HASKEN MUSULUNCI
HASKEN MUSULUNCI
February 4, 2025 at 05:50 AM
📘 BULUGUL-MARAM 📓 - 05/08/1446. Talata. 04/02/2025. Talata. - Bulugul-maram min adillatil ahkam, na babban malami imamul-hafiz ibn hajar al'asƙalaniy. - DARASI NA {164} _______________ - 896. An karɓo daga ɗan Buraida daga babansa Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Lallai Annabi ﷺ ya sanya wa kaka ta mace sudusi, amma idan babu uwa‛. Abu Dawud da Nisa’I ne suka ruwaito shi‛ (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 897. An karɓo daga Miƙidar ɗan Ma’adi Karb, ya ce: ‘Manzon Allah ﷺ ya ce: ‚Kawu yana gadon abinda babu mai gadonsa‛. Ahmad da mutune huɗu ne suka ruwaito shi. Sai dai banda Tirmizi. Kuma Abu Zur’a Al-rrazi ya kyautata shi, Kuma Hakim da ɗan Hibban ne suka inganta shi‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 898. An karɓo daga Abi Umama ɗan Sahal Allah Ya yarda da shi ya ce, ‚Umar ya rubuta zuwa ga Abi Ubaidah Allah Ya yarda da su ya ce: ‚Lallai Manzon Allah ﷺ ya ce; ‚Allah da ManzonSa sune majiɓantar wanda baya da majiɓinci, kuma kawu yana gadon wanda baya da mai gadon‛. Ahmad da mutane huɗu ne suka ruwaito shi, sai dai banda Abi Dawud, Tirmizi ya kyauta shi. Amma kuma ɗan Hibban ya inganta shi‛. (Hadisin Ingantacce ne)‛. - 899. An karɓo daga Jabir Allah Ya yarda da shi daga Annabi ﷺ ya ce: ‚Idan abin haihuwa yayi kuka yana gado, (wato idan aka haifi yaro yana darai, to, shima yana gado).‛ Abu Dawuda ya ruwaito shi, ɗan Hibban ya inganta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛ - Allah kasa mudace __________________ Muhammad Umar Baballe Aßu Amatillah - DAGA Zauren HASKEN MUSULINCI - Ku kasance damu a channel ɗinmu na WhatsApp. https://whatsapp.com/channel/0029VaB2uck0bIdoYXUH752K - Kuna iya samun mu a shafin mu na telegram ta nan https://t.me/haskenmusulinci - Domin samun mu a facebook ɗin mu kuma sai a biyo mu ta wannan koren link ɗin, ta hanyar danna shi. https://mobile.facebook.com/groups/151610345250905?refid=27&ref=opera_speed_dial_freefb - ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ.

Comments