HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 2, 2025 at 07:46 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 03/08/1446. Lahadi. 02/01/2025. Lahadi. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {162} _______________ - *BABIN BAYANIN HUKUNCIN TSUNTUWA DA YANDA AKE AIKATAWA IDAN AKA SAME TA*. - 885. An karɓo daga Anas ya ce: ‘Manzon Allah ﷺ ya shige wani dabino, a kan hanya, sai ya ce: ‚Da ba domin ina tsoron kada ta kasance na sadaka ce ba, dana ɗauka naci.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 886. An karɓo daga Zaidu ɗan Khailidil Juhani ya ce: ‚Wani mutum ya zo ga Annabi ﷺ ya tambaye shi game da kayan tsuntuwa, sai ya ce, masa: ‚Ka sanar da haƙiƙa da a binda aka ɗaure da shi, sa’an nan ka sanar zuwa shekara, idan mai kaya ya zo, to, shikenan, idan kuwa bai zo ba kayi ɓataccen akuya, sai ya ce: ‚Ta kasance taka, ko ga ɗan uwanka, ko ta kasance karen dawa.‛ Ya ce: ‚To, mene ne hukuncin ɓataccen rakuma, sai ya ce: masa: ‚Me ya haɗa ka ita tana da ruwan shanta da takalma tana shan ruwa tana cin abinci, sai Ubangijinta ya haɗu da ita.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛ - 887. An karɓo daga gareshi Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Wanda ya taro ɓataccen kaya, to, ya taro wa cikinsa bata matuƙar bai sanar da ita.‛ Muslim ya ruwaito shi.‛ - 888. An karɓo daga Iyad ɗan Himar Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: Wanda ya samu tsuntuwa, sai ya sanar da ita, ga masu Adalci ya kiyaye jakka, da madaurinta, sa’an nan kada ya ɓoyeta, idan shugabanta ya zo shine mafi cancanta da ita, idan ba haka dukiyar Allah ce yana bada wanda yaso.‛ Ahmad da mutum huɗu suka ruwaito shi, sai dai banda Tirmizi. Ɗan Khuzaima da ɗan Jarud da ɗan Hibban suka inganta shi.‛ (Hadisin ingantacce ne).‛ - 889. An karɓo daga Abdurraham ɗan Usman Tamimi, Allah Ya yarda da shi ya ce: haƙiƙa Annabi ﷺ ya hana game da ɗaukar kayan tsuntuwar mai aikin Hajji.‛ Muslim ya ruwaito shi.‛ - 890. An karɓo daga Miƙidad ɗan Ma’adi Karib Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku saurarawa dabbobi, wa masu kunba safika basa halatta, da jakin gida, da tsuntuwa daga dukiya wanda akayi alƙawari, sai idan an wadata daga gareta.‛ Abu Dawuda ya ruwaito shi.‛ ( Albani ya Inganta shi).‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments