
Aminiya
February 24, 2025 at 06:38 AM
Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya.
Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya.
Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Jos ta Arewa da Bokkos da Shendam da Mangu da kuma Kenke.
Ko waɗanne irin matakai ya kamata al’umma su ɗauka don kauce wa kamuwa da wannan cuta?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan matakan kariya daga cutar ƙyandar biri.
Domin sauke shirin, latsa nan👇
https://aminiya.ng/najeriya-a-yau-matakan-kariya-daga-cutar-%c6%99yandar-biri/