โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ WhatsApp Channel

โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ

143 subscribers

About โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ

๐Ÿ”น AD WEB3 ACADEMY ๐Ÿ”น Wannan Wata Web3 Academy Ce Inda Ake Raba Ilimin Web3 Da Crypto Airdrops Cikin Harshen Hausa.... Muna Taimakawa Alโ€™ummar Hausawa Wajen Fahimtar Yadda Ake Cin Gajiyar Airdrops, Testnets, Node Mining, Da Dabarun Bunkasa A Web3... Ka Tabbata Kayi Sharing Wannan Channel Ga Abokanka, Domin Samun Ilimi Da Sababin Damarmaki Da Ke Cikin Duniyar Crypto! ๐Ÿš€

Similar Channels

Swipe to see more

Posts

โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
5/25/2025, 9:25:36 AM

Crypto = Strategy ________/________ From Zero to Profits: Wato wannan shine Strategy mai aiki ko kuma nace wanda yake fita. Kafin hakan dole kana buฦ™atar abubuwa guda biyarโ€”Indai kana da waฦดennan abubuwan to in shaa Allahu dole sai ka fara samun kuษ—i ko nace riba a Crypto Trading ษ—in da kakeyi. 1]-Abu na farko dai shine (Educate Yourself), bro/sis babu shortcut a wannan bangaren. Indai kana son ka samu kuษ—i a Crypto ko ka iya trading, ya zama dole sai ka fara gina kanka da ilimi. Wlh duk kuษ—inka idan babu ilimi zaka daษ—e kana buga-buga a kasuwar crypto tare da yin asara mara dalili. Dan haka, abu mafi mahimmanci da yakamata kowa ya sani kamar yadda kusan kowa ษ—in ya sani shine ya zama dole ya mutum ya nemi ilimi kafin investing a crypto idan kana son samun zaman lafiyar dukiya da kuma samun kwanciyar hankalinka. Ilimi yana matukar taka rawar gani a wannan space ษ—in. Space dama da masu ilimi suke wasa da hankalin jahilai. 2]-Abu na biyu shine (Concrete Goals), wato ya zama dole sai ka samarwa kanka wani Clear Goals da zaka tabbata a kansa. Domin Emotion ษ—inka shine kusan yake jagorantar 80%-90% ษ—in duk wani yanke hukuncinka a crypto. Dan haka 'You must set a clear Goals' idan kana son kayi trade successfully a crypto. 3]-Abu na uku shine (Trading Plan), duk wani Successful Trader da ka sani a duniya to dole akwai wani Trading Plan da yake dashi. Wannan abu ne da kowa yake da irin nasa, dan haka kaima ka samarwa da kanka naka. Misali: Kamar ni, a sati akwai iya ranaku da lokacin dana ware gurin yin Trading ษ—ina a baya. Sannan ba ko wanne lokaci nake shiga Trade ba koda kasuwar babu Volatility sosai. Da yawan lokaci nafi shiga Trade cikin dare zuwa wayewar gari. Idan ina son nayi Trade akan wani Token/Coin a baya, so adding ษ—insa zuwa Fav Section ษ—ina ne, sai nayi 'Volume Analysis' akansa zuwa wani ษ—an lokaci kafin na shiga. Idan naga ana samun demand either massive or small, to sai nayi amfani da Trading Plan ษ—ina na yanke hukunci. Dan haka kaima yakamata ka koyi hakan. 4]-Abu na huษ—u shine (Demo Account), ษ—an uwa da shawara kake nema sai nace ma ka fara koyar Trading da Demo kafin ka fara zuba kuษ—inka. DEMO ACCOUNT, free money ne da aka tsara za'ai Trade dasu aci riba ko a faษ—i dasu amma ba tare da ka ita cire kuษ—in ko riba ba. Da yawan wasu Exchanges ษ—in sukan bawa new users ษ—insu irin wannan demo account ษ—in domin ilimantarwa. Kamar wani practical ne da akeyi da kuษ—in bogi, bawai real money bane domin gujewa asara. 5]-P2P = Real Profits! Wato malam abu mafi mahimmanci da yakamata ka dinga yi shine a duk lokacin daka samu kuษ—i a Crypto, to ka tabbatar da kacire abunda ka samu idan kana da bukata. Koda kaci riba a Crypto Market, bata tabbata taka ba sai lokacin da kayi p2p kaga saukar kuษ—in a account ษ—inka. Domin sau da yawan lokaci idan mutum yayi wani (Successful Trading) ษ—in daya samu Profits sosai, emotion ษ—insa yana iya sake yaudararsa domin sake shiga wani Trade ษ—in nan take domin ฦ™ara samun wani Profit ษ—in, wanda hakan yakan iya janyo mutum ya rasa capital tare da Profits ษ—insa gaba ษ—aya. Dan haka, taking profit is one of the best Strategy dana yi imani dashi a harkar Crypto Currency. Ba'a na damar taking profits sama da yadda ake na damar rashin taking profit ษ—in a Crypto. Dan haka, ya zama dole kayi aiki da wannan Strategy ษ—in idan kana son ka amfana da wani abun a wannan space ษ—in. In shaa Allahu nan gaba zamu sake baku wasu shawarorin da muke tunanin zasu amfanar daku game da crypto trading. Abunda muke faษ—a muna faษ—in sune 'By Experience', dan haka yana da kyau a matsayinka na sabon Trader ko mai son fara Crypto Trading kayi aiki dasu. Allah ubangiji yasa mudace. #AminuDayyibZakariyya

โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
5/26/2025, 8:38:23 AM

Idan burinka koyon crypto kyauta trading square is here, idan ma'aikaci ne kai ko dan kasuwa kuma kana son signal genuine free! trading square has tackled all of these ๐Ÿ‘‡https://t.me/tradingsquare001

Post image
Image
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/13/2025, 1:19:57 AM

~ A yanzu Solana kwaya daya (full unit) yana kan farashin Dala 157, idan bani da kudin da zan sayi SOL guda daya zan iya sayan wani bangare nasa kamar 0.5 SOL, 0.02 SOL, haka ma Bitcoin zan iya sayan 0.05 misali, to su NFT ba zaka iya sayan su irin haka ba. Ba zaka iya yankan 0.3 na wani NFT ka saya ba, sai dai ka saya guda (full unit) to shine Non Fungible din, ba'a iya tsaga shi ko fasa shi a sayi wani bangare kamar yadda ake iya sayan 0.1 BNB ko Bitcoin. NFTs suna dauke da digital value na wani abinda yake akwai shi a zahiri, misali "Durov Cap" akwai ta a zahiri amma anyi mata kudi anyi tokenizing dinta Online. Idan ka sayi na Online din kamar exactly ka sayi wancan na zahirin ne. Kuma yana iya kasancewa zallan digital value ne dashi ba lallai ya zama akwai shi a zahiri ba. Kamar Digital Land wanda kamfanin SandBox suka yi NFT dinsu a 2022 kuma suka yi daraja sosai. Duk wani NFT daka gani to shi kadai ne babu irin sa sai dai mai kama dashi amma ba exactly shi ba, misali: ~ Bitcoin akwai irin sa exactly har guda miliyan 21,000,000 babu abinda ya bambanta wani Bitcoin da wani, amma NFT kwaya to kwaya dayan ne kawai, misali: za'a iya yin NFT na Sarkin Kano akan TON blockchain, Sarki Ado Bayero, sannan za'a iya yin NFT na Sarki Aminu ko Sarki Sanusi, kaga waษ—annan mutane ne daban daban. NFT na farko da aka fara yi Crypto da Blockchain industry shine wanda aka yi proposing akan Ethereum a 2018, proposal din ya fito da EIP-721 daga baya DAO suka amince ya koma ERC-721 kamar dai yadda kowa yasan yadda ake yin proposal akan Ethereum, daga EIP zuwa ERC. Kamar yadda ake da kasuwanni Crypto CEX da DEX to suma haka NFT suke da kasuwannin su. Wanda aka fi sani a duniya itace OpenSea, tana kan blockchain fiye da 20, kamar Bitcoin, Ethereum, BNB, da sauran su. Akwai irin su Getgems akan TON, har wa yau akwai kasuwar Fragment akan TON, akwai Magic Eden da Tensor da Nifty duk akan Solana, akwai XRP Cafe akan XRP chain. ~ Akwai Rarible da Foundation akan Ethereum. Suna nan da yawa gaskiya. Sannan NFT suna da "Rarity" wato yanayin yadda suke a kasuwa, zai iya zama suna da yawa kamar daga 1 zuwa 100 suna bangaren high Rarity, wato basu da yawa. Gwargwadon ฦ™arancin NFT a kasuwa gwargwadon darajar sa, idan suna da yawa zaka ga Rarity dinsa is Common, to ba lallai yayi daraja sosai ba. Idan kuma wani abu ne daban kamar Expensive, Light, ko Legen ko Gifted zai iya yin daraja gwargwadon irin darajar abinda ke kunshe cikin NFT din da kuma darajar da aka bashi tun da farko. A yanzu haka TON ya zarce kowane blockchain wajen daily trade na NFT a duniya, idan akwai wanda ya zarce shi bai wuce Ethereum ba, tun bayan NFT na Gift da Pavel Durov ya raba. Kuma wani abun burgewa shine Telegram Collectibles Gifts ana iya Swapping dinsu Off-Chain. NFT gifts da TON suka yi suna kan wallet guda dubu 184,021 kuma rabin su anyi trade dinsu. Telegram Stars da TON coin da kuma Gift suna daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen motsawar TON blockchain. Sai dai muna ganin Stars din zasu iya kawo tsaikowa TON coin, duk da cewa bamu san tsarin da suka yi ba nan gaba. Ya ake yi NFT yayi daraja? Dayan uku ne: 1. Ko dai abinda aka yi NFT dinsa ya fito daga wani babban mutum mai daraja (kamar Durov Cap ๐Ÿงข) ko hoton wani Sarki, ko zanen wata masarauta (Fada). 2. Ko saboda tsananin kaunar da mutane suke yi ma wannan abun. 3. Ko kuma saboda ana neman sa ruwa Ajallo domin ayi amfani dashi, wani zai ce kamar yaya? Idan kana yawan buga wasanni "Games" akan Blockchain kuma Games na kudi zaka ga yawancin su NFT ne. Misali: Game din kwallo (Ball), sai kace kai ne Ronaldo, Owen ko Fele, ko Kanu Nwanko, Okocha ko Babangida, sai a baka Ronaldo shi kadai, sai ace kafin ka fara iya buga Ball din sai kayi dressing din Ronaldo, sai ka sayo Rigar Ronaldo, Wandon sa, takalmar sa, Rigar NFT ce zaka je NFT marketplace ka sayo. Wando da takalmar duka NFT ne, zaka je ka biya a baka, sai ka sakawa Ronaldo din, wani zai je ya sayo kayan Okocha ko Ahmad Musa, daga yadda ake zuwa sayan kayan daga nan darajar su ke karuwa. Ina fatan mun gane, idan ka sayi Rigar Ronaldo to ta kare kenan sai dai in an sake yin wata Rigar. So, masu siyar da NFT suna siyarwa masu buga game suna saya. Haka abun yake a bangaren littattafai da sauran su. Haka idan Game din yaki (War) ko fada (Battle) kake bugawa za'a ce ka sayo Bindiga, ko Bullet ko Bullet prove shirt ๐Ÿ‘•. Zaka same su ne a kasuwar NFT idan ka sayo sai ka saka kaje kayi yakin. Kada rubutun yayi yawa bari mu tsaya a nan, nan gaba zamu duba yadda ake yin NFT din, da kuma digital identity da verification da suke dauke dashi akan Blockchain, sai rabe raben NFT da kuma yadda zamu amfana da NFT fiye da yadda ada mutane suke kallon NFT a matsayin wani bakon abu ko abin Gwaigwai ๐Ÿฅณ da sauran su. Harka ce mai fadi mai girman gaske, a yanzu a duniyar blockchain babu inda NFT yake yin daraja kamar kan TON blockchain a 'yan watannin nan, saboda me? zamu bayyana haka nan gaba, in sha Allah.

โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
5/25/2025, 9:25:32 AM
Post image
Image
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/13/2025, 1:18:01 AM
Post image
Image
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/13/2025, 1:18:58 AM

Menene NFT (Non Fungible Token)... Yau dai bari mu leka cikin NFT wato "Non Fungible Token". A cikin Crypto da Blockchain industry idan aka ce NFT ana nufin token din da baya rabuwa, token din da ba'a iya fasa shi, ko a iya raba shi gida biyu, a faskara shi ko a 'bangara shi. Yadda yake guda daya to haka zai cigaba da zama a matsayin abu daya babu wani irin sa. NFTs crypto tokens ne da ake iya ajiye video clip a cikin su, ko hoto, ko zane ko wata murya ko kuma wani Art work, kuma a dora shi akan blockchain domin a adana shi. NFTs ba'a iya exchanging dinsu da wani Crypto ya zama madadin su kai tsaye, sai dai ana iya biyan kudi a bayar dasu, kamar ka bayar da TON a baka NFT. Domin mu fahimci NFT sosai, zan bayar da misali da Fungible Tokens, idan aka ce Fungible Tokens sune irin su Bitcoin, Ethereum, BNB, CORE, Solana da sauran su, misali: ~ A yanzu Solana kwaya daya (full unit) yana kan farashin Dala 157, idan bani da kudin da zan sayi SOL guda daya zan iya sayan wani bangare nasa kamar 0.5 SOL, 0.02 S

Post image
Image
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/14/2025, 11:20:46 PM

Some Important Facts Nigerians Should Understand About: Iran ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ท and Israel ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ฑ - Iran ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ท is not an Arab country; it is predominantly Persian. - Israel ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ฑ is not a Christian nation; it is predominantly Jewish. - The Jewish people practice Judaism, not Christianity โœ. - In Israel ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ฑ, both Christianity and Islam are minority religions, but there are far more Muslims than Christians. More than 23% of Israel are Muslims but only 1.2% are Christians. - Iran ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ท actually has a larger Christian population than entire population of Israel. - There are more Arabs in Israel ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ฑ than there are Christians โœ. - Preaching Christianity is easier in Iran than it is in Israel. - Iranians ๐Ÿ‡ฎ๐Ÿ‡ท speak Persian (Farsi), and only a small minority speak Arabic. - Iran is the leading Shia Muslim nation and often at odds with Sunni Islamic doctrine, which is led by Saudi Arabia. If the only reason you support Israel is because it is mentioned in the Bible or you believe it is a Christian country... If the only reason you support Iran is because you think it is an Arab nation or simply because it is predominantly Muslim. If your support is not based on who is right or wrong, who breaks international laws, or who upholds justice and fairness; but is instead based solely on religious sentiment... Then you are not standing for truth, fairness, or humanity. You are simply acting out of religious bias. Let us stand for truth, justice, and human dignity; no matter who is involved.

โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/14/2025, 11:20:45 PM
Post image
Image
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/13/2025, 1:18:05 AM

Notcoin, Not Pixel, da Waษ—anda sukayi Void an raba musu stickers daga team ษ—in Notcoin, wanda ana shirin fara pre-market ษ—in su kamar yadda aka fara pre-market ษ—in Notcoin voucher. Sai dai ba random suka raba ba. Akwai matakai da dole ne ka cimma kafin a baka sticker na wannan matakin. Zaka iya samun fiye da ษ—aya, gwargwadon matakin da ka kai. Waษ—anda sukayi Notcoin an basu sticker da ke daidai da level ษ—inka: diamond league, bronze, da makamantansu. Ku duba wajen inventory. Waษ—anda sukayi Notpixel an raba musu pixel dudes da leader. Su ma duba wajen inventory. Waษ—anda suke Void, suma an basu stickers guda 7 โ€” ko kuma ya danganta da yadda aka raba lokacin da muka gama Season 0. Duba inventory. Wajen achievement kuma, an bada stickers 2: Test Pilot: An baiwa waษ—anda sukayi aiki tukuru tun daga lokacin testnet na Notcoin. Alpha: An baiwa waษ—anda suka kawo community lokacin Notcoin. Notpixel: Alliance: Idan ka gayyato mutane 128. King: Idan ka gayyato sama da mutane 1000. Void: Idan ka kasance cikin waษ—anda suka samu sticker lokacin da aka gama Season 0, sai aka baka Zero Champion. Iya mutum 2500 suka samu wannan sticker Wannan shine airdrop na farko da TON Blockchain ta bayar ta hanyar stickers, a kokarinsu na farfaษ—o da kasuwar NFT da akeyi a Blockchain ษ—insu. Duk da haka, yanzu haka su ne Blockchain da yafi samun karbuwa da kuma bada riba a kasuwancin NFT. Zaku iya duba sticker nawa suka ba ku a nan: ๐Ÿ”— https://t.me/notgames_bot/profile (ba referral link bane) An kusa buษ—e pre-market domin fara cin kasuwa. Ubangiji Allah ya bamu sa'a, yasa suyi daraja.

โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
โœฆโœง ๐€๐ƒ ๐—ช๐—˜๐—•๐Ÿฏ ๐€๐‚๐€๐ƒ๐„๐Œ๐˜ โœงโœฆ
6/6/2025, 5:32:24 AM
Post image
Image
Link copied to clipboard!