
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
4.6K subscribers
About HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
Manzon Allah (SAW) Ya ce: "Duk wanda yayi nuni akan aikin alkhairi yana da lada kwatankwacin na wanda yayi aikin". Muslim TELEGRAM https://t.me/hausaislamicpicturesquotes INSTAGRAM https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6 FACEBOOK https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial_fre
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

𝗞𝗔𝗦𝗨𝗪𝗔𝗡𝗖𝗜 𝗠𝗔𝗜 𝗥𝗜𝗕𝗔. - "Kasuwanci mai riba shine kasuwancin da bawa ya ƙulla shi da ubangijinsa Allah, ta hanyar bauta masa, kamar yin sallah, karatun alƙur'ani mai girma, da yin sadaƙa, da dai sauran aiyukan ɗa'a ga Allah" - "Ƙulla kasuwanci da Allah ta'ala shine kasuwanci mafi riba da albarka acikinsa, kasuwanci wanda babu asara ko tasgaro acikinsa, wanda kuma shi sharaɗin ƙulla wannan kasuwancin da Allah buwayi, shine: karatun alƙur'ani, yin sallah, da kuma ciyarwa ko yin sadaƙa domin neman yardar Allah buwayi" - 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝘽𝙐𝙒𝘼𝙔𝙄 𝙔𝘼𝘾𝙀: - "إِنَّ ٱلَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَٰبَ ٱللَّهِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقْنَٰهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِجَٰرَةً لَّن تَبُورَ" "Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah kuma suka tsayar da sallah, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro" (al-faaTir 29) - Biyo Instagram ɗinmu https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5 - Telegram channel https://t.me/hausaislamicpicturesquotes

*ALLAH YANA DUBI GA ZUƘATA NE.* - "Kada ka taɓa yin tunanin cewa Allah yana kallon gangar jikinka ne domin yi maka hisabi akai, a'a yana yin dubi izuwa ga zuciyarka sannan sai yayi maka hisabi akai" - "Dukkanin wani aikin da ka aikata, to lallai shi Allah babu ruwansa da wannan aikin komai yawansa, shi dai zai duba zuciyarka ne yaga niyyarka da kuma ƙudrinka na zuci" - "Manzon Allah ﷺ, yace: haƙiƙa lallai Allah baya yin kallo izuwa ga gangar jikinku, ko ƙirar ku, (ko fuskokin ku), saidai kaɗai yana yin kallo ne izuwa ga zuƙatan ku" Sahih Muslim (2564) - "Lallai Allah baya yin dubi izuwa ga surar jikinku, ko dukiyoyinku, saidai kaɗai yana yin dubi ne izuwa ga zuƙatan ku da kuma aiyukan ku" Sahih Muslim (2564) - Telegram channel https://t.me/hausaislamicpicturesquotes - Biyo Instagram ɗinmu https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5

*MU YAWAITA SALATI A GARESHI SAW A DAREN JUMAA DA RANAR JUMA'A* Sheikh Uthaimin (Rh) Yace: "Ya Kai ɗan uwana ka yawaita yima Annabi salati sai imaninka ya ƙaru al'amuranka kuma suyi maka sauƙi". [رياض الصالحين ٥/٤٧٠] - WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i

RAKA'ATAL FAJRI. - "Lokaci ne da zaka bayyanarwa da ubangijinka Allah irin buƙatun da kake dasu a gareshi, ta hanyar gajarta baccinka, ta hanyar datse baccinka a daidai lokacin da kake jin daɗinsa, kafin sallar asubahi" - "Kada kayi ƙasa a guiwa wajen zage damtse da yaƙar shaiɗan acikin ƙarshen darenka, ka tashi kayi raka'o'i biyu daidai wannan lokacin, domin haƙiƙa raka'o'i biyun nan sun fi duniya da abinda ke cikinta alkhairi" - "Manzon Allah ﷺ, yace: raka'o'i biyu na alfijir, sun fi duniya da abinda ke cikinta alkhairi" (Sahih Muslim) - Biyo Instagram ɗinmu 👇 https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5 - Telegram channel 👇 https://t.me/hausaislamicpicturesquotes - Facebook page 👇 https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial_freefb

Mata ku saurara......................... Tabbas akwai abun tsoro da tashin hankali a yadda muke gudanar da wasu abubuwa na rayuwar mu. Yana da kyau ka sawa matarka ta gani ko ka saya mata data dan ta saurari wannan video. Allah ya gyara mana zuciya da dabi'un mu. https://www.facebook.com/ZulaykhaMuhammad1818/videos/493062417225278/?app=fbl