HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
February 16, 2025 at 03:31 PM
MU KIYAYI CIN HARAM. - "Ɗan adam yakanci haram a nan duniya yayi zaton yaci banza ne, yana mantawa da cewa sai ya biya wannan haƙƙin a ranar ƙiyamah, malam haram haram ce ko da kuwa dukkanin mutane suna bibiyarta, yanzu da yawan mutane sunfi bibiyar haram a kan halal ɗinsu" - "Kada kaci haram kuma kayi tunanin kaci banza, haƙiƙa Allah baya taɓa yafe haƙƙin wani a kan wani, da sannu Allah ta'ala zai tasheka a ranar ƙiyamah ka biya haƙƙin wanda yake binka haƙƙi" - "Wallahi da yawan mutanenmu basa tsoron cin haram a yau, domin kuwa sunsan cewa waccen haram ce, amma duk da hakan za su bita su auka mata, sunsan cewa Allah yana gani, kuma zai tambaye su a ranar ƙiyamah, amma duk da hakan suke zakke mata, subhanallah" - WhatsApp channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i - Telegram channel https://t.me/hausaislamicpicturesquotes - Biyo Instagram ɗinmu https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6
Image from HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES: MU KIYAYI CIN HARAM. - "Ɗan adam yakanci haram a nan duniya yayi zaton...
❤️ 💯 😢 👍 🙏 11

Comments