
Bakandamiya Kitchen
February 20, 2025 at 10:13 AM
*Yadda ake Chinese rice*
*Abubuwan hadawa*
1. Dafaffafiyar shinkafa (wanda aka dafa da gishiri)
2. Karas (carrots)
3. Peas (na gwangwani)
4. Albasa
5. Kwai
6. Tattasai
7. Butter
8. Gishiri
*Yadda ake hadawa*
1. Da farko za ki fasa kwanki a ciki wani karamin kwano sai ki yanka mishi albasa, sai ki sa gishiri kadan sannan ki ajiye a gefe.
2. Ki yanka su tattasai, albasa kanana, sai ki yanka karas na ki (ki sa masa tafasashshe ruwan zafi da baking powder ki rufe nadan wani lokaci sannan ki tace).
3. Ki bude peas naki na gwangwani ki juye shi a kwano sai ki zuba mishi ruwa sosai sannan ki tace. Anan sai ki hada duk veggies naki dukka wuri daya ki ajiye a gefe.
4. Ki daura non stick pan naki akan wuta ki sa butter ki a ciki idan ya narke sai ki kawo kwanki ki sa a ciki, sai ki rika juyawa, (kamar yadda ake miyar kwai)
5. Idan yayi sai ki dauko su carrot da ki ka gyara ki ka ajiye su wuri daya sai ki zuba a ciki ki juya a hankali dan karya kama.
6. Sai ki dauko dafaffafiyar shinkafa ki sa a ciki ki juya a hankali har sai ya yi.
7. Sai ki sauke ki sa a plate ki kawo miyar stew ki sa.
https://kitchen.bakandamiya.com/yadda-ake-chinese-rice/
❤️
👍
🫶
7