna sai a kwatsama wata irin razananniyar ƙara gami da tsawa, tamkar za’a kece da matsanancin ruwan sama.
Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce. “Idan ana babbakar Giwa wa yake jin ƙaurin ɓera” kuma tabbas “Sawun Giwa ya take na raƙumi”.
Sa’adda waɗannan GWARAZAN SARAKAI biyu suka fara bawa hammata iska sai suka tashi hankalin duk wata halitta dake wajen, ba shiri dakarun dake daf! Da inda suke fafata artabun suka dinga yin ƙaura domin tsira da rayukansu daga sharrin shuwagabannin na su.
Al’amarin mahaifina kuwa lokacin da ya shiga cikin wannan ƙofa dake ƙarƙashin wannan macijiya mai kawuna uku, sai kwatsam ya tsinci kanshi a cikin wani makeken waje mai ɗauke da manyan duwatsu, bishiyu gami da sarƙaƙiyar duhuwa, haka abbana ya ci gaba da tafiya a cikin wannan duhuwa har ya zamana ya shafe tsawon daƙiƙa ɗari uku, a dai-dai wannan lokaci ne kishi da yunwa suka addabi mahaifina, kuma dama ga shi ya jefar da jakar guzurin shi tun a wajen da ya fafata yaƙi da wannan macijiya.
Yana cikin wannan hali ne ya hango wata bishiyar tuffa can nesa kaɗan da inda yake, cikin matuƙar farin ciki ya durfafi inda take, yana isa ya sanya hannunshi ya tsinki guda ɗaya ya kai bakinshi da nufin ya ci. Kawai sai ya ji an daka mashi tsawa, wacce ta sanya hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi. Abbana ya waiga gabas, yamma, kudu da arewa bai ga kowa ba.
Al’amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan, kawai sai ya sake kai tuffar bakinshi karo na biyu domin ya ci, amma sai aka sake daka mashi tsawa, a wannan karon sai da firgita ya jefar da tuffar dake hannunshi.
Kwatsam! Sai ga wata BAƘAR INUWA na ketowa daga cikin gajimare, lokacin da ta kammala sauka sai ta rikiɗa izuwa wani zabgegen maridi.
Maridin ya kasance narkeke tamkar basamude yana da tafkeken kai irin na bil’adama, mai ɗauke da ido guda ɗaya jal! A tsakiyar goshinshi, ƙofofin hancinshi manya ne tamkar mazirari, yana makeken baki tamkar mazirari, ƙirjinshi makeke ne ya tara ƙwanji tamkar duwatsu aka cusa mashi a ciki, sangalalon hannayenshi da ƙafafuwanshi masu kauri ne tamkar bishiyar kuka, Kuma yana sanye cikin gagarumar shigar shigar yaƙi ta baƙin sulke mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a gadon bayanshi yana rataye da waɗansu zaratan adduna biyu masu kaifin tsiya.
Kaico! Haƙiƙa wannan maridi ya cika GAGARABADAU, komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da shi, dole ne ya ɗimauce ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa.
Sa'adda mahaifina ya yi arba da maridin, nan take ya ɗimauce jikinshi ya kama tsuma ya ja da baya.
Maridin ya tako lafta-laftan ƙafafuwanshi ya durfafi inda mahaifina yake, duk sa’adda da ya ajiye ƙafarshi ɗaya idan akan dutse ne sai kaga ya nutse izuwa cikin ƙarƙashin ƙasa, ya yin da ya rage saura taku biyar tsakaninsu sai ya ja ya tsaya ya ƙarewa mahaifina kallo tun daga ƙasa har sama, nan take mahaifina ya zamto tamkar an ajiye ƙyanwa a gaban raƙumi, saboda matuƙar tsawon maridin.
Daga can sai maridin ya wangame bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da gurnanin zaki ya dubi mahaifina ya ce “ya kai Yasiran ka yi sani cewa fiye da shekaru dubu uku a cikin halarar tsafina na gano cewa kai ne bil’adama mau tsananin sa'a da zai iya shiga cikin kogon dutse na Garul-shammar kuma har ya samu nasarar ɗauko littafin KUNDIN AL'AJABI. Bisa wannan dalili ne ya sanya na yi GABA DA GABA da kai domin na canja wannan ƙaddara taka, saboda haka yanzu ina so ka miƙo min kubar Miftahul-sihir, cikin ruwan sanyi domin na yi maka kisa mafi sauƙi, ta hanyar tsinka gaɓoɓin jikinka, ba tare da ka sha wata azaba ba”;
Koda jin wannan batu sai mahaifina ya bushe da dariyar ƙarfin hali, sannan daga bisani ya haɗe rai ya dubi maridin ya ce “ya kai wannan rafkanannan halitta ka yi sani cewa GWARZON DUNIYA ba ya taɓa gudu a filin fama, ballantana ya miƙa wuya ga abokin gaba, face ya yi GWAGWARMAYA domin ya yi MUTAWAR JARUMTA”.
Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai maridin ya fusata ainun, jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma, idanuwanshi na fitar da wani tiririn baƙin hayaƙi.
Kawai sai ya yi wuri! Ya zare waɗansu zaratan Adduna biyu a gadon bayanshi ya kaiwa mahaifina wani bahagon sara da nufin tsinke mashi wuya, cikin baƙin zafin nama ya wurƙila ya zamewa harin, sannan ya afkawa mahaifina suka rugumtsume da azababben yaƙi mai matuƙar kwarjini, muni da ban tsoro.
Duk sa’adda maridin ya kai mashi hari idan ya goce, duk abin da ya sara koda dutse ne sai kaga ya yi bindiga ya tarwatse, amma sai ya zamana cewa maridin ya ƙi yarda kubar Miftahul-sihir ta taɓa jikinshi.
Sai da daƙiƙa ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin GWARAZAN JARUMAN biyu, tamkar jikkunnansu ba su kasance na jini da tsoka ba, lokacin da sa’a biyu ta shuɗe nan take sai ya zamana cewa abbana ya fara galabaita saboda ƙishi da yunwa da suka adda be shi.
Koda maridin ya fahimci halin da mahaifina ya shiga sai kawai ya shammace shi ya gabza mashi naushi a fuska, saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da abbana ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya, sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim! Da rubda ciki a matuƙar galabaice yana aman jini ta baki da hanci, amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta GAGARABADAU sai ya ƙi yarda ya saki kumar Miftahul-sihir daga hannunshi”.
Sa’adda jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran yazo nan a labarin ta sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta zuwa kan kuncinta.
Al’amarin da ya sanya ni da Raudatul-abyad da sauran tawagarmu muka kamu da matuƙar tausayinta kenan har ƙwalla ta cika mana idanu.
Daga can sai Sulaiza ta share hawayenta sannan ta ci-gaba da cewa.
“Tabbas mahaifina ya sha matuƙar wahala a cikin kogon Garul-shammar kafin ya ɗauko littafin KUNDIN AL'AJABI, wanda har ta kai cewa ya rasa dukkan idanuwanshi. Bayan ya fito ne sai yaƙi ya ɓarke tsakanin sarakunan shida, da zarar wannan ya ƙwaci kundi da kuba, sai wancan ya yi mashi fin ƙarfi ya ƙwace.
Koda aljani Zaruhul-Amwat da ya ɗauko mahaifina da sarakuna huɗu ya kawo su gaɓar kogon Garul-shammar ya ga halin da mahaifina ke ciki, kuma ya tabbatar da cewa zai iya rasa rayuwarshi sai tausayin shi ya kama shi, kawai sai ya ɗauke shi ya kawo shi izuwa bakin kubbarmu ya ajiye, sannan ya tashi izuwa sama yq ɓace ɓat! A cikin gajimare,
Tsananin iskar fuka-fukan aljani Zaruhul-Amwat ta sanya muka yi tsammanin harin sumame aka kawo mana, sai daga bisani muka lura cewa a she mahaifina aka ajiye a daf da mu.
Cikin matuƙar tashin hankali muka fito daga bukkar muka rugo izuwa gare shi, muka rungume shi, yana mai bamu labarin irin butulci da sarakunan duniya huɗu suka yi mashi. Bayan ya kammala bamu labarinne idanuwanshi suka ƙafe, jikinshi ya sandare komai ya daina motsi, alamar rai ya yi halin shi, baƙin cikin rasuwar abbana ya sanya mahaifiyata ta faɗi ƙasa matacce ko shurawa bata yi ba.
Nan fa na sake fashewa da sabon matsanancin kuka ina mai kiran sunayen mahaifana, ina mai jijjiga su ina cewa, ku tashi kar ku mutu ku barni, amma babu wanda ke saurare na ballantana ya kawo min ɗauki, har da muryata ta disashe, idanuwana suka yi jajur tamkar garwashi, bayan na haƙa ƙabari na binne mahaifana, kullum sai na tsugunna a gaban ƙaburburan iyayena ina kuka gami da karanto baitocin bege a gare su.
Haka rayuwata ta kasance cikin maraici da ƙunci, kullum sai ya fita farautar abin yin kalaci.
Daga wannan rana na sha alwashin ɗaukar fansa akan sarakunan duniya huɗu”;
Lokacin da jaruma Sulaiza ta zo nan a labarin ta sai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya daban tausayi.
Nan take dukkaninmu muka ƙara kamuwa da matuƙar tausayinta, hatta aljani Jauharul-layal da bai kasance bil’adama ba sai da ƙwalla ta zubo mashi saboda matuƙar tausayin Sulaiza.
Mu haɗu a KUNDIN AL'AJABI babi na 10 last Free Page
Domin jin wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
👍
❤️
😮
4