
HASKEN MUSULUNCI
February 3, 2025 at 05:30 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓
-
04/08/1446. Litinin.
03/02/2025. Litinin.
-
Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy.
-
DARASI NA {163}
_______________
-
*BABIN BAYANIN HUKUNCIN WAƊANDA SUKE GADO DA WAƊANDA BASA GADO DA YANDA AKE RABAWA.*
-
891. An karɓo daga ɗan Abbas ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Ku bada gado ga mazowanta, abinda ya saura, to, ya kasance ga wanda ya zan ya cancanta ga mutum na miji.‛ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.
-
892. An karɓo daga Usama ɗan Zaidu Allah Ya yarda da shi ya ce, ‚Lallai Annabi ﷺ yace: ‚Musulmi baya gadon kafiri, haka kuma kafiri baya gadon Musulmi‛. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi‛.
-
893. An karɓo daga ɗan Masa’ud Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Cikin ɗiya mace da ɗiyar ɗa, da kuma ‘yar’uwa. Sai Annabi ﷺ yayi hukunci da cewa: ‚ɗiya mace tana da rabi, ga ɗiyar da da cewa: ‚Ita tana sudusi – wato kashi uku cikin huɗu, sa’an nann kuma abin da yai shaura, to, yana ga ‘yar’uwan‛. Bukhari ne ya ruwaito shi‛.
-
894. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Babu gado ga masu addini biyu‛ (Muslmi da kafiri)‛. Ahmad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi da Tirmizi. Kuma Hakim ya ruwaito da lafazin Usama‛. Kuma Nisa’i ya ruwaito shi da hadisin Usmasa ta wan nan lafazin‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛.
-
895. An karɓo daga Imrana ɗan Husani Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Wani mutum ya zo ga Annabi ﷺ sai ya ce: haƙiƙa ɗana ya mutu, to, me ke gareni na gadonsa? Sai ya ce: ‚Kana da sudusi ɗiya cikin shida, lokacin da ya juya, sai ya kira shi, sai ya ce: ‚Masa kana da wani sudusin, kuma ya sake kiransa, ya ce: haƙiƙa sudusin nan na ƙarshe, to, shi na abinci ne‛. Ahamad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi‛. (Hadisin Dwa’ifi ne)‛.
-
Allah kasa mudace
__________________
Muhammad Umar Baballe
Aßu Amatillah
-
DAGA
Zauren HASKEN MUSULINCI
-
Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp.
https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K
-
Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan
https://t.me/haskenmusulinci
-
Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb
-
ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.