HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
March 1, 2025 at 01:51 PM
*MACE MAI HAILA A WATAN RAMADANA?* - ❣️"Mace mai haila zata iya yin kowace nau'in ibadah in banda sallah, azumi, kewaya ka'abah, da kuma yin i'itikafi a masallaci" - ❣️"Babu wani laifi gameda mace mai haila tayi wa kanta ruq'yah ta hanyar karanta alƙur'ani, ko sauraron addu'oi, da zikirori waɗanda wajibai ne a musulunci, sannan kuma babu laifi ta karanta mus'hafi a matsayin da ba sai ta kai ga taɓa mus'hafin ba face sai da shamaki" IslamQA.info. Fatawa no 152742 - ❣️"Mace mai haila zata iya yin istigfãri, (neman gafarar Allah) ta hanyar maimaita faɗin A'stagfirullah!, (ina neman gafarar Allah), da kuma sauran addu'oin da suka tabbata acikin alƙur'ani da sunnah" - ❣️"Zata iya yin addu'a, ta roƙi Allah dukkanin abu mai kyau da take buƙata anan duniya da kuma lahira, domin itama addu'a ai ibadah ce" - "Manzon Allah ﷺ, yace: addu'a itama ibadah ce" Sunan Abi Dawud (1479) - ❣️"Zata iya yin zikirori kamar faɗin: SubhanAllah, Wal-Hamdulillah, Wala-Ilaha-ilLallah, Alhamdulillah, da makamancin hakan, waɗanda suka tabbata a Qur'ani da sunnah" - INSTAGRAM https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5

Comments