HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 1, 2025 at 05:32 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 02/08/1446. Asabar. 01/02/2025. Asabar. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {161} _______________ - 880. An karɓo daga Umar ya ce: ‚Na bada doki ga Hanyar Allah, sai yayi ƙunciwa Ma’bucinsa, sai na yi zaton shi zai sayarda shi, da sauki, sai na tambayi Manzon Allah ﷺ game da haka, sai ya ce: ‚Kada ka saye shi, ko za’a ba kashi da dirhami.‛ zuwa hadisin.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ . 881. An karɓo daga Abi Huraira daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Ku dawo ku tuba ku yi soyayya.‛ Bukhari ya ruwaito shi, A cikin Adabil Mufuradu da Abu Ya’ala, isnadi mai kyau.‛ - 882. An karɓo daga Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku yi kyauta domin kyauta tana saukakar da miyagun aiki.‛ Bazari ya ruwaito shi, da isnadi mai rauni.‛ (Hadisi dwa’ifi ne).‛ - 883. An karɓo daga Abi Huraira ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ya matan musulmai kada maƙwafciya ta wulaƙanta maƙwafciyanta, ko da taƙona akuya.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. - 884. An karɓo daga ɗan Umar Allah Ya yarda da su daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Wanda yayi kyauta da wani kyauta, to, shine yafi cancanta da ita, matuƙar ba’a samu gare taba.‛ Hakim ya ruwaito shi, ya inganta shi,kuma abin kiyayewa daga ruwayar ɗan Umar, daga Umar wannan faɗinsa ne.‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments