HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
January 31, 2025 at 07:31 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 01/08/1446. Juma'a. 31/01/2025. Juma'a. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {160} _______________ - 878. An karɓo daga ɗan Abbas Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Wani mutum yayi wa Manzon Allah ﷺ kyautar raƙumi, sa’an nan sai (Manzon Allah ﷺ ya yi masa sakayya akanta. Sai ya ce: ‚Ka yarda? Sai ya ce: ‚A’a, sai ya ƙara masa, sai ya ce: ‚Ka yarda? Sai ya ce: ‚A’a, sa’an nan ya ƙara masa, sai ya ce: ‚Ka karda? Sai ya ce ‚Na’am‛. Ahmad ne ya ruwaito shi. Kuma dan Hibban ya inganta shi‛. - 879. An karɓo daga Jabir Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Umura (wato zama na kyauta) yana ga wanda aka bada.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. Daga Muslim kuma ya ce: ‚Ku kame daga dukiyarku, kada ku yi ɓarna, to, wanda aka yi masa kyautan zama zuwa rayuwa, to, kyautar tana ga wanda aka yi masa Umara da rayuwa, ko da mutunwa, da aƙibarsa.‛ - A cikin wani lafazi: ‚Umaran da aka sani shine wanda Manzon Allah ﷺ ya halatta kuma shine mai badawa ya ce: ‘Ta kasance da Aƙibarka, amma idan ya ce: ‚Na kane zuwa abinda ka rayu, to, tana koma ga mai ita.‛ (bayan mutum wanda aka ba).‛ Daga Abi Dawuda da Nisa’i cewa: ‚Kada kuyi rububa (wato shine mutum ya ce wa wani mutum ga gidana mu zauna idan na rigaka mutuwa ya kasance naka, amma idan ka rigani, to, ya zama nawa, kada kuyi Umara (wato shine kace wa wani kazo mu zauna tare zuwa mutuwata da kai da iyalan ka) wanda yayi ruƙuba, da wani Abu, ko yayi Umara da wani abu, to, yana ga maga ɗansa.‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments