TARIHIN JARUMAN MATA 🌹
TARIHIN JARUMAN MATA 🌹
February 5, 2025 at 05:41 AM
Mauludin Gwarazan Karbala: JAGORA YA GANA DA ‘YAN MU’ASSASATU ABUL FADL ABBAS (AS) Daga Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Da yake ganawa da mambobin Mu’assasatu Abul Fadl Abbas, wanda suka hada har da bangarorinta irin su Kasshafa, Intizar da JASAZ, a ranar Talata 5 ga watan Sha’aban 1446 (4/2/2025), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada bukatar sadaukarwa ga addini saboda Allah. Jagoran, ya fara jawabinsa ne da taya ‘yan uwa murna da zagayowar kwanukan haihuwan gwarazan Karbala, wanda yace, ba zai zama a bisa hadari ba ne haihuwarsu ya zo a jere. “Na farkonsu Abi Abdullahil Husain (AS) wanda aka haifa ranar 3 ga watan Sha’aban; Sai kuma na biyunsu, dan uwansa wanda ya ba da ransa wajen kare shi, Abul Fadl Abbas, haihuwarsa ta kasance ranar 4 ga wata. Sai kuma Imam Zainul Abidin, wanda muna iya cewa shi ma ya fi kowa shan wahalar Karbala, don akan idonsa aka yi komai, shi kuma haihuwarsa ta zo ranar 5 ga wata.” Yace: “Duk wadannan gwaraza, duk cikansu ‘rumuz’ (alamomi) ne na sadaukarwa, kowannensu an haife shi a gwagwarmaya, ya bar duniya a gwagwarmaya.” Jagora ya bayyana yadda mahaifiyar Sayyid Abbas ta yi masa tare da ‘yan uwansa tarbiyar girmama ‘ya’yan Sayyida Zahra (SA), wanda haka yasa ko da suke uba daya, amma basu ganin ‘ya’yan Sayyida Fatima a matsayin ‘yan uwansu, face a matsayin shugabanninsu. Yace: “Sayyida Ummul Banin, mahaifiyar Sayyid Abbas bata taba daukan Sayyida Zahra a matsayin kishiyarta ba, tana ganinta a matsayin shugabarta ne, kuma tace ma danta Abul Fadl Abbas, na haneka, kar ka kuskura kace ma Husaini ‘akhiy’ (dan uwana), kace masa ‘Sayyidiy wa maulaya’, domin Sayyidinka ne kuma Maulanka, shi shugabanka ne.” Ya cigaba da cewa: “Saboda haka kullum shi Abul Fadl Abbas abin da yake kiran Imam Husaini shi ne ‘Sayyidi wa Maulaya’, sai sau daya rak ya taba kiransa da ‘dan uwansa, shi ne ranar Shahadarsa bayan an harbe shi da kibiya a wajen debo ruwa.” Jagora ya bayyana muhimmancin tsayuwa kyam a tafarkin Allah Ta’ala, tare da albishir ga duk wanda ya tsaya kyam da cewa akwai jarabawa, wanda yace lazim ne. “Har in ka ga jarabawar bata zo ba, ka tambayi kanka, kyam kuwa ka tsaya din? Don dabi’ar hanyar kenan.” Ya jaddada cewa: “Wadannan bayin Allah din sun zamo ‘rumuz’, wato alamomi da za a yi koyi da su a wajen sadaukarwa. Su gabadayan rayuwarsu sun sadaukar ne, shi ne kuma ya wanzar mana da wannan addini.” Sannan ya ja hankali akan tsayuwa da raya al’amarinsu da kuma tasirantuwa da rayawan da ake yi. Yace: “Raya al’amarinsu na sa a ga tasirinsa a tare da mu. Ya kamata a ga irin wannan ne a jikinmu mu ma, a ga mu ma muna koyi da irin abin da suka rayu a kai, suka sadaukar akai.” Yace: “Kulasan abin, kalma daya na abin da duk suka yi, ita ce sadaukarwa. Sadaukar da rai. Ka ba da komai saboda Allah. Shi ne abin da ke gabagaremu, sadaukarwan nan. Kuma al’ummar nan abin da ta rasa kenan, su waye za su sadaukar ‘Fisabilillah’” Sannan ya karkare jawabinsa da nasiha akan ya zama mutum ya sadaukar ne bisa zabin kansa kuma saboda Allah Ta’ala. “Ya zama sadaukarwar nan bisa zabin kai mutum zai yi don neman yardar Allah, ba bisa tilasci ba.” Ya jaddada. Bayan kammala jawabin, an gabatar da waken jinjina ga gwarazan Shahidai, musamman Shahidan Mu’assasar Abul Fadl Abbas, tare da alkawari akan cigaba da dafawa Jagora (H) da neman afuwarsa akan gazawa. Daga nan Jagora ya yanka alkakin da aka yi guda uku don haihuwar gwarazan na Karbala (AS). @SZakzakyOffice #eidmobarak #prayforpalestine #ourmartyrsourheroes 05/Shaaban/1446 04/02/2025

Comments