HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
February 15, 2025 at 01:33 PM
ZUWA GA MAI YIN WA'AZI KO RUBUTUN NASIHA.
-
"Lallai ka sani! Tabbas duk lokacin da kayi yunƙurin yin rubutu ko wata nasiha ga jama'a, to haƙiƙa kana wakiltar Allah da manzonsa ne, sabida haka sai ka kyautata niyyarka, ka kyautata lafuzzanka, ka kuma tsaftace harshenka. sannan kuma kada ka faɗa face sai abin da kake da hujja a kansa don gudun kada ka yiwa Allah da manzonsa ƙarya, kuma kada kayi don ka burge kowa, sai dai kayi domin Allah kawai, domin haƙiƙa shi ne kaɗai zai iya biyanka"
-
"Da yawa suna mantawa da cewa Allah yana kallon dukkanin abin da suke aikatawa a rayuwarsu, wannan dalilin yasa idan suka tashi yin rubutu ko wani abu suke yin son ransu, basa duba haƙƙin Allah a cikinsa"
-
"Hatta da yawa daga cikin masu yin rubutu a social media, ko yin wata ƴar nasiha, zamiya takan ɗan ɗaukesu su dinga yin abin da basuda hujja a kansa, wataƙila ko don neman suna ko don son su burge wani, SubhanAllah".
-
WhatsApp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6