
TARIHIN JARUMAN MATA ๐น
127 subscribers
About TARIHIN JARUMAN MATA ๐น
Tarihin jaruman mata da daukan darussa daga rayuwar su ๐น
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

*SALLAR DAREN BAKWAI GA SHA'ABAN*๐๐ Voice Of Aqeelatu Bani Hashem โ๏ธ Sallah Raka'a 2. Raka'a Farko Fatiha 1, Kulhuwallahu 100, Raka'a ta Biyu Fatiha 1, Kursiyyu 1. Wanda yayi wannan sallah Allah zai Amshi Addu'ar sa Ya Biya Masa Bukatun Sa, Za kuma a cigaba da Rubuta Masa Ladar Shahidi A Kulli Yaumin A Watan. *SALLAH TA BIYU*.๐ Sallah Raka'a 2. A Raka'ar Farko Fatiha 1, Kulhuwallahu 100, A Raka'a ta biyu Fatiha 1, Kursiyyu 100. Wanda yayi wannan sallah Allah zai Sanya shi cikin Muminai. Maitham At-tammar Zone ๐ธ *Allahumma Ajjeel liwaliyukal Faraj* ๐คฒ๐ผ

Mauludin Gwarazan Karbala: JAGORA YA GANA DA โYAN MUโASSASATU ABUL FADL ABBAS (AS) Daga Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Da yake ganawa da mambobin Muโassasatu Abul Fadl Abbas, wanda suka hada har da bangarorinta irin su Kasshafa, Intizar da JASAZ, a ranar Talata 5 ga watan Shaโaban 1446 (4/2/2025), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada bukatar sadaukarwa ga addini saboda Allah. Jagoran, ya fara jawabinsa ne da taya โyan uwa murna da zagayowar kwanukan haihuwan gwarazan Karbala, wanda yace, ba zai zama a bisa hadari ba ne haihuwarsu ya zo a jere. โNa farkonsu Abi Abdullahil Husain (AS) wanda aka haifa ranar 3 ga watan Shaโaban; Sai kuma na biyunsu, dan uwansa wanda ya ba da ransa wajen kare shi, Abul Fadl Abbas, haihuwarsa ta kasance ranar 4 ga wata. Sai kuma Imam Zainul Abidin, wanda muna iya cewa shi ma ya fi kowa shan wahalar Karbala, don akan idonsa aka yi komai, shi kuma haihuwarsa ta zo ranar 5 ga wata.โ Yace: โDuk wadannan gwaraza, duk cikansu โrumuzโ (alamomi) ne na sadaukarwa, kowannensu an haife shi a gwagwarmaya, ya bar duniya a gwagwarmaya.โ Jagora ya bayyana yadda mahaifiyar Sayyid Abbas ta yi masa tare da โyan uwansa tarbiyar girmama โyaโyan Sayyida Zahra (SA), wanda haka yasa ko da suke uba daya, amma basu ganin โyaโyan Sayyida Fatima a matsayin โyan uwansu, face a matsayin shugabanninsu. Yace: โSayyida Ummul Banin, mahaifiyar Sayyid Abbas bata taba daukan Sayyida Zahra a matsayin kishiyarta ba, tana ganinta a matsayin shugabarta ne, kuma tace ma danta Abul Fadl Abbas, na haneka, kar ka kuskura kace ma Husaini โakhiyโ (dan uwana), kace masa โSayyidiy wa maulayaโ, domin Sayyidinka ne kuma Maulanka, shi shugabanka ne.โ Ya cigaba da cewa: โSaboda haka kullum shi Abul Fadl Abbas abin da yake kiran Imam Husaini shi ne โSayyidi wa Maulayaโ, sai sau daya rak ya taba kiransa da โdan uwansa, shi ne ranar Shahadarsa bayan an harbe shi da kibiya a wajen debo ruwa.โ Jagora ya bayyana muhimmancin tsayuwa kyam a tafarkin Allah Taโala, tare da albishir ga duk wanda ya tsaya kyam da cewa akwai jarabawa, wanda yace lazim ne. โHar in ka ga jarabawar bata zo ba, ka tambayi kanka, kyam kuwa ka tsaya din? Don dabiโar hanyar kenan.โ Ya jaddada cewa: โWadannan bayin Allah din sun zamo โrumuzโ, wato alamomi da za a yi koyi da su a wajen sadaukarwa. Su gabadayan rayuwarsu sun sadaukar ne, shi ne kuma ya wanzar mana da wannan addini.โ Sannan ya ja hankali akan tsayuwa da raya alโamarinsu da kuma tasirantuwa da rayawan da ake yi. Yace: โRaya alโamarinsu na sa a ga tasirinsa a tare da mu. Ya kamata a ga irin wannan ne a jikinmu mu ma, a ga mu ma muna koyi da irin abin da suka rayu a kai, suka sadaukar akai.โ Yace: โKulasan abin, kalma daya na abin da duk suka yi, ita ce sadaukarwa. Sadaukar da rai. Ka ba da komai saboda Allah. Shi ne abin da ke gabagaremu, sadaukarwan nan. Kuma alโummar nan abin da ta rasa kenan, su waye za su sadaukar โFisabilillahโโ Sannan ya karkare jawabinsa da nasiha akan ya zama mutum ya sadaukar ne bisa zabin kansa kuma saboda Allah Taโala. โYa zama sadaukarwar nan bisa zabin kai mutum zai yi don neman yardar Allah, ba bisa tilasci ba.โ Ya jaddada. Bayan kammala jawabin, an gabatar da waken jinjina ga gwarazan Shahidai, musamman Shahidan Muโassasar Abul Fadl Abbas, tare da alkawari akan cigaba da dafawa Jagora (H) da neman afuwarsa akan gazawa. Daga nan Jagora ya yanka alkakin da aka yi guda uku don haihuwar gwarazan na Karbala (AS). @SZakzakyOffice #EidMobarak #PrayForPalestine #OurMartyrsOurHeroes 05/Shaaban/1446 04/02/2025