
Al-Wesam Center
481 subscribers
About Al-Wesam Center
💡Al-Wesam Center cibiya ce da ta mayar da hankali wajen haɓaka Ilimin Qur'ani da dukkanin ɓangarorin shi a cikin harshen Hausa. 📌Muna amfani da salo na yada karatuttu na kallo (video) da na sauraro (Audio) da kuma rubuce-rubuce (PDF) a ɓangarorin na Qur'ani. Sannan kuma akwai tsarin shirya Daurori da samar da shirye-shirye (Programs) na tsawon wani lokaci wanda idan mutum ya kammala zai iya samun shaidar kammalawa (Certificate). 📌Domin samun shirye-shiryen mu zaka iya bibiyar mu a kafafen yaɗa bayanai kamar haka: 👇 *Whatsapp 👇* https://whatsapp.com/channel/0029VaBOzv6BA1ey8K2O8l3w *Telegram 👇* https://t.me/alwesamforquran *Facebook 👇* https://www.facebook.com/Daurawa8?mibextid=ZbWKwL *YouTube 👇* https://www.youtube.com/@alwesamquraniccentar Muna fatan Allah ya taimake mu a wannan yunƙuri namu 🤲
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

Fa'idar mu ta yau 💚🌾 #Sha'aban 20, 1446 #February 19, 2025 WhatsApp https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7 Telegram https://t.me/dausayinramadan


Ramadan Mubarak 🌙 Muna yiwa Al'ummar Musulmi maraba da shigowar Watan Ramadan, Allah ya sa muna cikin ƴantattun bayi a cikin shi.💚🌾


Farin ciki tare da Qur'ani🤗 Farin ciki lokacin karanta shi. Farin ciki lokacin sauraron shi Farin ciki yayin koyon shi Farin ciki yayin koyar da shi Farin ciki lokacin haddace shi Farin ciki yayin tadabburin shi Farin ciki a ranar lahira lokacin da zai cece mu 💚🌾 #Alwesamforquran WhatsApp Channel 👇🏼 https://whatsapp.com/channel/0029VaBOzv6BA1ey8K2O8l3w Telegram Channel👇🏼 https://t.me/alwesamforquran

Mafi kyawun Application na Qur'ani da na taɓa amfani dashi a duniya baki ɗaya. Sunan shi #Surah Wannan Application ɗin Mallakin: مركز تفسير للدراسات القرآنية Santa (Center) ce da ta mayar da hankali wajen haɓaka darussa na Alƙur'ani (دراسات القرآنية) ta fannoni daban-daban. Suna da wasu Application ɗin masu kyau sosai da ya kamata duk ɗaliban Alƙur'ani su neme su domin amfana. Suma sauran Application ɗin zan yi bayanin su nan gaba, in sha Allah. Daga cikin abubuwan da ya ƙunsa wanda ba a kowanne application na Alƙur'ani ake samun shi ba ka akwai: 1) Tafsir: Yana ɗauke da tafsirin Malamai guda 5: - المختصر في التفسير - تفسير ابن كثير - تفسير السعدي - تفسير البغوي - تفسير الطبري 2) Ƙira'ãt: Akwai ƙira'at guda goma a cikin shi, ta yanda idan ka zo kan aya kana iya dubawa sauran Malaman ƙira'at yaya suka karanta ta. 3) Li'irabi: Kowacce aya akwai Li'irabin ta, kuma Li'irabi mai kyau sosai . 4) Sarfu: Akwai Hukunce-Hukuncen na Sarfu na kowace kalma a cikin shi. 5) Tarjama: Ana iya duba Tarjamar aya (da harshen Turanci kaɗai). 6) Ulumus Surah: Duk wani abu da ya kamata ka sani akan sura akwai a cikin shi. Misali: - Sunayen ta - Lokacin saukar ta (Makka ko Madina) - Jigon abin da take koyarwa - Falalar ta - Adadin ayoyin ta, da saɓanin lissafi da ake samu na Malamai, duka akwai. - Adadin kalmomin ta. - Adadin haruffan ta. - Adadin wasullan ta. - Jerin saukar ta (Itace Suratu ta nawa a sauka) 7) Darasin da aka koya a kowanne shafi na Alƙur'ani 8) Fihrasa: Zaka iya bincikar sura ko juz'i ko shafi da kake so, domin ka isa gare ta kai tsaye. 9) Sanya Alama: zaka iya sanya alamar wajen da ka tsaya yayin maraja'a ko hadda. 10) Sauti (Audio): Akwai sauti na Malamai guda 20 daga cikin Malaman da suka karanta Alƙur'ani na sauti na duniya, ta yanda zaka iya sanyawa kana sauraro kuma kana gani. -Kuma akwai Sauti na tafsirin Alƙur'ani (المختصر في التفسير) Ta yanda ake karanto aya sannan kuma a karanto tafsirin ta. -Sannan kana iya sauraron kalma ita kaɗai, kuma ka sanya adadin da kake so ta maimaitu. -Haka nan zaka iya sanya sautin aya guda ɗaya ko biyu ko sama da haka, kuma ka sanya adadin da kake so ta maimaitu. (Wannan zai taimaki masu son haddace Alƙur'ani). 11) Kuɗɗa ( Planning na muraja'a ko hadda): Zaka iya tsara yanda zaka ringa yin muraja'a da abin da zaka ringa karantawa kullum, ko haddacewa. 12) Jarrabawar (Quiz): Akwai Quiz kala guda 4 ga waɗanda suke haddar Alƙur'ani, domin gwada ƙarfin haddar su. 13) Ta'aliƙi (Ƙarin bayani): Idan kana cikin karatu sai kaga wata fa'ida zaka iya rubuta ta ka ajiye a cikin wannan Application. 14) Bincike (Searching) Zaka iya binciko kowacce irin kalma ta Alƙur'ani, sannan ka ga sau nawa wannan kalmar ta maimaitu a cikin Alƙur'ani da surorin da ta fito a ciki, kuma ita ta nawace a cikin jerin su, da kuma Juzūr (asalin kalma) sau nawa ya maimaitu. 15) Launin shafi: Yana ɗauke da launuka guda 5 (kore, blue, brown etc) ta yanda zaka iya zaɓar kalar da kake so. - Sannan zaka iya sanya yanayi na dare (night mode 🌃) domin gudun matsalar Ido. 16) Yare: Zaka iya amfani da shi da ɗaya daga cikin yaruka guda 4 ( Arabic, English, Urdu, Chinese) 17) Sanya Alama tsakanin Maudu'ai na Alƙur'ani daban daban, misali: a cikin Suratul Munafiƙun, tun daga aya ta 1 zuwa ta 8 Allah yana magana akan munafukai ne, daga ta 9 zuwa ƙarshen surar kuma Allah yana magana da muminai ne. To zaka iya sanya wannan alamar ta yanda zaka iya ganewa an gama magana akan abu kaza an koma kan wani abu daban. 18) Nau'in bugu: An yi amfani da rubutun Alƙur'ani ɗan Madina ne (مصحف المدينة) 19) Darussa: Yana bayanin fa'idodi da darussan da aka koya a kowane shafi. 20) Sannan kuma kyautata ne, babu wani kuɗi ko tallace-tallace a cikin shi kwata-kwata. Da sauran abubuwan da sai wanda ya yi amfani da shi zai san su. Ga link ɗin shi nan a ƙasa domin saukewa (Downloading)👇 https://play.google.com/store/apps/details?id=com.surahapp #Dausayin_Ramadan_1446 WhatsApp https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7 Telegram https://t.me/dausayinramadan

Dausayin Ramadan 🌙 Sauran bayanai zasu biyo baya in sha Allah🗒️


Amsar wasu daga cikin tambayoyin ku a kan shirin Dausayin Ramadan

*🌙DAUSAYIN RAMADAN 1446🌙* Ina mai neman rabauta a watan Ramadan⁉️ Ina mai son ya kasance cikin waɗanda suka ci nasara a Ramadan⁉️ Ina mai son ya kasance cikin waɗanda Allah zai ƴanta su daga wuta zuwa aljanna⁉️ Zo ga amsar tambayoyinka📑 Cibiyar Al-Wesam ta samar da wannan shiri domin ƙoƙarin taimakawa ƴan uwa su yi shiri domin tunkarar azumin Ramadan, da kuma cikin Ramadan ɗin. ✨Shirin zai taimaka wajen kula ayyukan ibada tare yin su da wani irin salo da zai ka riƙa yin ibada irin yanda Manzon Allah ﷺ ya koyar, (ibada daga cikin zuciya, ba a iya gaɓɓai ba). ✨Shiri ne da zai taimake mu domin mu gyara tsakanin mu da Ubangiji domin tunkarar azumin Ramadan ✨Shiri ne da zai yi ƙoƙarin haɓaka imanin da gyara ibadun domin mu riƙa yin ibada irin yanda Manzon Allah ﷺ ya koyar. ✨Shiri ne da ya shafi dukkanin ɓangarorin imani, tarbiyya da ibada, a cikin rayuwar Musulmi. 🗒️Wannan shiri ya ƙunshi abubuwa kamar haka: 1- Wuridin Karatun Alƙur'ani Na Kullum📓 2- Tafsirin Izun ƙarshen Alƙur'ani (Suratul A'ala Zuwa Nasi)📖 3)- Jerangiyar darussa na sauraro 🎤 4- Ramadan Calendar 📅 5- Taƙaitattun rubuce-rubuce📝 6- Azkar na safiya da maraice🗒️ 7- Tuni a lokutan aikata ibadu⏰ Shirin zai gudana tsawon kwanaki 45 📅Za'a fara a tsakiyar watan Sha'aban 15/8/1446 📅Za'a kammala ƙarshen watan Ramadan zuwa 29/9/1446 Da wasu abubuwa masu yawa wanda za su zo in sha Allah. Domin babiyar wannan shiri👇🏼 WhatsApp 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7 Telegram👇🏼 https://t.me/dausayinramadan

Kada ka bari rikicin duniya ya raba ka da abin da aka halicci domin shi (bautar Allah) Ita wannan duniyar ba za'a samu komai a cikin ta ba sai abin da Allah ya rubuta zaka samu💚🌾 #Alwesamforquran WhatsApp Channel 👇🏼 https://whatsapp.com/channel/0029VaBOzv6BA1ey8K2O8l3w Telegram Channel👇🏼 https://t.me/alwesamforquran

In dai kana da lokacin yin Facebook, Twitter, Instagram, Tiktok da sauran kallace-kallace; to kana da lokacin hardace Alƙur'ani 📖. Hardar Alƙur'ani akwai falala, da albarka, da nishaɗi, da natsuwa a ciki zuciya tun daga nan duniya har zuwa lahira. Ƴan uwana masu albarka, lokaci bai ƙure ba. Wanda bai hardace yana ƙarami ba, zai iya hardacewa a yanzu (ko da kuwa bayan aure ne ko manyanta), sai a yi hardar kaɗan-kaɗan. In dai da tsari mai kyau, kuma da malamin da za ka dinga baiwa hardar, InshaAllah za a iya hardacewa. Kawai ka saka himma, kuma ka roƙi Allah ya taimake ka. Allah ka sa mu cikin ma'abota Qur'ani 💚🌾 #Alwesamforquran WhatsApp Channel 👇🏼 https://whatsapp.com/channel/0029VaBOzv6BA1ey8K2O8l3w Telegram Channel👇🏼 https://t.me/alwesamforquran