
Al-Wesam Center
February 18, 2025 at 07:11 AM
Mafi kyawun Application na Qur'ani da na taɓa amfani dashi a duniya baki ɗaya.
Sunan shi #surah
Wannan Application ɗin Mallakin:
مركز تفسير للدراسات القرآنية
Santa (Center) ce da ta mayar da hankali wajen haɓaka darussa na Alƙur'ani (دراسات القرآنية) ta fannoni daban-daban.
Suna da wasu Application ɗin masu kyau sosai da ya kamata duk ɗaliban Alƙur'ani su neme su domin amfana.
Suma sauran Application ɗin zan yi bayanin su nan gaba, in sha Allah.
Daga cikin abubuwan da ya ƙunsa wanda ba a kowanne application na Alƙur'ani ake samun shi ba ka akwai:
1) Tafsir: Yana ɗauke da tafsirin Malamai guda 5:
- المختصر في التفسير
- تفسير ابن كثير
- تفسير السعدي
- تفسير البغوي
- تفسير الطبري
2) Ƙira'ãt: Akwai ƙira'at guda goma a cikin shi, ta yanda idan ka zo kan aya kana iya dubawa sauran Malaman ƙira'at yaya suka karanta ta.
3) Li'irabi: Kowacce aya akwai Li'irabin ta, kuma Li'irabi mai kyau sosai .
4) Sarfu: Akwai Hukunce-Hukuncen na Sarfu na kowace kalma a cikin shi.
5) Tarjama: Ana iya duba Tarjamar aya (da harshen Turanci kaɗai).
6) Ulumus Surah: Duk wani abu da ya kamata ka sani akan sura akwai a cikin shi. Misali:
- Sunayen ta
- Lokacin saukar ta (Makka ko Madina)
- Jigon abin da take koyarwa
- Falalar ta
- Adadin ayoyin ta, da saɓanin lissafi da ake samu na Malamai, duka akwai.
- Adadin kalmomin ta.
- Adadin haruffan ta.
- Adadin wasullan ta.
- Jerin saukar ta (Itace Suratu ta nawa a sauka)
7) Darasin da aka koya a kowanne shafi na Alƙur'ani
8) Fihrasa: Zaka iya bincikar sura ko juz'i ko shafi da kake so, domin ka isa gare ta kai tsaye.
9) Sanya Alama: zaka iya sanya alamar wajen da ka tsaya yayin maraja'a ko hadda.
10) Sauti (Audio): Akwai sauti na Malamai guda 20 daga cikin Malaman da suka karanta Alƙur'ani na sauti na duniya, ta yanda zaka iya sanyawa kana sauraro kuma kana gani.
-Kuma akwai Sauti na tafsirin Alƙur'ani
(المختصر في التفسير)
Ta yanda ake karanto aya sannan kuma a karanto tafsirin ta.
-Sannan kana iya sauraron kalma ita kaɗai, kuma ka sanya adadin da kake so ta maimaitu.
-Haka nan zaka iya sanya sautin aya guda ɗaya ko biyu ko sama da haka, kuma ka sanya adadin da kake so ta maimaitu. (Wannan zai taimaki masu son haddace Alƙur'ani).
11) Kuɗɗa ( Planning na muraja'a ko hadda): Zaka iya tsara yanda zaka ringa yin muraja'a da abin da zaka ringa karantawa kullum, ko haddacewa.
12) Jarrabawar (Quiz): Akwai Quiz kala guda 4 ga waɗanda suke haddar Alƙur'ani, domin gwada ƙarfin haddar su.
13) Ta'aliƙi (Ƙarin bayani): Idan kana cikin karatu sai kaga wata fa'ida zaka iya rubuta ta ka ajiye a cikin wannan Application.
14) Bincike (Searching) Zaka iya binciko kowacce irin kalma ta Alƙur'ani, sannan ka ga sau nawa wannan kalmar ta maimaitu a cikin Alƙur'ani da surorin da ta fito a ciki, kuma ita ta nawace a cikin jerin su, da kuma Juzūr (asalin kalma) sau nawa ya maimaitu.
15) Launin shafi: Yana ɗauke da launuka guda 5 (kore, blue, brown etc) ta yanda zaka iya zaɓar kalar da kake so.
- Sannan zaka iya sanya yanayi na dare (night mode 🌃) domin gudun matsalar Ido.
16) Yare: Zaka iya amfani da shi da ɗaya daga cikin yaruka guda 4 ( Arabic, English, Urdu, Chinese)
17) Sanya Alama tsakanin Maudu'ai na Alƙur'ani daban daban, misali: a cikin Suratul Munafiƙun, tun daga aya ta 1 zuwa ta 8 Allah yana magana akan munafukai ne, daga ta 9 zuwa ƙarshen surar kuma Allah yana magana da muminai ne.
To zaka iya sanya wannan alamar ta yanda zaka iya ganewa an gama magana akan abu kaza an koma kan wani abu daban.
18) Nau'in bugu: An yi amfani da rubutun Alƙur'ani ɗan Madina ne (مصحف المدينة)
19) Darussa: Yana bayanin fa'idodi da darussan da aka koya a kowane shafi.
20) Sannan kuma kyautata ne, babu wani kuɗi ko tallace-tallace a cikin shi kwata-kwata.
Da sauran abubuwan da sai wanda ya yi amfani da shi zai san su.
Ga link ɗin shi nan a ƙasa domin saukewa (Downloading)👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.surahapp
#dausayin_ramadan_1446
WhatsApp
https://chat.whatsapp.com/GA99DCOoskP5gOtQEvOyK7
Telegram
https://t.me/dausayinramadan
❤️
2