
SUFI NOVELS OFFICIAL CHANNEL
February 19, 2025 at 10:25 AM
KUNDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp Number
08137237071
Following 👉🏽 https://whatsapp.com/channel/0029ValIxY3D8SDvGZsppD3s
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
KUNDIN AL'AJABI
GWARAZAN JIYA
BABI NA GOMA
Lokacin da boka Matawus ya zo nan a labarin shi, sai ya ɗago kai ya dubi sarki Sabrul-marhut, nan take ya ga ƙwalla na zuba daga idanuwanshi, bakomai ne ya sanya shi hakan sai bisa mutuƙar tausayin jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran.
Matawus ya yi ajiyar zuciya sannan ya ja dogon gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce “ya kai Sabrul-marhut ka yi sani cewa “mun sha matuƙar wahala sosai a domin isa fadar Sarkin bokaye, wanda dukkanin mu babu wanda bai rasa wani sashi a jikinsa ba, kuma nine kaɗai na samu nasarar fitowa daga fadar sarki bokaye a raye bayan na samu nasarar tone shirin tsafin da aka yiwa mahaifinmu na tawo da shi, domin na koma zuwa birninmu, na yi kukan baƙin ciki bisa mutuwar Raudatul-Abyad tare da jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran, bayan na samu nasarar kama hanya domin komawa zuwa gida, na ci karo da sauran ‘yan uwana in da suka yi min abin nan da masu iya magana ke cewa kura da shan bugu gardi da ƙawace kuɗi, suka yaudare ta hanyar bayyana min nadamar su akan ƙiyayyar da suke yi min, tare da alƙawarin cewa za su goya min baya na haye bisa karagar mulki, amma sai suka soka min takobi a gadon bayana suka jefar da ni ƙasa a tunanin su na mutu. Mahaifinka Maigirma Marhut shine ya ɗauke ni a wannan hali a lokacin da ya fitowa farautar ƙarshen shekara da ya saba yi, ya ceto rauwata, ya yi jinyar raunin dake jikina har na warke sumul, har na samu nasarar komawa izuwa birninmu, amma abin mamaki koda na isa sai na tarar dukkanin ‘yan uwana sun rasa rayukansu, domin ashe yaƙi ya kaure a tsakanin su domin hawa karagar mulki, amma abin da ya bani farin ciki shine mahaifinmu ya samu lafiya, kowa ya yi farin ciki da dawowa ta bayan an cire rai cewa bana raye, ‘yan majalisar sarki suka sake naɗani sabon sarkin Romaniya.
Ya kai Sabrul-marhut ka yi sani cewa wannan abun alheri da mahaifinka ya yi min ban manta da shi, dare da rana ina binciken hanyar da zan saka masa da abin da ya yi min sai a halin yanzu.
Ya kai Sabrul-marhut ina so ka kwantar da hankalinka, ka sani cewa za ka samu magaji da zai zamo halifanka, sai dai ina so ka saurari jawabin da zan yi maka, a halin yanzu uwar gidanka na ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni takwas, ba tare da ita kanta ta sani ba, ni ne wanda ya ɓoye junan biyun ta hanyar shiri domin kawar da idanu da bakin maƙiya daga sharrin matarka, junan biyun ba zai bayyana gare ta ba sai a daren da naƙuda zata kama ta, ina so da zarar ta haife abin da ke cikinta ka ɗauke sa ka sanya sa a cikin akwatin baƙin ƙarfe tare da TAKOBIN SARAUTA daka gada a wajen mahaifinka. Ka ɗora su abisa kenan doki a can bayan gari ka tafi ka barsu, abin da aka haifa maka zai dawo gare ka cikin aminci a lokacin da dukkanin maƙiyanka na ɓoye da fili za su bayyana. Sai dai zan gargaɗe ka koda ita matarka kar ka kuskura ka sanar da ita wannan sirri, ballantana waninta”.
Sa’adda boka Matawus ya zo dai-dai nan a zancen sa sai sarki Sabrul-marhut ya cika da ɗumbin al’ajabi gami da farin ciki, bai sa’adda ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Matawus ba.
Koda ya tashi tsaye ya buɗe ba ki da nufin ya ce wani abu, sai ya ga boka Matawus ya zama wani koren haske ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Take dukkan dakaru da barorin gidan sarautar da suka kamu da barci suka wartsake.
Nan fa sarki Sabrul-marhut ya sake cika da matuƙar mamaki, yana ta juya wannan hikaya da umarni da boka Matawus ya yi masa, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya wanzu yana kai komo a cikin turakarsa, a haka har a alfijir ya keto.
Kamar yadda boka Matawus ya labartawa sarki Sabrul-marhut haka al’amarin ya kasance. Kwanaki na bin kwanaki mako bayan mako, wata ranar asabar lokacin sulusainin dare naƙuda ta kama uwar gidan sarki wato gimbiya Nadirat, al’amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin Nadirat kenan, ta yi zaton ko cutar ajali ce ta zo mata, domin ta san bata ɗauke da wani abu da nuna cewa tana ɗauke da juna biyu, a wannan lokaci dukkanin kudancin dake turakar a ɗimauce suke, tamkar a ce ƙyat! Su cika wandon su da iska. Kwatsam! Sai sarki Sabrul-marhut ya kunno kai cikin turakar, cikin matuƙar tashin hankali ya durfafi inda take, lokacin da kuyangin suka ja da baya suka zube ƙasa gami da kwasar gaisuwa.
Sarki ya daf da ita bisa ƙasaitaccen gadon sarautar, sannan ya sanya hannunsa ɗaya a tallabo kanta, ɗayan hannun kuma yana shafa gashin kanta, cikin lallausar murya sai ɗauke raɗaɗin ciwo ga masoya ya ce “kwantar da hankalinka ya abar bege na dare da rana, kuma uwar ‘ya’yana ki yi sani cewa a halin yanzu za ki haife abin da ke cikinki, wanda ke kan ki ba ku san cewa kina ɗauke da shi ba, boka Matawus ya bayyana min cewa ya ɓoye wannan juna biyu na ki ne domin kawar da idanun maƙiya.
Mu haɗu a book 2 na kuɗi ne domin jin cigaban wannan kayataccen littafi.
Za a biya kuɗin littafin ta wannan hanyar
₦400
Account Number: 0084279025
Account Name: USMAN UMAR MANSUR
Bank: Access Bank Nigeria
Sai a tura shaidar biya ta wannan number
08137237071
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
08137237071
❤️
👍
🙏
5