✦✧ 𝐀𝐃 π—ͺπ—˜π—•πŸ― π€π‚π€πƒπ„πŒπ˜ ✧✦
✦✧ 𝐀𝐃 π—ͺπ—˜π—•πŸ― π€π‚π€πƒπ„πŒπ˜ ✧✦
February 19, 2025 at 08:52 PM
*Mene Ne Web3?* Assalamu Alaikum 'yan uwa! Maraba da zuwa wannan darasi na Web3 a cikin harshen Hausa. A yau, zan yi bayani a saukake kan *Web3* menene shi, yadda yake aiki, da kuma yadda zamu yi amfani da shi. *1. Mene Ne Web3?* Web3 yana nufin sabon salo na internet wanda yake ba mutane yancin amfani da tsarin da babu tsaka tsaki (decentralization). Yana amfani da blockchain, wato wata fasahar da ke ba mutane ikon mallakar bayanansu ba tare da dogaro da kamfanoni irin su Google, Facebook ko banks ba. A takaice, Web3 yana nufin internet mai yanci koh nace freedom wanda ba ya bukatar tsaka tsakiya, kuma yana baiwa kowa iko da bayanansa. *2. Bambancin Web1, Web2, da Web3* Domin mu fahimci Web3, bari mu yi duba ga abubuwan da suka gabata: *Web1 (1990s - Early 2000s):* Wannan shine farkon internet, inda mutane kawai iya karanta bayanai (Read Only Web). Misali, shafukan yanar gizo kamar Yahoo da Wikipedia a lokacin. *Web2 (2005 - Yanzu):* Wannan shine tsarin da muke amfani da shi yanzu, inda mutane za su iya karantawa da aikar da bayanai (Read & Write Web). Amma matsalar shi ita ce, kamfanoni irin su Facebook, Google da Twitter su ne ke mallakar bayananmu. *Web3 (Coming Future):* Wannan sabon zamani ne da yake baiwa kowa iko da bayanansa (Read, Write & Own Web). Yana aiki ne da BLOCKCHAIN, wanda ke hana kamfanoni mallakar bayanan mutane. *3. Yadda Web3 Ke Aiki* A Web3, ana amfani da cryptocurrency, smart contracts, da kuma decentralized applications (DApps).kamar hakaπŸ‘‡πŸ‘‡ *Cryptocurrency:* Kudi na zamani da ake amfani da su a blockchain, kamar Bitcoin, Ethereum, da dai sauransu. *Smart Contracts:* Wadansu yarjejeniyoyi ne na digital da ke aiki automatic a kan blockchain ba tare da bukatar matsakaic koh tsaka tsakiyai ba. *DApps (Decentralized Applications):* Manhajoji ne da ke aiki a kan blockchain, kamar su Uniswap, OpenSea, da Metamask. *4. Fa'idodin Web3* *Yancin Kai:* Babu kamfani ko hukuma da ke mallakar bayananka. *Babu Matsakaici or intermident:* Kana iya aikawa da kudi ko bayanai ba tare da amfani da banki ko Facebook ba. *Ayyuka na Zamani:* Za ka iya amfani da NFTs, DeFi, da Metaverse don samun kudin shiga. *5. Summary* *Web3* wani sabon zamani ne da zai sake fasalin internet da yadda muke mu'amala da duniya. Idan kana son samun ilimi akan Web3, yana da kyau ka koyi yadda blockchain ke aiki da kuma yadda ake amfani da crypto...
πŸ‘ ❀️ 5

Comments