
HASKEN MUSULUNCI
255 subscribers
About HASKEN MUSULUNCI
Domin yaɗa nasihun musulunci cikin hotuna masu ƙayatarwa FISABILILLAHI.
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 08/08/1446. Juma'a. 07/02/2025. Juma'a. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {167} _______________ - 907. An karɓo daga Amamatal Bahili Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa: haƙiƙa Allah ya bada dukkan ma’abucin haƙƙi haƙƙinsa, to, babu wasiyya ga mai gado.‛ Ahmad da mutane huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Nisa’i. Ahmad da Tirmizi sun kyautata shi, ɗan Khuzaima da ɗan Jarud suka ƙarfafa shi.‛ (Hadisin ingantacce ne).‛ - Daga Darul ƙuɗini daga Hadisin ɗan Abbas Allah Ya yarda da su, ya ƙara a cikin karshen sa: ‚Sai dai masu gado, idan sun so.‛ isnadinsa mai kyaune.‛ - 908. An karɓo daga Mu’azu ɗan Jabal Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Annabi ﷺ ya ce: Haƙiƙa Allah yana yin sadaka da sulusin dukiyar ku, a lokacin mutuwar ku, ƙari a cikin kyawawan ayyukanku.‛ Darul ƙuɗini ya ruwaito shi.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne). Ahmad da Bazzari sun ruwaito daga Hadisin Abi Darda’i.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ - Kuma ɗan Majah ya ruwaito shi, daga Hadisin Abi Huraira Allah Ya yarda da shi, dukkan ta mai rauni ce, Amma sashe yana ƙarfafa sashe, Allah shine Mafi sani.‛ (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ - *BABIN BAYANIN HUKUNCIN AJIYA DA YANDA AKE KARƁA.* - 909. An karɓo daga Amru ɗan Shu’aibu daga babansa daga kakansa Allah Ya yarda da su, daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Wanda aka ba shi wani ajiya, to, (idan ta halaka) babu biya kansa.‛ ɗan Majah ya ruwaito shi, a cikin isnadinsa akwai rauni.‛ (Hadisin Hasanun ne). - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 09/08/1446. Asabar. 08/02/2025. Asabar. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {168} _______________ - *LITTAFIN AURE BABIN BAYANIN HUKUNCIN AURE DA YANDA AKE NEMAN AURE DA KUMA WASU ABUBUWA DA SUKA SHAFI AURE.* - 910. An karɓo Abdullahi ɗan Mas’ud Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Yaku taro samaruka, wanda ya mallaki wurin zama daga cikinku, yayi aure, shine yafi daga rintsewan ido, yafi daga kiyaye wan farji, amma wanda ba shi da ikon, to, yayi azumi, domin shine daab-kansa, daga sha’awa.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 911. An karɓo daga Anas ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ yayi godiya yayi yabo ya ce: ‚Amma ni ina yin sallah, ina yin aure in mace, ina yin azumi ina kuma cin abinci, ina yin auren maccen wanda yayi kyamar, sunna ta baya tare dani.‛ Bukhari da Musulmi suka ruwaito shi.‛ - 912. An karɓo daga gareshi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya kasance yana umurtarmu da wurin zama, yana hanamu kada ita, hani mai tsanani yana cewa: ‚Kuyi auren mai haifan ‘ya’ya masu sayayya domin nayi fariya da yawanku wa Annabawa ranan ƙiyama.‛ Ahmad ya ruwaito ɗan Hibban ya ingantashi.‛ Yana da shaida daga Abin Dawuda da Nisa’i da ɗan Hibban daga Hadisin Ma’aƙil ɗan Yassar.‛ - 913. An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Ana auren mace don abubuwa huɗu sune: ‚Domin dukiyar ta, da kuma domin kyawunta, da domin addininta, sai ya rinjaryar da ma’abuciyar addini, ko da hannun ka zai ja ƙasa domin talauci.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, tare masu ruwaya nan bakwai.‛ + 914. An karɓo daga gareshi kuma ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya kasance idan mutum yayi nufin yin aure, sai ya ce: ‚Allah yayi maka Albkarka, Allah ya yi Albarka ya haɗa tsakaninku da Alheri.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi.‛ Tirmizi da ɗan Khuzaima da ɗan Hibban suka inganta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 05/08/1446. Talata. 04/02/2025. Talata. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {164} _______________ - 896. An karɓo daga ɗan Buraida daga babansa Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Lallai Annabi ﷺ ya sanya wa kaka ta mace sudusi, amma idan babu uwa‛. Abu Dawud da Nisa’I ne suka ruwaito shi‛ (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 897. An karɓo daga Miƙidar ɗan Ma’adi Karb, ya ce: ‘Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Kawu yana gadon abinda babu mai gadonsa‛. Ahmad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi. Sai dai banda Tirmizi. Kuma Abu Zur’a Al-rrazi ya kyautata shi, Kuma Hakim da ɗan Hibban ne suka inganta shi‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 898. An karɓo daga Abi Umama ɗan Sahal Allah Ya yarda da shi ya ce, ‚Umar ya rubuta zuwa ga Abi Ubaidah Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Lallai Manzon Allah ﷺ ya ce; ‚Allah da ManzonSa sune majiɓantar wanda baya da majiɓinci, kuma kawu yana gadon wanda baya da mai gadon‛. Ahmad da mutane huɗu ne suka ruwaito shi, sai dai banda Abi Dawud, Tirmizi ya kyauta shi. Amma kuma ɗan Hibban ya inganta shi‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 899. An karɓo daga Jabir Allah Ya yarda da shi daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Idan abin haihuwa yayi kuka yana gado, (wato idan aka haifi yaro yana darai, to, shima yana gado).‛ Abu Dawuda ya ruwaito shi, ɗan Hibban ya inganta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

*Assalamu Alaikum* - *_29/04/1440,_* _Lahadi._ *_06/01/2019,_* _Lahadi._ - *<KITABUT-TAUHID>* - *Wallafar:* Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan. *Fassarar:* Aliyu Muhammad Sadisu *Wanda ya duba:* Attahiru Bala Dukku - *DARASI NA (055)* *__________________* - *_•┈┈┈┈•﷽•┈┈┈┈•_* - _Kore imani dangane da wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukarba._ - _Yana nuna cewa ashe hukunci da shari’ar Allah imanine kuma aƙidace kuma bautawa Allah ne, wannan ya zama kowanne musulmi ya bautawa Allah dashi, ba wai za’a yi hukunci da shari’ar Allah bane don cewa hukunci da ita shi ya fi yi wa mutane kyau kuma shi ya fi tabbatar da tsaro ba._ - _Domin wasu sun fi maida hankali akan wannan ɓangaren, sai su bar ɓangaren farko._ - _Kuma Allah maɗaukakin sarki haƙiƙa ya aibanta waɗanda suke hukunci da shari’ar Allah domin fa’idar kansa ba wai domin bauta ga Allah maɗaukakin sarki ba._ - ```Allah mai girma da ɗaukaka yana cewa:``` - _*(“Kuma idan aka kirayesu izuwa ga Allah da Manzonsa domin ya yi hukunci a tsakaninsu kawai sai wasu tawaga daga cikinsu su juya baya, idan kuwa ya kasance su suke da gaskiya sai su zo wurinsa a guje”)*_. Suratun Nur, aya ta: 48-49. - _Su basa himmatuwa sai akan abinda suke so, abin kuwa da ya saɓawa son zuciyarsu sai su kawar da kawunansu daga gareshi, domin su basa bautawa Allah da kai ƙararrakinsu wurin Manzon Allah (ﷺ)._ - *Allah ka datar damu.* *__________________* _Muhammad bn Umar_ " DAGA Zauren *HASKEN MUSULINCI* " Ga masu buƙatar shiga zauren sai su aiko da cikakkiyar sallama tareda cikakken suna ta wannan number ɗin ta whatsApp sai su faɗi buƙatar su +2348133045868 " Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb " سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 06/08/1446. Laraba. 05/02/2025. Laraba. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {165} _______________ - 900. An karɓo daga Amru ɗan Sha’aibu daga babansa daga kakansa ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu gadon komai ga mai kisan kai, (wato wanda ya kashe ɗan’uwansa, to, baya gadonsa).‛ Nisa’i da Darul ƙuɗini suka ruwaitoshi, ɗan Abdul Bari ya ƙarfafa shi, kuma Nisa’I ya ce hadisi ne Ma’alulli, kuma sawaba shine dakatar da hadisin akan Amru.‛ (Hadisin dwa’ifi ne).‛ - 901. An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗabi Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa: ‚Wanda ya tsare uba, ko ɗa, ko da toshi yana da abinda ya kasance akansa tare asibai.‛ Abu Dawuda da Nisa’i da ɗan Maja suka ruwaito shi, ɗan Madina da ɗan Barri suka inganta shi.‛ (Hadisin Hasanun ne). - 902. An karɓo daga Abdullah ɗan Umar Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Walicci na mace kamar nanar nasaba ba’a sayarwa, ba’a kyauta.‛ Hakim ya ruwaito shi, daga hanya Shafi’i, daga Muhamadu ɗan Hassan, daga Abi Yusuf ɗan Hibban ya inganta shi.‛ Baihaƙi yayi masa illah.‛ - 903. An karɓo daga Abi ƙilabata daga Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Wanda yafiku sanin hukuncin gado, shi ne Zaidu ɗan Sabitu.‛ Ahmad da Mutum Huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Abi Dawuda.‛ (Hadisin Ingantacce ne)‛. - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 04/08/1446. Litinin. 03/02/2025. Litinin. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {163} _______________ - *BABIN BAYANIN HUKUNCIN WAƊANDA SUKE GADO DA WAƊANDA BASA GADO DA YANDA AKE RABAWA.* - 891. An karɓo daga ɗan Abbas ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku bada gado ga mazowanta, abinda ya saura, to, ya kasance ga wanda ya zan ya cancanta ga mutum na miji.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. - 892. An karɓo daga Usama ɗan Zaidu Allah Ya yarda da shi ya ce, ‚Lallai Annabi ﷺ yace: ‚Musulmi baya gadon kafiri, haka kuma kafiri baya gadon Musulmi‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛. - 893. An karɓo daga ɗan Masa’ud Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Cikin ɗiya mace da ɗiyar ɗa, da kuma ‘yar’uwa. Sai Annabi ﷺ yayi hukunci da cewa: ‚ɗiya mace tana da rabi, ga ɗiyar da da cewa: ‚Ita tana sudusi – wato kashi uku cikin huɗu, sa’an nann kuma abin da yai shaura, to, yana ga ‘yar’uwan‛. Bukhari ne ya ruwaito shi‛. - 894. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu gado ga masu addini biyu‛ (Muslmi da kafiri)‛. Ahmad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi da Tirmizi. Kuma Hakim ya ruwaito da lafazin Usama‛. Kuma Nisa’i ya ruwaito shi da hadisin Usmasa ta wan nan lafazin‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 895. An karɓo daga Imrana ɗan Husani Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Wani mutum ya zo ga Annabi ﷺ sai ya ce: haƙiƙa ɗana ya mutu, to, me ke gareni na gadonsa? Sai ya ce: ‚Kana da sudusi ɗiya cikin shida, lokacin da ya juya, sai ya kira shi, sai ya ce: ‚Masa kana da wani sudusin, kuma ya sake kiransa, ya ce: haƙiƙa sudusin nan na ƙarshe, to, shi na abinci ne‛. Ahamad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi‛. (Hadisin Dwa’ifi ne)‛. - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 02/08/1446. Asabar. 01/02/2025. Asabar. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {161} _______________ - 880. An karɓo daga Umar ya ce: ‚Na bada doki ga Hanyar Allah, sai yayi ƙunciwa Ma’bucinsa, sai na yi zaton shi zai sayarda shi, da sauki, sai na tambayi Manzon Allah ﷺ game da haka, sai ya ce: ‚Kada ka saye shi, ko za’a ba kashi da dirhami.‛ zuwa hadisin.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ . 881. An karɓo daga Abi Huraira daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Ku dawo ku tuba ku yi soyayya.‛ Bukhari ya ruwaito shi, A cikin Adabil Mufuradu da Abu Ya’ala, isnadi mai kyau.‛ - 882. An karɓo daga Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku yi kyauta domin kyauta tana saukakar da miyagun aiki.‛ Bazari ya ruwaito shi, da isnadi mai rauni.‛ (Hadisi dwa’ifi ne).‛ - 883. An karɓo daga Abi Huraira ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ya matan musulmai kada maƙwafciya ta wulaƙanta maƙwafciyanta, ko da taƙona akuya.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. - 884. An karɓo daga ɗan Umar Allah Ya yarda da su daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Wanda yayi kyauta da wani kyauta, to, shine yafi cancanta da ita, matuƙar ba’a samu gare taba.‛ Hakim ya ruwaito shi, ya inganta shi,kuma abin kiyayewa daga ruwayar ɗan Umar, daga Umar wannan faɗinsa ne.‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 01/08/1446. Juma'a. 31/01/2025. Juma'a. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {160} _______________ - 878. An karɓo daga ɗan Abbas Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Wani mutum yayi wa Manzon Allah ﷺ kyautar raƙumi, sa’an nan sai (Manzon Allah ﷺ ya yi masa sakayya akanta. Sai ya ce: ‚Ka yarda? Sai ya ce: ‚A’a, sai ya ƙara masa, sai ya ce: ‚Ka yarda? Sai ya ce: ‚A’a, sa’an nan ya ƙara masa, sai ya ce: ‚Ka karda? Sai ya ce ‚Na’am‛. Ahmad ne ya ruwaito shi. Kuma dan Hibban ya inganta shi‛. - 879. An karɓo daga Jabir Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Umura (wato zama na kyauta) yana ga wanda aka bada.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. Daga Muslim kuma ya ce: ‚Ku kame daga dukiyarku, kada ku yi ɓarna, to, wanda aka yi masa kyautan zama zuwa rayuwa, to, kyautar tana ga wanda aka yi masa Umara da rayuwa, ko da mutunwa, da aƙibarsa.‛ - A cikin wani lafazi: ‚Umaran da aka sani shine wanda Manzon Allah ﷺ ya halatta kuma shine mai badawa ya ce: ‘Ta kasance da Aƙibarka, amma idan ya ce: ‚Na kane zuwa abinda ka rayu, to, tana koma ga mai ita.‛ (bayan mutum wanda aka ba).‛ Daga Abi Dawuda da Nisa’i cewa: ‚Kada kuyi rububa (wato shine mutum ya ce wa wani mutum ga gidana mu zauna idan na rigaka mutuwa ya kasance naka, amma idan ka rigani, to, ya zama nawa, kada kuyi Umara (wato shine kace wa wani kazo mu zauna tare zuwa mutuwata da kai da iyalan ka) wanda yayi ruƙuba, da wani Abu, ko yayi Umara da wani abu, to, yana ga maga ɗansa.‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 03/08/1446. Lahadi. 02/01/2025. Lahadi. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {162} _______________ - *BABIN BAYANIN HUKUNCIN TSUNTUWA DA YANDA AKE AIKATAWA IDAN AKA SAME TA*. - 885. An karɓo daga Anas ya ce: ‘Manzon Allah ﷺ ya shige wani dabino, a kan hanya, sai ya ce: ‚Da ba domin ina tsoron kada ta kasance na sadaka ce ba, dana ɗauka naci.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 886. An karɓo daga Zaidu ɗan Khailidil Juhani ya ce: ‚Wani mutum ya zo ga Annabi ﷺ ya tambaye shi game da kayan tsuntuwa, sai ya ce, masa: ‚Ka sanar da haƙiƙa da a binda aka ɗaure da shi, sa’an nan ka sanar zuwa shekara, idan mai kaya ya zo, to, shikenan, idan kuwa bai zo ba kayi ɓataccen akuya, sai ya ce: ‚Ta kasance taka, ko ga ɗan uwanka, ko ta kasance karen dawa.‛ Ya ce: ‚To, mene ne hukuncin ɓataccen rakuma, sai ya ce: masa: ‚Me ya haɗa ka ita tana da ruwan shanta da takalma tana shan ruwa tana cin abinci, sai Ubangijinta ya haɗu da ita.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 887. An karɓo daga gareshi Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Wanda ya taro ɓataccen kaya, to, ya taro wa cikinsa bata matuƙar bai sanar da ita.‛ Muslim ya ruwaito shi.‛ - 888. An karɓo daga Iyad ɗan Himar Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: Wanda ya samu tsuntuwa, sai ya sanar da ita, ga masu Adalci ya kiyaye jakka, da madaurinta, sa’an nan kada ya ɓoyeta, idan shugabanta ya zo shine mafi cancanta da ita, idan ba haka dukiyar Allah ce yana bada wanda yaso.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Tirmizi. Ɗan Khuzaima da ɗan Jarud da ɗan Hibban suka inganta shi.‛ (Hadisin ingantacce ne).‛ - 889. An karɓo daga Abdurraham ɗan Usman Tamimi, Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya hana game da ɗaukar kayan tsuntuwar mai aikin Hajji.‛ Muslim ya ruwaito shi.‛ - 890. An karɓo daga Miƙidad ɗan Ma’adi Karib Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku saurarawa dabbobi, wa masu kunba safika basa halatta, da jakin gida, da tsuntuwa daga dukiya wanda akayi alƙawari, sai idan an wadata daga gareta.‛ Abu Dawuda ya ruwaito shi.‛ ( Albani ya Inganta shi).‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 07/08/1446. Alhamis. 06/02/2025. Alhamis. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {166} _______________ - *BABIN BAYANIN HUKUNCIN WASIYYA DA KUMA YANDA AKE YINTA DA YANDA AKE AIKI DA ITA*. - 904. An karɓo daga ɗan Umar Allah Ya yarda da su ya ce; haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu wani abu na haƙƙin Musulimi da yake son yin wasiyya cikinsa ya kwana dare biyu, face wasiyya ce wanda aka rubuta daga gare shi‛. Bukhari da Muslum ne suka ruwaito shi‛. - 905. An karɓo daga Sa’adu ɗan Abi Waƙƙas Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Na ce wa Manzon Allah ﷺ ya Manzon Allah ni mai dubiyane babu mai dagona, face ɗiyata guda data ke gareni, to, na yi sadaka da sulusi biyu na dukiya? Sai ya ce: ‚A’a, (wato biyu cikin uku na dukiya) sai na ce, ‚To, na yi sadaka da sulusinsa (wato ɗaya cikin uku na dukiyarsa), sai ya ce: ‚Sulusi da sulusi da yawa, haƙiƙa kai kabar wa mai gadonka da wadata shine, yafi maka alheri da kabarsu matalauta suna yawo ga mutane‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛. - 906. An karɓo daga Aishatu Allah Ya yarda da ita ta ce: haƙiƙa wani mutu ya zo ga Annabi ﷺ sai ya ce, ‚Ya Manzon Allah! Haƙiƙa mahaifi yata an karɓi ranta bata yi wasiyya ba, nayi zaton da tayi magana za ta yi wasiyya da sadaka, tana da lada, idan na yi mata sadaka? ‚Sai ya ce: ‚Na’am.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.