Al-Wesam Center
Al-Wesam Center
February 4, 2025 at 05:17 AM
In dai kana da lokacin yin Facebook, Twitter, Instagram, Tiktok da sauran kallace-kallace; to kana da lokacin hardace Alƙur'ani 📖. Hardar Alƙur'ani akwai falala, da albarka, da nishaɗi, da natsuwa a ciki zuciya tun daga nan duniya har zuwa lahira. Ƴan uwana masu albarka, lokaci bai ƙure ba. Wanda bai hardace yana ƙarami ba, zai iya hardacewa a yanzu (ko da kuwa bayan aure ne ko manyanta), sai a yi hardar kaɗan-kaɗan. In dai da tsari mai kyau, kuma da malamin da za ka dinga baiwa hardar, InshaAllah za a iya hardacewa. Kawai ka saka himma, kuma ka roƙi Allah ya taimake ka. Allah ka sa mu cikin ma'abota Qur'ani 💚🌾 #alwesamforquran WhatsApp Channel 👇🏼 https://whatsapp.com/channel/0029VaBOzv6BA1ey8K2O8l3w Telegram Channel👇🏼 https://t.me/alwesamforquran
👍 🙏 2

Comments