Bakandamiya Kitchen
Bakandamiya Kitchen
February 20, 2025 at 10:19 AM
*Yadda ake hada egg masala* *Abubuwan hadawa* 1. Dankalin turawa 2. Albasa 3. Carrots 4. Maggi 5. Mangyada 6. Kwai *Yadda ake hadawa* 1. Farko za ki wanke dankali da carrots ki yanka su kanana sosai sai ki dafa. 2. Idan sunyi laushi sai ki zuba a cikin bowl ki fasa kwai. Ki saka maggi da albasa da tarugu a ciki sai ki juya. 3. Za ki dora tandar soya waina akan wuta ki saka mai. Idan ya yi zafi ki dinga diban wannan hadin ki na zubawa a ciki. Idan ya yi sai a juya dayan gefen kaman yanda ake toya waina. Idan ya kammala sai a sauke, haka za ki yi ta yi har sai kin kare. https://kitchen.bakandamiya.com/yadda-ake-hada-egg-masala/
👍 ❤️ 🫶 8

Comments