Al-Wesam Center
Al-Wesam Center
February 18, 2025 at 07:11 AM
Wasu daga cikin amfanin da Qur'ani na waya (application) ne ke da shi kaɗai, banda normal Qur'ani. 1- Sauƙin ɗauka ko rikicewa a kowane guri kasancewar yana wayar ka. 2- Halaccin karanta shi ba tare da sharaɗin tsarki a yayin amfani da shi ba. 3- Kana da damar sanya alamar tsayawa sama da guda ɗaya, saɓanin na takarda wanda zaren saka alamar tsayawa guda ɗaya ne a cikin shi. 4- Rubuta wata fa'ida da kaci karo da ita a yayin karatu, da kuma tura ta zuwa wasu kafafen sadarwa. 5- Sauraron aya ko surar da kake so da sautin malamai mabanbanta. 6- Damar karatu cikin duhun dare ba tare da ka buƙataci haske ba. 7- Sanin tafsiri, li'irabi, sarf, sababun nuzuul, Makki da Madaniy, Qira'a'at da sauran su a kowace Surah. 8- Jiyewa kanka karatu, ga dalibai masu haddar Qur'ani. 9- Sanin Hukunce-hukunce na tajweed. 10- Shirya Planning na haddar ko muraja'ar Qur'ani, tare da sanya alarm ⏰ a lokacin da kake so ya ringa bugawa. 11- Daidaita girman rubutu, a yayin karatu. 12- Sauƙin bincike a Qur'ani ko tafsiri. 13- Babu buƙatar sai ka tashi zuwa ɗauko shi a cikin kanta ko wani guri lokacin da ka so karantawa, domin yana cikin wayar ka. 14- Sauƙin sanin lokaci a yayin da kake karatu. 15- Buɗe shafi kai tsaye ba tare da ka taɓa ba, ta yanda zaka saita shi ya riƙa buɗe shafi na gaba da kansa bayan wani lokaci da ka saka. 16- Galibin su kyauta ne ba tare da biyan kuɗi ba, kawai downloading zaka yi a wayar ka. 17- Cancanja kalar shafi, daga fari zuwa wata kala daban. 18- Samun tarjamar aya zuwa wasu yaruka daban-daban. 19- Sanya alama da zata rarrabe maka maudu'an Qur'ani. 20- Samun kaso mai tsoka na Ulumul Qur'an a wasu App ɗin. 21) Sauƙin buɗe shafi ko surar da kake son karantawa. 22) Kacici-kacici (Quiz) domin auna fahimta ga wanda suke haddar Qur'ani. Wannan kaɗai na iya tattarawa cikin amfanin da Qur'ani na waya kaɗai ke da shi, kuma na san zaku iya samo wasu. Mafiya kyawun App na Qur'ani da na sani a duniya akwai: "Wahy" https://play.google.com/store/apps/details?id=com.logicdev.quran_reader "Surah" https://surahapp.com #dausayin_ramadan_1446 WhatsApp https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7 Telegram https://t.me/dausayinramadan
❤️ 🙏 2

Comments