
Al-Wesam Center
February 3, 2025 at 06:03 PM
*🌙DAUSAYIN RAMADAN 1446🌙*
Ina mai neman rabauta a watan Ramadan⁉️
Ina mai son ya kasance cikin waɗanda suka ci nasara a Ramadan⁉️
Ina mai son ya kasance cikin waɗanda Allah zai ƴanta su daga wuta zuwa aljanna⁉️
Zo ga amsar tambayoyinka📑
Cibiyar Al-Wesam ta samar da wannan shiri domin ƙoƙarin taimakawa ƴan uwa su yi shiri domin tunkarar azumin Ramadan, da kuma cikin Ramadan ɗin.
✨Shirin zai taimaka wajen kula ayyukan ibada tare yin su da wani irin salo da zai ka riƙa yin ibada irin yanda Manzon Allah ﷺ ya koyar, (ibada daga cikin zuciya, ba a iya gaɓɓai ba).
✨Shiri ne da zai taimake mu domin mu gyara tsakanin mu da Ubangiji domin tunkarar azumin Ramadan
✨Shiri ne da zai yi ƙoƙarin haɓaka imanin da gyara ibadun domin mu riƙa yin ibada irin yanda Manzon Allah ﷺ ya koyar.
✨Shiri ne da ya shafi dukkanin ɓangarorin imani, tarbiyya da ibada, a cikin rayuwar Musulmi.
🗒️Wannan shiri ya ƙunshi abubuwa kamar haka:
1- Wuridin Karatun Alƙur'ani Na Kullum📓
2- Tafsirin Izun ƙarshen Alƙur'ani (Suratul A'ala Zuwa Nasi)📖
3)- Jerangiyar darussa na sauraro 🎤
4- Ramadan Calendar 📅
5- Taƙaitattun rubuce-rubuce📝
6- Azkar na safiya da maraice🗒️
7- Tuni a lokutan aikata ibadu⏰
Shirin zai gudana tsawon kwanaki 45
📅Za'a fara a tsakiyar watan Sha'aban 15/8/1446
📅Za'a kammala ƙarshen watan Ramadan zuwa 29/9/1446
Da wasu abubuwa masu yawa wanda za su zo in sha Allah.
Domin babiyar wannan shiri👇🏼
WhatsApp 👇🏼
https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7
Telegram👇🏼
https://t.me/dausayinramadan
❤️
👣
💚
🙏
4