HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
February 14, 2025 at 01:17 PM
KADA KA ZAMTO SILAR SANYA WANI YIN KUKA. - "Kayi iyakar bakin ƙoƙarinka wajen ganin ka kyautatawa bayin Allah, amma kada ka yadda bayin Allah suyi kuka ta dalilinka. imma ta hanyar ƙuntata musu don kana kan karagar mulki, ko kuma ta hanyar danne musu haƙƙi, ko tsaurara musu ta fuskar kasuwanci, haƙiƙa Allah yana kallon dukkanin abin da bayinsa suke aikatawa a ban-ƙasa kuma wallahi da sannu zai yi hukunci a dukkanin abin da suke aikatawar a ranar ƙiyamah" - "A koda yaushe ka zamto mai yawan sanya mutane farin ciki da jefa sanyi a cikin zuƙatansu, kada ka zamto wanda mutane zasu dinga yin kuka dominka" - "Kodai ka kyautata mu'amalarka garesu, ko ka taimaka musu da abin hanunka, ko kuma ka kame daga cutar dasu, haƙiƙa hakan zai farantawa jama'ar da kake tarayya dasu" - WhatsApp channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i - Telegram channel https://t.me/hausaislamicpicturesquotes - Biyo Instagram ɗinmu https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6
🙏 1

Comments